💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙24
Suna zuwa gida khalifa yadauki motan shi yakama hanyan damaturu ana kiran magrib ya isa,da zumudi yawuce gidansu Nihal saidai yana isa ya tarad da mutane sosai a kofan gidan kuma yawanci su en jajere ne don haka baisamu daman zuwa kofan gidan ba….duk yadda yaso abun ya faskara haka yakai har karfe shadaya a wajen amma baisamu ganin Ammie ba karshe yaje ya nemi wajen kwana.
da sassafe yazo don ko baccin kirki bai samu yayi ba saidai yana zuwa motan su Ammie natashi, shine yagansu itakam bata ganshi ba..tayan motan shi ya buga da kafa yace what a fuck, gashi wajen bakowa balle wani ya mishi bayani,take yakama hanyan jajere don yasan acan ne zaiji meyake faruwa.
Haka ranan Nihal ta kwana batare da ta rintsa ba,washegari sosai fuskan ta ya kumbura saboda rashin bacci da kuma kukan datayi,ya yasir ne yazo dubata da safe ganin yadda fuskanta ya kumbura bakaramin tayar masa da hankali yayi ba haka yazauna yanata rarrashin ta sai da yaga tadan sake kafun yace mata zaije aiki don yau za'afara shiga kotu akan wancan case din daya bata labari,zai kira nasir yazo ya dubata kuma ya jadadda mata data kula da kanta,da ya fita dakin Ahmad yaje yace mishi Dan Allah ya kula da nihal sosai shi zai fita,a fili yace adawo lafiya a zuciyan shi kuma yace ai ko ba agayamin ba kula da nihal duty nane bazan taba bari ko kuda yatabata ba.
Tunda sukaga har kwana biyu khalifa baidawo ba suka fara tunanin ko rashin gsky ne ya hanashi dawowa.
Ammie sosai ta dage da addu’a harta samu nutsuwa acikin zuciyar ta,sannan tasamu tasake ranta akayi hidiman biki da ita ba yabo ba falasa,ranar da aka kai amarya shine ranar da khalifa yazo washegari kuma abuja suka wuce shine sabani da yayi dasu,saboda a satin Abba yasamu promotion tare da transfer zuwa abuja.a bikin dagin shi suka dinga guda da shwa wai khairat ta taho da alkhairinta saura wani shekara suzo suna,haka sukayita habaice habaice dakyar Ammie ta iya danne su umma Amina akan karsu tanka musu.
Abba yace dukansu zasu koma abuja amma Ammie tace ita babu inda zata harsai Nihal dinta tafito don haka yayi tafiyan shi da matan shi, shiko yace indai bazata ba saidai itama khairat din tazauna tare da ita shikadai yayi tafiyan shi,dakyar Ammie ta lallaba shi akan yatafi da khairat karya jawo mata magana agun dangin shi.
Ya yadda zasuje honeymoon amma harda ita badon taso ba saidon sanin kafiyan shi yasata ta amince.
Daya gayawa khairat dinma ta shirya zasu tafi abuja, take tace ita idan ba da Ammie ba bazata ba,ba kadan ba yaji dadin yadda ta nuna mishi son Ammie murmushi kawai yayi yajuya.
Khalifa yaje jajere yarasa wazai tambaya number Ammie, yasan kaf zuri'an su haushin shi sukeji bazasu saurare shi ba balle subashi number ta…daga karshe dai gidan su yawuce dakyar yasamu karfi gwiwa yayiwa antyn shi bayani,itama saida yayita mishi fada kafun nan tace zata tura akarbo mata number Ammie,bakaramin dadi yaji ba,a take ta tura aka karbo mata saidai basu dace ba don number da aka karbo din tadaina amfani dashi…khalifa duk ya rasa yadda zaiyi,kara rokon Antynshi yayi akan taje ta nemo mishi labarin abunda yake faruwa dasu Ammie,daga farko kin Amincewa tayi don tace ita bazai sata a shiriritan shi ba don tasan ko za'ayi yaya bazasu bashi ba Nihal ba,dakyar ta yadda don taanason khalifa sosai bakaman sauran matan baban shi ba,tace zataje amma saida yamma badon yaso ba saidon karya takura mata ya hakura,amma Sam yakasa samun sukuni ko abinci yakasaci.
Da yamma yayi taje yasamo mishi labari akan ai satin nan aka mata kishiya kuma sun wuce abuja tare da mijin su…. Kan khalifa ne yasake daurewa haka yakwana da tunanin ta ina zai fara Neman Ammie.
Ahmad ne ya bude kofan dakinta tare da sallama,ansawa tayi ciki ciki tana zaune akan sallaya ta hada kai da gwiwa,dama yasan haka zai sameta don kwana ki biyun nan haka takeyi,duk tasama ranta damuwa sosai kuma taki sakewa dasu kamar da.
Takowa yayi a hankali yazo gefenta ya zauna, irin zaman datayi yayi,a hankali yace Nihal kingaji damu kinason ki tafi gida ko? Hawaye ne ya gangaro mata ,yaci gaba gashi mukuma bamason rabuwa dake,inkika tafi zamu shiga kunci gidan zaima ba dadi,shima maganan yakeyi kamar zaiyi kuka dagowa tayi tana girgiza mishi kai,tace nima bazan iya Barin ku ba, kun zamo wani bangare na jiki na bazan iya rayuwa babu ku ba hawayen ta ne ya tsananta …
To meyasa kika sawa kanki damuwa idan har kina son mu,Ammie! Ammie na nakeson gani ya Ahmad nasan tana cikin damuwa... Ajiyan zuciya yayi yace indai wannan ki kwantar da hankalinki bazamujira mutumin nan ba(khalifa) in yaya yadawo zangaya mishi muje tare nemo miki Ammie ki,take tafara share hawayen ta tana murmushi,shima dadi yaji har ranshi yace to yanzu ki tashi muje muci abinci ko tace toh.
Yau shi yayi serving musu abinci,maa ne tafito tasa mesu,itama ganin Nihal acikin damuawa duk yasa taji ba dadi gashi tanaji tanagani lokacin tafiyan Nihal tabarsu yazo.
Kwanan khalifa uku a jajere ya koma borno,ya shaidawa Yusuf halin ake ciki,ajiyan zuciya yai yace wannan shine ga samu ga rashi,yanzu abunda za'ai ka huta sai muje mugaya musu halin da ake ciki, a ah aiba saina huta ba muje kawai, kuma gaskiya yau kam sai naga Nihal don inada kishin ruwan ganinta sosai…shuru Yusuf yayi sannan yace kaidai banason katada hankalinka insuka hanamu ganinta karka takura plss, kai kawai ya girgiza amma har cikin zuciyan shi ji yake hakurin shi yakare.
Sunje gidan me gadi yace bari yagayawa mutanen gidan,yaje yasamu Nihal da Ahmad a falo yace agayawa hajiya waisu Yusuf sunzo,take fara'an da dake fuskan Ahmad yadauke bata rai yayi sosai yace toh,jin abunda megadi yace yasa yasir fitowa da sauri yayi waje,shi kuma Ahmad hannu Nihal kawai ya rike ido tabishi dashi baiko kalleta ba yajata dakinta,idon shi dasukayi jajir ya sauke mata, ki zauna a daki karki fito yanzu zan dawo…kasa ansa mishi tai yaja kofan dakin ya rufe bakin gado taje tazauna zuciyan ta na mummunan bugawa.*Abdlzty💞*