12

42 5 0
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ





📙12



Ahmad ne yafito yanasa agogon shi yace mata muje ko? tashi tayi tabi bayanshi, mota ya bude musu suka shiga,hanyan uni-maid yakama, babu me magana acikin su saidai jifa jifa Ahmad yana juyowa ya kalleta, ita kuma hanya kawai take kallo,sun shiga yayi hanyan department dinsu a parking space yayi parking Shiya fara fita sannan itama ta fito,tun daga nesa en department din suka fara zuba musu ido kowa mamaki yake yau Ahmad ne da beb...wasu en mata ne sukaje suka samu wata budurwa a class tana karatu ita kadai,kyakkyawa ce ta ajin farko saidai ba fara Sol bace dukda baza asa ta a sahun bakake ba,desk din da hannun ta yake kai suka buga,ke Benazir tashi kizo kiga ikon Allah,hararan su tayi,tayi tsaki tajuya kanta tace kunsan fa banason shiririta kuma yanzu ba lokacin wasa bane,dayar ce tace dalla Aesh zo mu tafi har zamu kawo mata labari tana gwale mu,muna nan zatazo tana kuka da idonta mtsww,taja kawar ta har sun fara tafiya taji gwara fa taje tagani kar wani abun ne bata sani ba,da sauri tabi bayansu tana cewa Dan Allah ku tsaya mana,Aesh ce ta fara tsayawa,suna zuwa kofan class din,sai hango Ahmad da Nihal tayi suna tahowa tare bakaramin daukan ido sukeyi ba don kaf hankalin en makarantan yakoma Kansu…wani irin hajijiya taji,dakyar kawayenta suka riketa,innalillahy wa'inna ilayhir raji’un kawai take fada,zulaifa ce tace shine dama abunda muke kiran ki kike yanga,wasu hawayene masu zafi suka zubo a idonta, Aesh tayi saurin cemata shshshh haba kawata kuka kuma?ai tsayawa zakiyi ki nuna mishi kema mace ce me class,dago idanun ta tayi masu rauni tace Aesh kema kinsan banida sauran jarumta akan Ahmad sonda nake mishi bazai barni in iya mishi komai ba,da sauri zulaifa tace gasunan zuwa mu koma mu zauna ,wajen zama suka samu da hanzari sai ganinshi sukai yawuce dayan class din, Aesh ne ta sauke numfashi tace huh! Tare da juya idonta tace better, da sauri ta mike tace kinsan meye bena?kai kawai ta girgiza mata,tace may b mafa sister shine muketa tada hankalin mu ,maza ki tashi kije  kice mishi kinzo kuyi karatun tare anan ne zakisan meye halaqan shi da ita,gyara mata fuska tayi tace abeg kawata kidaina yin wani irin da fuskan ki, ki sake ranki, rakata sukai har kofan class din,tana shiga ta daga ido, suna hada ido ta sakar mishi murmushi shima ya maida mata,tana isowa takalli Nihal tana murmushi ta mika mata hannu,itama da fara'a a fuskan ta ta mika mata suka gaisa,juyawa yayi ya kalli Nihal yace mata this is Benazir my course mate(wannan ce Benazir er ajinmu) take ran Benazir ya sosu wato bazai iya presenting dinta a matsayin budurwan shi ba?sannan yajuyo itama yace mata bena this is Fulani my sister…kallon ta tayi tace wow nice meeting u ( naji dadin haduwa dake),amma bai gaya miki gaskiya ba I’m his girlfriend(ni budurwan shi ce) ta karishe maganan ne tare da kashe mata ido daya,murmushi kawai Nihal tayi don tadin su yanason tuno mata wani Abun da yashafi saurayi da budurwa,dayan gefen shi tazauna,yazamo sun sashi a tsakiya kenan,ta kaddun ta bena ta fitar tana ce mishi tun dazu fa nake jiranka muyi karatu,a hankali yace mata amma dai kinsan bana iya karatu da mutane ko,juyawa sukai suka kalli Nihal don bayason tajishi sai kuma ma yaga game dinta takeyi,marairai ce fuska tayi tare da langabar da kanta tace amma ai  gashi kazo da sister ka,bakin shi ya cije ya rufe ido ya bude ba tare da yace mata komai ba yaci gaba da karatun shi….babu Wanda yasake magana har suka gama karatu,tattara takaddun shi yayi yana duba agogo yaga har karfe daya yayi,yace Fulani kinajin yunwa ko? Tashi muje muci abinci kafun muwuce gida,bena sake baki tayi tana kallon ikon Allah don taga kamar ya manta da ita awajen, har sun tashi sai Nihal tace ya Ahmad, nuna mishi ita tayi da ido,kallon ta yayi yace bena ki tashi muje mana yanaga kina zaune tura baki tai tace ai jinai ba'a nemeni ba,goshin shi ya dafa yace ok I’m sorry, ki tashi muje itama tattara nata takaddun  tayi.

saida sukaci abinci sannan yacewa bena zasu wuce ko itama zata tafine sai su ajiye ta bata fuska tayi tace a'ah,saidai inada magana da kai,aranshi yace nashiga uku dajaraban yarinyan nan, a fili kuma yace ok, key motan ya mikawa Nihal yace taje ta jirashi..

Tana bude motan ya yasir na kiranta dauka tayi tana murmushi tace kaddai har yaya ya rigamu dawowa?shima murmushin yayi yace a ah amma dai nakusa,nakira ne inji yaya kuke,ko kun koma gida?tace muna lafiya yaya kuma yanzu muke shirin komawa gida,yace ina Ahmad din?juyawa tayi ta kalleshi tace gashi can ,yace ke din a ina yabarki naji kina cewa gashi can,tace muna tare fa har zamu shiga mota ne wata course mate din shi tace zasuyi magana shine tace injira shi,murmushi yayi yace Ahmad kenan, yanzu dai sai kun koma zan kira ki kinji,ki kula da kanki…murmushi tayi tace toh yayanmu Allah yadawo dakai lafiya, yace Amin suka kashe wayan.


Suna kebewa ya bata rai yace mata meye kuma?take idonta yayi narai narai zatayi kuka,idon shi ya rufe ya daga kanshi sama,sannan yace haba bena u knw I hate it(natsani haka)yanzu meye aka miki na kuka?daidai ta kanshi yayi ya sassauta muryanshi ta hanyar lallashi yace it’s ok,kinji kinsan banason ina ganin hawayen ki koda yaushe ,nasan akan maganan Fulani ne kuma na gaya miki sister nane,and u’ve to trust me(ki yarda dani),hawayen ta yashiga share mata ita kuma ta kafeshi da ido kamar yau yafara ganin shi,hannun ta ya riqe yace bena trust me I love u,kai ta  girgiza mishi halamun gamsuwa tare da mishi murmushi,shima murmushin ya mata yace sai munyi waya ko ,tace toh.


Ahmad mishkilin saurayi ne Wanda baya shiga harakan maza ma balle mata,tunda yazo makarantan yake fama da en mata wannan dalilin shiyasa yakara tsanani akan halayen shi don ya lura inya biye musu bazaiyi karatu ba,baya taba sake musu duk yadda sukeso,yahadu da Benazir ne ta dalilin wani friend din shi Wanda cousin dinta ne,ya hadasu ne don yana koya mata karatu da farko Ahmad yaki saboda bayason hidima da en matan uni maid don duk basuda kamun kai inji da fada,amma haka yanace mishi saida ta yadda.

da farko baya sake Mata amma yau da gobe yafi gaban wasa dole suka saba har yadawo inbai ganta ba shida kanshi zai nemeta itama haka,babu yadda bena batayi ba wajen danne soyayyan Ahmad aranta ba amma abun yagagara saboda Ahmad irin mazan da en mata basa kauda kai akansu bayan kyan da Allah ya bashi yabashi kamala da kwarjini,lokacin da bena tafara nuna mishi soyayya yaso yaqi amma sai shima yaji bazai iya watsa mata kasa a idon ba,kuma ya lura da yadda kawayenta kemata saboda shi,shiyasa shima ya dauki damaran basu mamaki,a haka soyayya me zafi ta kullu tsakanin su….dalilin shi bena taki kowane saurayi balle maganan aure,shikuma yanzu yafara gane shakuwa gashi shi kuma Bahama kawo maganan aure aranshi…saidai yanajin tausayin ta don tana sonshi dayawa, wannan shine takaicacen labarin bena da Ahmad.


***misalin karfe goma yatashi saboda baccin da bai samu jiya ba,duk da haka ma a gajiye ya tashi tare da lissafi kala kala da suke yawo a kwakwalwan shi…wayanshi yafara jawowa yana kallon hoton ta da aka tura mishi jiya yana shafa hoton yana cewa Dan Allah duk rintsi karki rabu dani Nihal kece rayuwa ta,kuma ina shirye da inyi komai a kanki…dasauri yafara Neman Yusuf a waya yana dauka yace badai sai yanzu kaga saqonni na ba?kanshi ya shafa yace wallahi tun jiya nagani issues ne sukamin yawa,yanzu dai abokina akwai matsala don dole indawo borno,kuma yaya za'ayi Mugane guyen da suke tare?yusuf yace gaskiya bansan shiba gashi kaga Maiduguri yanada yawa,saidai kawai nasan inna Ganshi zan ganeshi,kuma karka ka dawo ba tare da sanin daddy ba sannan ka lallaba shi karka bari yahanaka,saboda biyayya wa iyaye yana daya daga cikin sirrin samun nasara…ji yayi duk jikin shi yayi sanyi yace inshaa Allah abokina zan kiyaye…


Ya yasir bayan yadawo yaci abinci,Nihal ya kira tabashi labarin unimaid,Ahmad yanajinsu yafito, nan fa tafara dariya daga sun hada ido da Ahmad sai ta fashe da dariya,yasir ma dariyan yafara shiko Ahmad hararan wasa yafara mata don yasan abunda takeson fada,dakyar tasamu tadaina dariyan tace hmm…yaya kaga yadda en mata suke leken mu da suka ganmu tare,yace ainasan za'a Rina donma Ahmad gonin baqin hali ne watakila da har gida zasuna biyoshi,tace yaya kaga wata budurwan shi wallahi ta hadu gata da shegen kishi, kushin din kujera Ahmad yadauka ya wurga mata yace ai gobe ba zanje dake ba balle ki kwaso gulma,tashi yayi yakama hanyan dakin shi  da sauri tabi shi tana cewa haba ya Ahmad dina Dan Allah kayi hakuri wallahi nadaina,tana isa yana rufo kofan dakin,yasir ne yace rabu dashi zoki karisa min labarin,tace nikam babu ruwana kalen gobe yaqi fita dani…shima daya tura kofan dakin jingina yayi a jiki yana murmushi yace she’s amazing….

maa ma daga dakin ta tana juyo su dariya tayi tace Alhamdulillah lallai Fulani haske ce a rayuwar mu,rabon da inji yarana suna farin ciki haka tun rasuwan babansu,hawaye ne ya gangaro mata ta goge,soyayyan yarinyan ne taji yana ninkuwa a cikin zuciyata.

Zuwa tai ta zauna tace ya yasir yaushe kaima zaka kaini wajen budurwan ka?murmushi yayi ya jingina da kujera yace mata aini banida budurwa, baki ta bude sannan ta tabe baki tace Allah bazan yadda ba,kaima nasan innaje wajen aikin ka zanga masu crushing akan yaya na,dariya kawai yayi ya mike yace mata nidai bari naje huta don na lura kaina zaki dawo,itama tashi tayi tana cewa nima bari inje wajen mama na tunda duk kun gudu,tawuce dakin maa.



*Abdlzty💞*

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now