💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥
By :Zeety A-Z💞
Wattpad@Zeety-AZ
📙05
*** samari ne hudu a zaune a majalisan su dakagansu kaga yaran Fulani masuji da kyau,daya acikinsu kuma dakaganshi Kasan boko ya ratsashi tundaga shigarshi zaka San yafi sauran wayewa…
wanda ke gefenshi ne ya dafashi yace yanzu abokina haka zaka zuba ido kana jiran yarinyan daba asan inda tashiga ba?Wanda yake danna waya a hanunshi ne ba tare da ya kallesu ba yace atoh ilu fadamar dai wayasan ma ko yawon bariki taje bayan tadawo a hadaka da fanko, kwaliii.. Bushewa sukayi da dariya dukansu, shidai gogan harara kawai yabisu dashi, Sai Wanda yadanyi duhu ne a cikin su yace Kasan meye khalifa? katashi kawai mu rakaka kaje kasamu baban yarinyan nan kace mishi kafasa, ajiyan zuciya yayi tare da sa hannu shi duka biyu a aljihun wondon shi yace Nima hakan nake tunani amma Sai anyi magrib zanje insa meshi don gsky bazan iya jiranta ba, kuma ko na jirata ma bansan da me zata dawo ba,zubair ne yace shine magana mutumina…
Abban Nihal yana fita police station ya nufa yayi reporting sannan yawuce damaturu yaje gidan TV da radio duka yabada cikiyanta tare da hoton ta ,yana komawa jajere a tashan mota ya tsaya yaji ko ansamu wani lbr akanta saidai babu wani labari,Sannan yawuce gidan surkanshi kai tsaye nan ya shaidawa su bappah halin da ake ciki tun jiya,abun bakaramin girgizasu yayi ba….Tunda ya fita Ammie tasamu karfin halin ayukanta amma Sam takasa samun nutsuwa acikin ranta ko abinci takasa ci don haka ta yanke shawaran Kiran mijinta ta tambayeshi Izinin zuwa gidansu ko zata samu relief..
Lokacin data kirashi yayi daidai da yana tare da iyayenta yana ganin kiran ya kalli inna yace ga Ammie na kirana bari inji ko ansamo wani labari ne, da sauri inna tace maza dauka Dan nan, yana picking tagaya mishi tanason zuwa gida,yace mata to badamuwa Nima yanzu ina gidan kizo idan anyi magrib sai mu koma tare,da hanzari ta ansa da toh sannan ta katse wayan. Yace gatanan ma zuwa yanzu inna tace Allah yakawota lafiya.duka sukayi shuru kowa da abunda yake tunani aranshi..
Baifi minti sha biyar ba sai gatanan ta iso,karisawa tayi tace bappah ina yini? Lfy fatima, ya mukaji da hakurin musiban datazo mana kuma?tace Alhamdulillah bappah, saifa addu'a Fatima bacci bai samemu ba kuma kisawa ranki salama kinsan komai yasamu bawa dasanin ubangijin shi kai kawai take jinjinawa,inna ya kalla yace ki shiga ciki da ita zamu tattauna da Ahmad din,inna tace toh nan suka mike suka shige dakin inna..sai da suka zauna tace ina wuni inna? Lfy En nan, sai kuma muka tashi da tashin hankali,en hawayen datake dannewa ne suka gangaro ba shiri,tace inna jiya da safe fa lafiya muka tashi da yariyan nan tagama shirinta tsaf zata koma makaranta saboda dama hutun karshen sati tazo(weekend) na rokota har kofan gida muka jira mashin babu Wanda yawuce shine tace rana zai mata bari tadan taka ko zata samu agaba nace mata toh Allah ya tsare,ta tafi..jin har la'asar bata kirani ba shiyasa nakira wayanta naji akashe,sai nayi tunanin ko cajine batada shi. Bayan magrib sai na sake kira naji akashe shine na kira wayan kawarta nake tambayanta sai take cemin ai Nihal batadawo ba, nan ne naji numfashi namin kadan a take na mike nace mata bangane ba tun safe fa ta tafi, tace wlh Ammie bawasa nake miki ba dagaske bata dawo ba tundaga lokacin bamu samu kwanciyar hankali ba duk Inda mukasan zamu nemeta Nihal bata wajen, kuma na tabbata Nihal babu Inda zata shiga bata gayamin ba kuka Ammie takeyi sosai...
inna kuma sai salati takeyi tana tafa hannu can tadaga hannu ta sama tace “Ya Allah badon halayen mu badon munkai ba sai don daraja manzo(SAW) Kabaiya na mana Nihal kuma karaba ta dashiga mummunan hannu ya Rabbul izzaty, Ammie ta amsa da Amin
Bayan magrib inna yakawo musu abinci dakyar ta lallaba Ammie taci,sannan tace mata maza kije kisamu mijinki Ku koma gida dare nayi,bata fuska tayi tace nikam inna dama yabarni na kwana wallahi tunda yagayawa yayunshi suka gayawa matansu tun jiya habaici da gori kawai sukemin... inna tace hakuri zakiyi Fatima wannan dalilin bazaisa kidawo gida ba kuma shima yana cikin tashin hankali kamar yadda kike ciki don haka Ku koma kina kwantarwa da mijinki hankali kinji Allah yayi muku albarka tace Amin, tare sukaje side din bappah,suna zuwa suka samu yayanta ma yazo wanda Suke kira da hamma, yana aiki a damaturu ne kuma ba laifi Allah ya buda mishi don duk wani hidiman gidan su shiya dauki nauyi,Nihal ma yawancin rayuwanta na damaturu a gidan shi takeyi,tunda Ammie tasanar dashi halin da ake ciki bai samu nutsuwa ba,shiyasa yana gama abubuwan office Dana gida yakamo hanya..Haka dai sukayita jajanta abun daga karshe bappah yace dare nayi su Ammie su tafi gidan su shima hamma ya wuce masaukin shi kuma inshaa Allah gobe zai rarraba a masallatai da wajen malamai a tayasu da addu'a, sannan inna tace gobe kar Ammie ta fito ta zauna a gidan ta zata turama kanneta suje su tayata zama nan bappah ya rufa musu taron da addu’a kuma suka rakasu har kofan gida.
bayan sun fitone Abba yake gayawa hamma akan yayi processing transfer zuwa damaturu tun last 2 months kuma any moment zai iya fitowa, amma fa gsky shi yanzu ko ya fito ma bazai iya barin jajere ba tare da Nihal ba,ajiyan zuciya hamma yasauke sannan ya dafa kafadan Abba yace, karka damu Ahmad inshaa Allah za'a sameta Ku kwantar da hankalinku…hamma ne yakai su gida,suna sauka suka hango samari uku a duhu,hamma ne yace suwaye wayancan haka ajikin gidan Ku kamar marassa gaskiya? Abba yace bari na duba nagani,yana fita Ammie tasa hannu zata bude motan hamma yace a'ah Fatima bari dai yadawo muji, suna jiyoshi da yaran,yana isa yace Assalamu alaikum suwaye haka da Daren nan ? yana haskasu da wayanshi,sai yaga su khalifa ne kashe haske wayan yayi yace khalifa kune a Daren nan lafiya dai kam?khalifa na Sosa qeya abokan shi kuma duk sun tokare kamar dogarai,yace dama Abba tun magriba Muke jiran ka akace bakanan shine mukajira,Abba yace toh Allah yasa dai lafiya,Ammie tunda taji khalifa ne zuciyanta yafara bugawa,hamma ne yajuyo yace mata kodai yaron da aka baiwa Nihal ne? Kai kawai ta iya daga mishi,take ya bude motan yakarisa wajensu.
Dama Abba nazone akan maganan Nihal ,ina jinka,toh gsky baba ayi hakuri ni nafasa,abokan shi sai wani kada kai suke kamar kadangaru,wani mugun kallon Abba ya watsa mishi yace idan kafasa din Kaine zakazo katsaya mana kamar sanda kafasa?ko kuma tun ranan farko Kaine dakanka kazo muka ce mun baka? Kaje katuro magabatan ka saimuyi magana amma bada kai.. Caraf illu ya cabe gaskiyar magana dai shine ko sunzo ma mukam munfasa zubair yace ehe, hamma ne yace to ai dama walkiya ce ta haska muma kota dawo bazamu hadata da ire iren yara maras sa da'a kamar Ku ba,kuje Ku turosu,daga haka Abba da hamma suka juya sukabarsu sunata qunquni.saida sukaje jikin mota hamma yace wai Ahmad tun farko ina kuke gani kuka hada erku da fitsararrun yara irin wannan? Ajiyan zuciya Abba yayi yace wlh hamma tunda muke da yaron nan bai taba nuna mana irin wannan halin ba kuma bansan shi da yaran nan ba saboda shi tun hasalima ba'a garin nan yayi karatu ba, kuma kowa ya shaida yanada hankali yaron nan…iska hamma ya fetsar yace Allah ya kyauta, kuma ko Nihal tadawo bazata auri wannan yaron bakam,mota ya leka yace Fatima kifito kushiga gida…
fitowa tayi kamar kwai yafashe mata a ciki tayi kuka harta gaji…hamma ne yakaleta yace Fatima dole fa saikin koyi hakuri a rayuwan nan bakomai akeyiwa kuka ba,akwai abubuwan dasunfi karfi kuka saidai addu'a don haka ki kiyaye, mikawa Abba hannu sukayi musabaha kowa yawuce gida.
Tunda su khalifa suka kama hanyan gida abokan shi suketa ketata dariya shikam tafiya kawai yakeyi amma hakalinshi baya jikin shi suna isowa wajen gidan su khalifa babu Wanda yayiwa magana kawai yashige gida, sake Baki sukayi suka bishi da kallo,zubair ne ya kece da dariya yace wlh ilu batan yarinyan nan yamin dadi Allah yasa ma wayanda suka saceta sumata fyade…ilu shafa habarshi yayi yana lashe baki yace wlh dasun more don daganin yarinyan nan zata kawo light, tafawa sukayi sukaci gaba da tafiya.
*Abdlzty💞*