23

35 4 2
                                    

💥 *HASKEN RAYUWA TAH* 💥



By :Zeety A-Z💞



Wattpad@Zeety-AZ




📙23



Fita sukaiyi,su kuma suka koma ciki....

Ahmad ne yabisu da ido yanason ya tambayesu ya sukayi kuma baison ayi maganan gaban Nihal, waje duk suka samu suka zauna...

sannan yasir ya kira sunanta Nihal! Karo na farko dataji yakirata da sunan ta kenan dagowa tai tana kallon shi ba tare da tace uffan ba.

Shuru ne yadan gifta sannan yace, Zaki iya bamu labarin ki,don halamu ya nuna kin tuno ke waye ce...shuru tai ta kalli kasa sai hawayen daya fara ambaliya a fuskan ta... babu Wanda yayi magana don basason takura mata,sanda tayi kuka me isanta sannan ta share hawayen ta tafara.


Sunana NIHAL AHMAD ni asalin er garin jajere ce dake jihan Yobe, babana ma'aikacin asibiti ne mamana kuma malamar makaranta ce,ni kadai iyayena suka aifa tun bayan aihuwa ta Ammie na ko bari bata sakeyi ba, nasamu kulawa mekyau da gata dakuma tarbiya a wajen iyayena, Ammie na da Abba na suna so na sosai amma wannan dalilin baisa sunbarni na lalace ba.

akaf duniya ta banida kawar data wuce Ammie na, tafi kusa dani akan ko wace kawata,bana tabayin abu ba tare da shawaranta ba,haka rayuwa ta taso dagani sai Ammie na da Abba na,ko ciwon kai yasameni Ammie bata samu nutsuwa harsai nawarke.

A lokacin Dana gama secondary school ina jiran fitowa result a wannan lokacin khalifa ya shigo rayuwa ta,duk saurayin da yamin magana idan nagayawa Ammie na ita take cemin in fita a harakan duk Wanda zai tsareni a waje ba mutumin kirki bane,amma khalifa duk da yaganni a waje bai tareni ba saida yabari nadawo gida sannan yazo har gida,wannan dalilin ne yasa Ammie na tace inkarbeshi kar in wulakanta shi ko banason shi sannan kuma bawai tace inje zubda mutunci na ba,inkula dakaina don halamun ya nuna yaron kirki ne.


A haka mukafara da khalifa ahankali soyayya me karfi ta shiga tsakanin mu har nasamu admission a school of nursing damaturu, Kusan duk wani hidiman makaranta tare mukeyi dashi, haka kuma ko bana gida zaije ya gaida Ammie harsuyi tadi, ba'a dau lokaci ba ya tura iyayenshi aka bashi ni,kullum soyayya mu karuwa takeyi khalifa yanasona kamar ya hadiyeni,amma duk da haka baitaba nuna sha'awan tabani ba ko kadan.

Huh!wani weekend nazo gida zan koma makaranta narasa mashin din dazai kaini tasha haka na taka harkusa da tashan anan naga wani private car tana lodin damaturu har zan wuce su naji sun dage da damaturu mutun daya,duba agogo nayi naga na makara gashi inna shiga tasha ba lallai insamu motan daya cika ba,don haka kawai na yanke shawaran shiga wancan motan,ina shiga naga nikadai ce mace a motan kuma saida muka fara tafiya na lura da kamar ba passengers bane a motan tundaga lokacin zuciya ta tafara tsinkewa nafara addu'a acikin zuciya ta,bankara tabbatar da zatona ba saida naji suna waya suna cewa tunda kaki kawo mana ita munzo mun dauketa dakan mu gata nan a hannu mu, innalillahi wa'inna ilayhir raji'un shine abunda nafara fada a fili hankali nane ya tashi sosai.

naciro wayana zan kira Ammie,suka wafce wayan kuka nafarayi ina rokonsu su maidani gida amma ko kallo na basayi saima gudun dasuka kara kamar zasu tashi sama,karshe ma sai gani nai sun shiga jeji saida muka kai tsakiyan jejin kafun sukai parking, Ashe akwai wani motan dayake binmu a bayan,juyawan dazanyi don ganin motan saina Ashe motan khalifa ne,fito dani sukai suka samin bindiga akaina take khalifa ya zube yahau rokonsu akan sukyaleni su tafi dashi... Sam suka dage akan nidin sukeso nan suka hau wasu surutan da suka firgitani,wai khalifa yana kungiyan matsafa kuma Shiya badani take yafara ihu yana cemin kar in yadda dasu karya sukeyi....

anan ne duka sukaje kanshi suka kyaleni a take dabaran gudu yazomin ahankali na lallaba nasa gudu, gudu nakeyi sosai kamar raina zai fita inajin khalifa yana kwallamin kira amma nakasa zuwa gareshi,don bansan dawa daya zan yadda ba,su ne ko shi?a haka harnakai bakin hanya tundaga nan kuma bansan meya kara faruwa ba .... Kuka ne ya balle mata sosai wajen kowa yayi shuru da tunani kala kala aransu.

cikin sheshekan kuka tace nasan yanzu haka Ammie na nacikin tashin hankali ba kadan ba,sosai ta basu tausayi tareda karya musu zuciya, maagana ce tazo ta rungumeta tace kiyi hakuri inshaa Allah komai yazo karshe kuma Ammie ki ma bakin cikinta yakare.




*Abdlzty💞*

HASKEN RAYUWA TAHWhere stories live. Discover now