ALMAJIRI NA.......PAGE 4

3.1K 135 6
                                    





A wannan satin Hajiya Safiyyah ba zata iya tantance halin da take ciki ba, murna ne saboda ta san ta samo mafitar matsalar ta, ko kuwa baqin cikin rashin mijin ta a kusa, wanda ta tabbata dayan biyu ne, ko yayi tafiya qasar waje, ko kuma kashe wayar shi ya yi yana cikin garin.

Sati biyu sun wuce ba alamar bayyanar Alhaji, dan haka yau wanka tayi tin safe ta shirya cikin atampar ta mai tsadar gaske ta sha gayu, Yaseer na zaune yana karyawa ta wuce, motar ta ta shige ta dau hanyar Katsina, can a wani qauye mai nisan gaske ta nausa motar ta, ta yi tafiyar awa biyu kafin ta tsaya a wata bukka, wadda ita daya ce a dajin, ko tsoro ba bu a ran ta, burin ta kawai ta samu biyan buqatar ta.

Wani siririn mutum ne fari ya fito a bukkar, yana ganin ta ya washe baki, haqoran shi da gani tin da ya fara haqora yana yaro bai taba wanke su ba,hammatar nan ta yi kore shar saboda rashin wanka, wari kamar mutum ya sheqa amai, dik da tashin zuciyar da Hajiya ke ji bai hana ta isa cikin bukkar ba, yana zama itama ta zauna,

"Ran boka makau ya dade, boka ka taimake ni, wannan karon ban san wace iriyar yarinya Alhaji ya samu ba,yau satin shi biyu baya gida, na shiga damuwa na rasa ina zan saka kai na, in ya qara aure mutuwa zan boka"

Kuka ta saka sosai, kamar zata hadiyi zuciya(ta kasa kokawa gaban Allah dan neman biyan buqata tana kokawa gaban bawan Allah)

"Daina kuka Hajiya, kin zo wajen da za a share maki hawaye, kema kin san indai kinyi imani da mu baki da matsala,"

Share hawayen ta tayi,saboda da gaske tayi imani da shi sosai, bata taba kawo masa kukan ta bai share mata hawaye ba.

Tashi ya yi tsaye ya hau zagaye ta, yana surkulle, tare da yarfa wani abu mai kama da gashin dawisu.

Zama ya yi ya dakko wata kwarya ya aje, nan da nan sai ga ruwa a cikin ta, surkulle ya fara sai ga hoton Alhaji yana kwance a wani hotel, da ke a cikin garin nasu, dubawa sukai suka ga sunan Hotel shi da wata yarinya, dan haka ya sa hannu ya share hoton,

Hajiya kuka ta ke sosai, saboda ganin mijin ta kwance da wata a qirjin shi, tana shafawa,

"Lallai kina son mijin ki, son da har yanzu ban hango iyakar shi ba, amma ki sani, mijin ki mai son mace ne sama da daya, ya dade yana wannan harkar tin kafin auren ki manemin mata ne, bayan auren ku zuwa yanzu ya yi wa mata ciki ba su da adadi, wasu an haife masa, wasu sun zubar, wasu sun mace wajen haifar su, akwai dan shi ko 'yar shi da zata buwaye ku a nan gaban rayuwar ku, na duba iya dubana na kasa gane ina yake ko nace ina take, kuma na kasa gane inda yake ko nace take, sai dai zan baki shawara ki yi taka tsantsan, wannan kuma da take tare da shi ki je yau ba sai gobe ba, ki hura mata wannan tana shaqa an gama da shafin ta, zata tsani mijin ki tsana mai tsanani, shima kuma haka, zaki tafi da mijin ki gida,"

Ta shiga rudani sosai, amma ita ba wai sabon labarin da taji bane abinda yake damun ta, indai mijin ta zai kasance tare da ita koma me zai faru ya faru.

Kauda damuwar ta tayi ta bude jakar ta ta fiddo kudi ta aje, ta na ta zabga godiya, maganin ya dauko mata a cikin wata jar fata,ta amsa tana godiya.

Hanyar komawa ta dauka, ta isa cikin gari da la'asar, saboda cinkoso da ta samu, direct hotel din ta isa, tana zuwa ta je wajen masu kula da hotel din, da kyar ta samu aka barta shigewa wajen dakunan, bayan ta nuna masu shaidar mijin ta ne tana son tai suprising din shi ne, dan haka bata son a sanar da shi zuwan ta, sai da ta dudduba sannan ta gano number dakin da yake, a qofar dakin ta tsaya ta jima dan taji meke faruwa, shiru taji ba alamar motsin kowa, dan haka ta bude a hankali, kwance ta gan shi yana ta sheqa bacci, hankali kwance, cikin sanda ta rufe qofar, ta bude jakar ta ta bude yar fatar ta hura masa maganin, kayan ta ta cire ta fada wanka abun ta hankalin ta kwance, tana wanka ta ji an bude qofar da qarfi, yana ganin ta ya yi baya da sauri,

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now