ALMAJIRI NA....PAGE 40

1.9K 157 11
                                    

Suna asibiti, Alhaji ya je, Habi ta ci kuka ta gode Allah, Alhaji wajen likita ya nufa, anan ne likita ke sanar da shi hawan jinin Hajiyan ya tsananta, tana buqatar hutu sosai, ta samu isasshen bacci, da nutsuwa daga dukkan damuwa, sannan ya rubuta magunguna da za a sai mata, Alhaji sai da ya biya bills din komai sannan ya shiga dakin da aka kwantar da ita, Habi na ganin shi ta fice, kallon inda ta bi ya yi, sannan ya maida hankalin shi wajen Hajiya .

"Ya jikin na ki?"

"Da sauqi "

"Allah ya qara lafiya, kina buqatar wani abu ne?"

"Eh"

"Ok me ye shi inna fita na taho Ma ki da shi ?"

"Alhaji ka yi wa Allah kar ka auri Habi, Habi dattijuwa ce fa, me zata iya tsinana maka? Matar da tare muke qulla komai a baya da ita, na san sharrin ta, ta san nawa, dan Allah ka auri kowacce mace amma banda Habi, na amince ka auri wata bana son Habi"

"Habi na ke so, ita na ga damar aura, ki amince shine zai fi Maki sauqi a rayuwar ki, rashin amincewar ki da qin kwantar da hankalin ki zai iya ja maki tawaya, wadda zata ja bayan Habi ma na qaro wasu, U better get well soon ok?"

Kuka Hajiya kawai take, dan ta kula yanda ya dau lamarin sai ya yi abinda ya qudurta, sai dai daga baya ya yi dana sani.

"Likita ya ce a dafa maki zobo ki Sha ba sugar Yana maganin hawan jini, dan haka za mu je gida da Habi ta dafa a kawo maki, in Ki na son lafiyar ki, ki sha ki warke, In Baki son lafiyar ki, kar ki sha,"

"Alhaji Ni ce fa, babyn ba, farin cikin ka, wadda In ka kalle ta ka ke samun nutsuwa, Ni ka ke wulaqantawa haka?"

"Zancen kike so, sanda ki ka gama yawo da Ni gidajen bokayen ki, kin tuna Ni waye a wajen ki? Ko sanda kike kwanciya da dan ciki na kin tuna Ni waye? Sanda kike lalata rayuwar duk macen da na so aura kin tuna farin ciki na da kike rusawa? Mata nawa ki kai sanadiyyar ran su a saboda kishi? In kika ga ban auri Habi ba Allah bai qaddara akwai aure a tsakanin mu ba"

Fita ya yi ya barta tana kuka sosai mai cin rai, koda suka shiga Mota Habi shiru ta yi kunya duk ta kama ta, Alhaji kam ko bata girme shi da yawa ba zata bashi shekara biyu, zuwa uku, qanin ta ne amma yake qoqarin auren ta, tana tsaka da tunani ta ji maganar shi.

"Ina fatan duk abinda na fada ba ki dauke shi da wasa ba, ina son amincewar ki, ba bata lokaci za a yi ba, ke ma ki shigo ki ci daular da na tara, da ke aka wahala, kema hutu ya zo miki, aikin gidan ya qare maki me ye ra'ayin ki?"

"Alhaji sai na yi shawara da yara na"

"Ba matsala, ina jiran amsar ki, muje yanzu ki dafa mata zobo kar a sa komai a ba ta, ta sha inshaa Allah zata ji sauqi, kar ta tsorata. Ki, kar kuma ki ga Kamar kin yi butulci, ba abinda zan ce Ma ki sai godiya, kin dade kina bauta a qarqashin mu, yanzu Allah ya yi daukakar ki ta zo"

Ita dai Habi ba baki, jinjina lamarin kawai take, suna shiga ta debi zobo ta dauraye, ta zuba ruwa ya dahu sosai, sannan ta tace, ta juye a flask ta dauka, driver ya maida ta asibitin.

Suna shiga Hajiya na kwance tana kallon ceiling idanun ta na zubar da hawaye ta gefe, jin motsin qofa ne ya sa ta juya, suna hada ido da Habi ta fara qoqarin tashi, ranta a tsananin bace.

"Habi ashe abinda zaki saka min da shi kenan, ki je wajen bokaye a Maki asirin da zaki auren miji? lallai ke butulu ce, kin dai san kar ta san kar ne Ni da ke ko? Mu zuba mu gani shege ka fasa, Allah ya bani lafiya, zan nuna miki Ni na fi ki zama 'yar zamani"

Ran Habi ya ɓaci sosai,da qazafin da Hajiya ta mata, asiri kuma? Ita da ta zo ta ce mata zata bar aikin, saboda ba zata iya auren shi ba, shi ne zata balbale ta da fada haka.

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now