Zama ta Yi sosai a jikin shi sannan ta Daga Kai tana kallon cikin idon shi, numfashin shi na sauka a fuskar ta, ta ce,
"Na amince dari bisa dari, na yarda da Kai, fatana Allah ya Kare min Kai, ya Kuma bada sa'a, Allah ya Sanya albarka"
"Ameen my Honeybee"
Fuskokin su suka hada waje Daya, tare da lumshe ido, su na Jin wani irin shauqin son junan su, yarda, aminci, qauna, tare da girmamawa.
Sun jima a hakan, daga baya Maryama ta janye fuskar ta, sannan ta ce,
"Mu je ka yi wanka , sai ka shirya ka sanar da su Mama abinda ke akwai ko?"
Hakan kuwa akai, sai da Naseer ya dawo sannan suka shiga sashen Maman, tana zaune a qasa yaran na gaban ta, Nasreen na jingine da ita, saboda Bata kware a zama ba sosai, sai Lamido da ya tankwashe qafa daya Yana Shan lemon fata.
Sallamar su ne ta Sa ya daga Kai ya kalle su, ya maida Kai abun shi, ya fi sakewa da Nusrah akan iyayen nashi, ita ce komai na shi, a wajen su ya ke kwana, tun daga yaye.
Zama Maryama ta Yi itama, ta dau lemon daya, little ma haka,
"Daga zuwa ba Wanda ya maku tayi KU sa Mana hannu?"
"Mama mun hutar da ke magana ne, na San an jima kadan za ki ce Mana Bismillah"
"Ni ban ce Miki zan maku Bismillah ba, ko Lamido ?"
Daga Kai ya Yi, Yana ci gaba da Shan lemon shi
"Dannema dama in ta Kai ne ai ba zamu Sha ba"
Little ne ya kalli hanyar dakin su, ya ce.
"Daddy fa? Ko Bai dawo ba ne?"
"Ya dawo, Yana ciki, wanka ya fito,"
"Wa ke tambayar daddy? Ga wani"
Gyara zaman su sukayi, musamman Maryama da ta baje a gaban lemo, bayan sun gaishe shi, little ya bayyana musu abinda ya kawo shi, Nan suka bashi shawarwari, sannan suka ce anjima a wajen dinner ya sanar da su Ammaa, Hira suka yi ta yi abun su, lokacin Dora girki na yi, Nusrah da Maryama suka bar yaran wajen su Naseer, suka nufi bangaren Ammaa, ta qofar baya suka shiga, suka hau aikin su.
Da dare bayan sun Gama dinner little ya sanar da su, aikin da Hajiya Safiyyah ta ce zata bashi a company'n da Alhaji ya bar Mata, zai zama shi ne CEO, tunda ita Bata San harkokin kasuwanci ba, company na neman durqushewa.
Ammaa da Abbaa sun Yi farin ciki da Jin hakan, ko ba komai, little din zai Dora daga abinda mahaifin shi ya yi.
Ta waya ya Fara sanar da Mum din, kafin safiya ta haɗa dik wasu takardu, Kuma ta sanar da ma'aikatan wajen meeting da za su yi gobe da misalin 8:00am.
Maryama a daren ranar ba ta Yi bacci sosai ba, ta tashi ta yi alwala ta yi sallah, sannan ta roqi Allah, in akwai alkhairi Allah ya tabbatar, in Babu, Allah ya yi mishi musanya da inda ya fi alkhairi, sannan ta mishi addu'ar neman tsarin Allah akan dikkan wani sharri.
Tana idarwa ta ji wani kwanciyar hankali, da nutsuwa sun shige ta, bacci Mai Dadi ya dauke ta.
Da asuba suna yin sallah, ta je hada mishi abun karyawa, ya yi wanka, ya shirya cikin manyan kaya farare, sun karbe shi sosai ,ya yi kyau, Maryama ta zaci za ta ji kishin fitar shi a haka, sai ta ji ba komai a zuciyar ta, tabbas wannan tasirin addu'a ne, ta sani ba komai ba.
Bakwai da rabi ya gama yi ma kowa sallama, ya shiga mota, Maryama ce tsaye dauke da Lamido a hannu, suna mishi addu'ar Allah ya kiyaye, Lamido ba a gane komi, sai qoqarin maimaita abinda ta fada ya ke, little na fita daga gidan ta koma bangaren su.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......