Daure ki/ka karanta daga farko zuwa qarshe, kamar yanda ki/ka karanta labarin, wannan ma zai taimake ki/ka inshaa Allahu.
Da farko zan roqi Wandan da suka bude Wattpad saboda karanta novel din ALMAJIRI NA in dai domin shi kuka bude to an Kai qarshe KU Yi wa Allah KU rufe, saboda Wattpad waje ne da marubutan duniya sure ciki, za KU ga novel Mai amfani da amfanarwa , sannan akwai lalatattun marubuta na gida da qetare, bana fatan na zama sanadiyyar lalacewar kowa a cikin KU, Ina maku fatan ci gaba da kasancewa nagartattu inshaa Allahu.
In Kuma Kuna ganin za KU bar shi, Kuna son ci gaba da karanta wasu novels din, akwai novels na mutanen da ba su lalata tarbiyya, novel kowanne iri ne indai kuka Fara kuka ji akwai batsa a ciki ku ji tsoron Allah Wanda ya ke qirga fitar numfashi da qiftawar idanun KU, ku cire shi a library din KU, Kar KU karanta shi, in kuka karanta u are on ur own ooo, Ni ba ruwa na, na gode da qaunar da kuke nunawa rubutu na.
Nasiha ta a gare ku MARUBUTA, Wai me ne ne dalilin KU da hujjar KU na rubuta kalamai da zantuka da simfanta Zina da batsa a rubutun KU, ta yanda in mutum na karantawa zai dinga Jin sunayen al'aura baro baro a rubutun KU, sannan zai ji yanda ake saduwar aure balo balo a rubutun KU, saduwar ma ta zina, wasu Kuma na aure? Shin dabbobi hankali suka fi ku ne? Ko me? Domin kuwa da Allah ya bawa dabbobi hankalin da ya bamu da ba su sadu a gaban kowa ba, za su buya kafin su sadu da junan su.
Wani novel din an maida mutane Basu San me su ke ba, ko marubutan suna tunanin su kadai ke karanta novels din turanci, ko Kuma kallon films din qetare, sai kiji novel an juya na turanci zuwa hausa, misali Kai ka je karantawa ka ji na turancin da batsa ka gudu ka bar shi, sai diyar musulmai, bahaushiya ta je ta fassara maku shi, ka karanta abinda ma baka San fassarar shi ba a ranar za kaji, fassara ce ta rashin mutunci da d'a'a, in an Yi magana kuji marubuta na fadin Basu Bata tarbiyya, ashe da ma ba tarbiyya kuke koyarwa ba tun asali? Me ye motive din rubutun KU? Wata ma fa wallahil Azeem da take taqamar matan hausawa ba su it's sex ba, ko matan hausawa akan sex ake sakin su, bazawara ce, ko Kuma ita kan ta maleji mijin ke yi da ita, zaman ya koma na hakuri, in ya tashi kafta Mata rashin mutunci mutan unguwa ma sai sun ji, Amma a haka zata zo tana rubuta imagination din ta, abinda Bata aiwatarwa ta sa matasa cikin musiba da bala'i, da zunubi.
Kuna nufin ku da kuke taqamar marubuta ne, a barku da Allah, Kar a Mu ku nasiha akan sharrin da kuke yadawa a al'umma, da bala'in da kuke yadawa, da gubar da rubutun KU ke dauke da shi, Allahn abokin wasan KU ne, da zaku nuna KU kun Isa a bar KU da shi? Wallahil dik bawan da sai aikata zunubi, ya aikata ba daidai ba a Masa nasiha, ya ce a barshi da Allah, in mutum na da hankali wallahi nesa zai da wanna bawan saboda Kar Mai shi ya fusata da shi ya hada da Kai a azabtar da shi da zai Yi, Amma da kw Zina tayi katutu a zuqatan mutane yanzu ba 'yan Mata ba, ba matan aure ba, ba kuma.maza ba matan ba, sai KU ga anaqale masu ana zuga su, ana hassada ake maku, Dan an ga kin daukaka, daukakar shiga wuta?
Me ne ne ribar ki/ka a karanta rubutu na batsa, ka/ki tada sha'awa ki/ka biyawa kan ka buqata? Wai Dan tsabar rainin wayo sai a ce an karanta ba aji komai ba, hummmm sannu duwatsu, ashe ba but system din sha'awa kwata kwata a jikin KU? Sun daina aiki ko? In an ce na masu aure ne Dan a Koya masu zamantakewar aure, to shi/ita Mai rubutawar wa ya koyawa iyayen ta saduwar aure har aka haife ta/shi? (I am sorry kalamin ya yi tsauri Amma gaskiya ne)
In Kuna taqamar a musulunci ba a kunya, KU fadan ayar qur'anin da kuka taba karantawa kuka ji sha'awar KU ta tashi, saboda karanta ayar, Ina ce dai qarshen fadakarwa da wa'azi shine qur'ani? KU sanar da mu a wanne hadisin ko fiqh ko wanne irin littafi na magabatan mu sanannu ba 'yan bidi'a ba, Wanda suke bin tafarkin Annabin rahama, kuka karanta ya tada maku da sha'awa.
Me zai Sa KU zama dabbobi Wanda Basu da sirri a gidajen auren su? Duk rubutun duniya in ka nuna Mata da Miji na tare suna soyayya, an San me za ai qarashe da shi, Wanda wani ma ba lallai a qare da saduwa ba, Amma saboda kun zama dabbobi, kun nuna ku a bude sirrin auren ku ya ke shine za KU dinga fadan sunayen al'aura gatsau, da yanda ake saduwa.
Wallahi wallahi mu sani Baki dayan mu, wannan musibun lassa, Corona ,da dai sauran cututtukan na annoba, suna daga cikin mugayen ayyukan mu, in bamu gyara ba, zamu fada komai Allah wuyar fita.
Mu sani a dik abinda muke yi wallahi billahi Allah Yana gani, daidai da tashin tsilin gashi a jikin mu Allah Yana gani, Kuma ya San dalilin tashin shi, balle sha'awa, ya San me muke kallo, me muke karantawa, tunanin mu da komai,mu sani Allah na kallon mu dik duhun inda muka buya muke aikata sabon, sannan duk qanqantar wajen.
Makaranta KU ji tsoron Allah, KU daina karanta batsa, ko novel Kika Fara Kika ji da batsa bar shi, shine samun nutsuwar ki, abun ya fi ban sha'awa mijin ki ya zama shine malamin ki a fannin sex da komai, yafi xama romantic,subhanallah KU duba shekarun Nana Aeeshaa sanda aka aura Mata Annabin rahama, saboda qananun shekarun ta, ya San kusan shi ya Rene ta, Dan haka muke Jin labaran soyayya Mai Dadi da kwantawa a Rai daga gare ta, KU kula da kyau, macen da ta San komai kafin aure wallahi Bata da value din wadda Bata San komai na harkar sex ba, wannan rashin sanin naki a wajen maza ma Yana da nashi tasirin da yake a zuqatan su, koyar da ke din Nan da suke ba qaramin Abu bane a wajen su da suke samun gamsuwa da nishadi, in sun tuna ya zama Yana qara masu son ki.
Makaranta KU ji tsoron Allah, in ba zaku ba marubutan da kuke tare da su shawara akan gyara lahirar su ba, KU ja bakin KU kuyi shiru.
A yanzu dai kowa ya Gama Gane dik wata Mai rubuta batsa da koyar da kwanciya aure a novel tana daga dangin su akuya da kaji, saboda mage da Kare ma sun boye sex life din su balle Dan Adam Mai daraja.
Na yi wannan nasihar ne ga kowa ga kowa, har Ni Kai na, Ina roqon dik wadda ta karanta indai tana da groups din da ake tura novels ta tura, a banza ma tura na batsa ake balle nasihar da in wani ya gyara Muna da Lada dika inshaa Allahu.
Allah ya yafe Mana kurakuren mu, Allah ya San mu aikata daidai, a rayuwar mu.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......