Cikin tashin hankali ya bude qofar ya fita, mutane sun kewaye wajen wasu na dauka a waya, wasu na salallami saboda ganin jini na zuba a gefen kan ta, masifa ya fara yi wa masu dauka a waya, ciki har da wasu mata sun ci gayu da wata dattijuwa ta sha hijabi da Niqabi amma wayar ta na hannun ta tana daukan video .
"Dalla ku matsa ku ba mutane waje marasa kishin kai kawai, wannan har abun dauka ne? Kuna mata kun ga musiba ta samu mace amma kun tsaya dauka , a wayar taku akwai likita ne da In kun tura masa zai duba ta ta wayar? Aikin banza kawai, ku taya Ni sanya ta a mota dan Allah Ni"
Da sauri suka soke wayoyin nasu jiki ba kwari,kunya duk ta kama su, suka hau tattara matar dan sanya ta a motar, bayan sun saka ta ne Alhaji Yaseer ya nufi kwaryar ta, dan daukar mata, sai ya ga ta fashe, dankwali ne kawai da mayafi a ciki, sai takalmi na maza debewa ya yi ya watsa gefen mai zaman banza ya ja motar sai asibiti.
Ko da ya isa ya kira nurses Suka shiga da ita, shi kuma ya juya yana waya da Hajiya Safiya yana mata bayanin abinda ya faru.
Da kyar aka samu jinin ya tsaya suka mata ɗinki a wajen da ta ji ciwo, sai kurjewa da ta yi a hannaye da qafa da kuma kafadar ta.
A daki guda aka aje ta saboda Alhaji ya fi son a aje ta waje daban.
Yana fita da 'yan mintoci ta farka, ta duba ko Ina bata gan shi ba, tini ta fita daga it sai dogon wandon ta da riga Mai hannun vest kan ta ba dankwali,ta dauki wayar ta, dakin little ta shige,
"Ina Daddyn ka?",
"Ya fice"
"Ok"
Kallon shi ta yi taga Yana babbata rai murmushi ta yi, ta aje wayar ta a saman gadon shi,sannan ta wuce bayin shi, ta wanko bakin ta tana fitowa ta zame dogon wandon ta, ya rage daga it sai kampan ta da rigar ta, zaunawa ta yi a jikin shi, ba bata lokaci Suka fara wasanni da junan su.
Wayar ta ce ta fara ringing suna tsaka da romancing junan su, sun yi wurgi da kayan jikin su, cike da kasala ta daga wayar.
Sallama ta mishi tare da tambayar shi Ina ya je,a tunanin shi bacci ya tada ta, Dan haka ya Bata hakuri, sannan ya mata bayanin me ya faru.
Hajiya Safiyyah Sarkin kishi tana jin mace Alhaji ya buge ta ce masa zata zo ta kula da ita ba sai ya je wajen ta ba, gata nan zuwa.
Little da ya daga kan shi yana kallon wayar da take ne ya ce.
"Mum me ya faru? Wajen wa zaki a asibiti?"
Labarta mishi komai ta yi cikin sauri ta fara zira dogon wandon da ta cire ta Yar a qasa, riga take qoqarin sanya wa ya riqe hannayen ta, tare da manna kan shi a qirjin ta,.
"Plss Mummy Kar ki je ko ina, I need u, besides ai Dad na can me zaki a wajen bayan ba ke kika buge ta ba, kuma wannan dama ce muka samu tunda baya nan,"
Tura shi baya ta ɗan yi , ta qarasa sanya rigarta, sannan tace,
"Little ka fahimci wani abu daya, ina son miji na, ba zan bar kowa ya shiga tsakanin mu ba, 'yar fulani fa yace ya Kade, so ka ke ina nan ta farka suyi ido hudu su kamu da son juna su fallashe ni? In babba ce wataqila a dangin ta wata ta maqalewa mijina , kai Ni ban yarda da kowa ba indai mace ce ta zauna daga Ita sai miji na"
Tsananin mamaki kawai little ke yi, bai gama mamakin ba yaji qarar rufe qofa har ta fice.
Hijabi kawai ta ɗora a kan riga da wandon har qasa yana sharar hanya,irin mai hannun nan, riqe take da jaka da wayar ta,ta shige mota ta tada, Bata tsaya ko Ina ba Sai asibitin.
Bayan ta Isa ta yi parking ta Masa waya Nan ya mata kwatancen inda zata same shi.
Yana tsaye ya harde hannayen shi a baya, ta qarasa cikin ran ta take magana,
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......