ALMAJIRI NA....PAGE 5

2.6K 150 7
                                    

Bayan Ameerah ta kashe wayar ta cikin fushi ta dinga tura ma Alhaji hotunan su da sukayi tsirara, da videon da suka dinga yi, sai hotunan shi da ya tura mata tsirara.

'Alhaji sai na b'ata maka rayuwar ka, in junan ka b'ata yaran mutane da sunan zaka aure su, yau ka kawo qarshen iskanci, sai.na b'ata maka suna a idon duniya, na baka daga yau zuwa gobe, ka aiko gidan mu, in ba haka ba, zan yad'a wannan videon a kowacce kafar sadarwa da nake, kai harda wadda bana yi zan bud'e a yau yau d'innan saboda kai'

Ta na gama rubuta wa ta tura,

Alhaji zufa ne kawai ke karyo masa, hankalin shi ya tashi, idanun shi sun yi jawur, cikin tsananin takaici Hajiya Safiyyah ta kalle shi, tsaki mai tsaho ta ja sanan ta zauna a bakin gado,

"Sai ka fadan adireshin gidan su,"

"Me zaki mata?"

Cikin tsananin fushi ta miqe,

"Cinye ta zan, nace cinye ta zan, nace ka ban adireshin ta har kana da bakin tambaya ta me zan mata? Dalla in zaka ban ka ban, in ba zaka ban ba ka bari ta aikata maka abinda ta so,"

Cikin b'arin jiki ya zauna kusa da ita ya fara bata hakuri, sannan ya zayyana mata kwatancen gidan su,

Danna kiran wayar Ameeran tayi tare da miqewa tsaye tana yawo a dakin cike da damuwa.

Tana dauka ta fashe da dariya, Hajiyan ma dariyar ta sake mata, tin Ameerah na dariya har ta fara jin tsoro ta daka ta,

"Me ya sa kk dariya kamar wata tab'ab'b'iya?"

"Yaro man kaza ne, yanzu ke dan baki da wayo kuma sokuwa ce, kawai sai ki yad'a videon ku ma duniya ku ga 'yan iska? To kar ki manta shi namiji ne, kuma iskanci ba wai sabon abu bane a wajen shi, ya dad'e yana aikatawa, tin baki da wayo, dan kin nuna ma media kinyi aikin banza, za a zage shi ne na wani lokaci saboda muqamin shi da girman shi, ko shekara ba za ai ba wanda ya fishi iskanci zai bayyana sai a aje nashi, amma kin san me? Matar da yayi iskancin da ita wato ke kenan, har abada ba za a manta da ita ba, sanan ba namijin kirkin da zai je mata sai dan iska, tinda sun ga yanda kk iya iskanci,"

Fashewa da dariya sosai Hajiya tayi da ta kai daidai nan, sannan ta bayyana wa ameeran adireshin gidan su.

"Ba nan ne gidan ku ba? Ina kyautata zaton tsoho da tsohuwa ba su san 'yar su na bin maza ba,kin san dai ba ke kadai ke da videon ku ba ko? Muma.muna da shi,mu ba zamu yad'a a media ba inda ba kowa ya san ki ba, gidan ku zan zo na.nuna ma iyayen ki, sannan na sa hukuma su kaman ke da laifin kina bin mijina,sanan na turawa samarin unguwar ku videon, yarinya baki san ni ba ne, ki tambayi tarihi na, akan mijina zan iya komai, inna ce ma ki komai ina nufin komai, har da daukan ran wadda dik ta shiga tsakani na da miji na, ki riqe wannan"

Ameerah jikin ta har rawa yake dan tsananin tsoro,

"Hello? Hello? Kina jina kuwa? Hahhhhha, yaro bai san wuta ba sai ya taka, ashe ke qaramar yar iska ce, ina mai baki umarnin yanzu ki shiga gallaryn wayar ki ki goge komai tasss ki min screenshot ki nuna min, baruwana da wasu hotunan ki masu amfani komai zaki goge, ni na baki daga yau zuwa gobe in banga shaida ba, zaki ga videon ki a wajen d'an garuwan unguwar ku da wayar gyatumin ki"

Kit Hajiya ta kashe wayar, Ameerah cikin tashin hankali ta shiga dik inda ta boye video da hotunan su ta hau gogewa, sai da tai wa wayar ta tasss, sannan ta yi yanda Hajiya ta umarce ta, tare da roqon ta akan ta rufa mata asiri kar ta nuna ma iyayen ta,"

Kuka sosai Ameerah take tana kiran no Alhaji amma Hajiya taqi dagawa, Alhaji ya qame qam saboda mamakin matar shi da kuma shakku da tsoron ta da ya darsu a ran shi.

Banza tayi da shi ta koma d'akin ta da wayar shi a hannun ta, duba hoton tayi taga yanda yarinyar ta goge komai kuma ga ban hakuri da kuka da ta turo mata, daga baya ta bude audion da ta yo mata na ban hakuri, kuka sosai take tana bata hakuri, tana roqon ta da ta dau wayar dan ta bata hakuri,Hajiya dariya tayi mai dauke da takaici, sannan ta duba wayar mijin nata kuka ta fashe da shi sosai ganin hotunan batsa na mata kala kala, turawa da baqar fata a wayar mijin ta, me ye bata mishi? Jiki ne da ita mai kyaun gaske, wanda mata da dama basu da irin shi, tsahon gashi ne har baya kawai bata da shi, ga videon shi da Ameerah nan da yawa wasu sina kiss, wani yana romance da ita, guda daya ne wanda suke sex sosai, kuka Hajiya take kamar an mata mutuwa, she is young and beautiful she is very obedient to him, dika dika shekarar ta 29, namiji wato dik abinda mace take masa in dan iska ne sai yayi iskanci, (Addu'a kawai ke taro su).

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now