Ko kudin motan zuwa gidan Bata da shi, haka ta samu ta hau adaidaita sahu har gidan, Idi ne ya fita ya leqa ya gan ta tsaye da alama tana Jin jiki, saurin bude Mata gate ya yi,
"Malama ya za ki shige ba ki bani kudi na ba?"
Kallon Idi ta yi, murya a wahale,
"Idi ba shi kudin shi, dari da hamsin za ka bashi,"
Da sauri Idi ya lalubu kudin ya miqa mishi, ya ja abun hawan shi ya tafi Yana surutai, Hajiya na Isa bakin qofa ta murda ta ji a bude, shiga ta yi , ta zube a kujera tana maida numfashin wahala, Alhaji da ke daki ya ji alar an shiga ne ya fito, sanye da jallabiyya, da carbi a hannun shi, ganin Hajiya zaune a saman kujera ne ya Sanya shi mamaki.
"Ke ya akai Kika dawo min gida? Ba ki ga takardar da na aje Maki a kan pillow ba?"
"Wacce takarda Kuma? Wataqila masu gyara dakin sun gani sun share, Amma ban ga wata takarda ba......Alhaji na fito daga asibiti ne ba da izinin likita ba, Dan da na nemi sallama Hana Ni sukai, Wai ban Gama warkewa ba, shi ne na gudo ba su sani ba, Dan Allah ka yafe min abinda na aikata, ka sani tun da yarinta ta ba a matsayin mazinaciya ka auren ba, na sani ina kula maza a da Dan mu samu abinda zamu ci, Amma ban taba kwantawa da kowa ba, Kai shaida ne,Kai da zan aura ma ban sake maka jiki na ba balle wasu mazan, Amma Kai Mata nawa ka yi wa ciki da aure na akan ka, Ni ke maganin matsalolin ka na neman Mata a Baya, ban taba rabuwa da Kai ba, kar ka rabu da Ni, bani da kowa ka sani in ba Kai ba"
Kuka take sosai tana magana, tausayin ta ne sosai a cikin zuciyar Alhaji, Amma haka ya dauke kan shi,
"Kin San me Kika aikata kuwa? Zina da Dan ciki na, har ya Miki ciki Safiyya ko na yafe Miki da wanne ido zan ci gaba da kallon ki a matsayin Mata ta?"
"Da irin idon da zuciyar da na ci gaba da kallon ka, a lokacin da ka yi wa Ameerah ciki, ka Kama hotel ku ke cin Amana ta, ba Ameerah ba kadai Kai kan ka ka sani ka yi wa Mata kala kala ciki wasu Ni nake bada kudi a zubar, Amma haka na hakura"
Wata uwar tsawa ya daka Mata sai da ta zamo a kujerar.
"Kar ki qara hada kan ki da ni, in ma baki ga takardar da na rubuta ba Bari na fada Maki abinda na rubuta, Ni Alhaji Yaseer Dalhat Waya, na Saki Hajiya Safiyyah Saki biyu,kinji me ye a cikin takardar yanzu? Ina magana kina magana kina tunamin rayuwar da na yi a Baya,? Ashe ba neman gafara kike ba so kike ki nuna min Nima na yi ramawa ki Kai? To in ke Zaki iya hakuri da Ni a matsayin na na mazinaci a da, Ni ba zan iya hakura da mazinaciya ba, ina fatan kin gane?"
Hawaye ne kawai ke zarya a fuskar ta, idanun ta kamar zasu Fado qasa, ita ake saki haka, a wulaqance, dik irin so da halaccin da ta nuna ma Alhaji, (halacci ko ba halacci ba, Yar rainin wayo, da kin barshi ya qara auren da ya ke so, ai da wataqila bai ci gaba da Zina da auren ba).
"Ni ka ke saki haka Yaseer? Ni ce fa Safiyyahn ka, Ni Yaseer ka ke wa irin wannan sakin wulaqancin?"
"An yi Miki, gida na qarami da ke unguwar KU ta da ki je na baki shi, ki koma ciki, Amma kin Gama zama a Nan"
"Qarya ka ke, baka yi tuna Ni ba, baka Isa ba, ka yi kadan, ka fidda Ni a wannan gidan, sai dai Kai ka koma wani, ai ba gida Daya ko biyu ko Uku gare ka ba, Yaseer ka yi kadan ka rabu da Ni, in ka rabu da Ni Ni ba zan rabu da Kai ba,"
A hasale ya Isa wajen ta zai bige ta, ta miqe ta manna jikin ta da nashi, tana nuna Masa in ya Isa ya dake ta, daga hannu ya yi zai dake ta ya kasa, saboda kallon juna da suke, ido cikin ido, jikin shi ne ya Yi sanyi, dik duniya ita ce macen da yake so sama da kowa, yau gashi ta zame Masa kamar baqin kumurci,a da ya so Nusrah kamar in ya rasa ta ba zai rayu ba, amma a yanzu Safiyyah ya fi so sama da kowa, sai dai ba zai iya zama da ita ba, Yana hango cin amanar da ta mishi.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......