Taku ya yi zuwa bakin qofar fita, sannan ya tsaya, Alhaji Yaseer ya baza kunnuwa dan jin me little din zai fada,
"In har kana so in yafe maka sai ka min alqawarin daga yau, zuwa har abada, ba mu ba kai, inna ce ba mu, ina nufin daga ni har mahaifiya ta, da dukkan abinda ya shafi rayuwar mu, sannan wannan shekarar bana buqatar sisin ka a account di na ko da za mu hadu a hanya, kar ka sake ka nuna ka sanmu, In ka amince za ka bi sharruddan nan, na yi alqawarin yafe maka, da zuciya mai kyau,har abada ba riqo a tsakanin mu"
Wata irin zufa ke karyo ma Alhaji Yaseer, gwanda little ya kashe shi da ya raba shi da rayuwar su baki daya, In ba su ba shi, cikin tsananin tashin hankali da damuwa Alhaji ya zube a bayan little Yana roqon shi, kuka ya ke sosai kamar wanda akai ma duka.
"Yaseer ka taimaki rayuwa ta, bani da kowa sai ku, kar ka raba Ni da ku, ku ne farin ciki na, ina son ka a matsayin dan da na haifa, tun kafin na san ko kai waye, na saba da kai, da son da nake maka, ba zan iya daina son Nusrah ba,a shirye na ke da na aure ta, dan na gyara kuren da na yi a baya"
Cikin fushi little ya juya, ya fara magana cikin daga murya, wanda ya ja hankalin Hajiya Safiyyah ta fito.
"Meye wai baka gane ba? Ba mu buqatar ka a rayuwar mu, Bama son mu sake hada ko da hanya ce da kai, har abada, da kana so na a matsayin d'a, da baka aikata abinda ka yi ba a shekarun baya, da ka yi hakuri ka je ka nemo kudi ka aure ta, kun samar da Ni ta hanyar da ta dace, a yanzu ba ka da 'yancin da zaka kira Ni dan ka, ko ka ce zaka so mahaifiya ta, ka je ka ji da matar ka"
"Little baka isa ka hana ni son Nusrah ba, sannan baka isa ka hana Nusrah so na ba, ko aure na, ka sani, zan janye neman ta ne kawai a duk lokacin da ta yi aure, amma a yanzu ba zan iya kasa gwada sa'a ta ba"
"Lallai kuwa zaka gane kai ba mai sa'a ba ne a rayuwar ka"
Yana fadin haka ya bude qofa ya fice daga gidan, Alhaji sai kwala masa kira ya ke amma ko juyawa bai ba, balle ya amsa.
Idi ne ya taso ya fara magana da Little, sama sama ya amsa mishi ya fice, abinda ya daure wa Idi kai kenan, ba su taba haka ba.
Hajiya kuwa tun tana kuka a tsaye sai da ta samu waje ta zauna, jiri ta ke ji na dibar ta, ashe akwai gurbin da wata macen zata samu a zuciyar mijin ta, duk qoqarin da take na kyautata masa? A zaton ta ita ɗaya ce macen da ya ke so, kuma zai ci gaba da so, har abada, ashe ba haka bane.
Daukan key din motar shi ya yi, ya fice daga gidan.
*************************
Kasa zama a office Naseer ya Yi, Dan haka ya sake ficewa, bai san me zai ce mata ba in ya je, amma ji ya ke in bai gan ta ba yau, ba zai iya qarasa rayuwa a duniya ba, jikin shi har bari ya ke, haka ya bude motar shi ya shige, da qarfin gaske ya ja ta, sai qauyen su Nusrah.
Tsifa Yadikko ta gama mata, tana Mata oiling da man kwakwa, da ta haɗa da man shanu danye,man ridi, da man habbatussauda da na olive,sai man Kade, gashin nan sai walqiya ya ke, gwanin sha'awa, idon ta lumshe tana jin dadin yanda ta ke mirza mata kan ta,iska mai dadi na busawa, labari Yadikko ta ke bata, amma bata gane komai, tunanin Alhaji Yaseer ta ke a zuciyar ta, duk irin abinda ya mata, ta kasa dai na tunanin shi, ta kasa dai na son shi, da ta na da halin tsince son shi, da ta tsince ko daya ba zata bari ba, iska ta shaqa tare da gyara kwanciyar ta a cinyar Yadikkon ,sallama suka ji, ta baquwar murya, Yadikko ce ta amsa Nusrah kuwa bude idon ta tayi dan ganin mai sallamar, wata dattijuwar mata ce ta shiga, tare da sake yin sallama, amsawa suka yi, Nusrah ta miqe zaune, ta daure kan ta, duk gashin ya barbazu bai shige ba duka, dan haka ta janyo hijabin ta, a daki ta saka.
"Sannu da zuwa, baiwar Allah, Bismillah mu shiga daga ciki"
Kallon Nusrah kawai ta ke, tana karantar ta,
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......