Kayan little na wanki ta kwaso, a cikin basket za ta kai waje dan mai wanki da guga na waje yana jiran ta bashi kayan ya je ya wanke a injin wanke kaya, wanda akai ma waje na musamman a bayan gidan.
Little na zaune ba riga daga shi sai dogon wandon jeans Mai kyau da tsadar gaske, wanda ta siyo mishi da kan ta sanda suka je shopping, remote ne a hannun shi yana kallon tashar Bollywood , Ana wani India movie Mai kyaun gasken, soyayya kawai ake zubawa, abun na qayatar da shi,bayan ta dawo dakin ta ta nufa ta cire dogon hijabi da rigar da ta zumbula ta sanyo wasu qananan kaya masu matuqar kyau da ɗaukan hankalin mai kallo.
Cikin yanga da yauqi ta zube a gefen shi, tare da rab'a rabin jikin ta a nashi, shafa qirjin shi ta yi tare da hura iskar bakin ta a saman qirjin shi, lumshe idanun shi ya yi ya ja numfashi, sannan ya dora hannun shi a saman nata, ya saqale yatsun su waje daya.
Sun shagala sosai da kallon da suke tare da shafe shafen junan su, su kaji ana buga qofa, wani irin faduwar gaba ne ya kama su duka, a kidime suka miqe, cikin shaqaqqiyar murya Hajiya ta furta,
"Waye?"
"Hajiya ni ne tare da baqo"
"Baqo kuma Idi?"
"Eh Hajiya"
little dakin shi ya shige ya na mai jin haushin baqon da akai, ya so ya gwada irin soyayyar da ya gani dazu, amma ba komai, zai gwada da dare ne.
Kwantawa ya yi, ya fara latsa wayar shi, bayan lokaci mai tsawo basu yi waya da abokin shi ba, dan haka danna wayar shi ya yi dan lalubo abokin na shi su gaisa.
Ita kuwa daki ta shiga da saurin gaske, ta sauya kaya, sannan ta bude qofar, baki ta bude sanda suka yi ido hudu da junan su, shi kuwa murmushi ya sakar mata.
Ya na tsaka da magana ya ji maganar Hajiya
"Alhaji? Yaushe ka dawo?"
Murmushi Alhaji ya yi wanda ya bayyana haqoran shi,
"Surpriseeee"
Da sauri ta rungume shi tana murna, shi din ma rungumar ta ya yi sosai saboda ba qaramin kewar ta ya yi ba.
Suna tsaye a haka Idi ya rab'a su ya shiga da kaya, yana ta fara'a , uban gidan shi ya dawo, Little ne ya fito sanye da jallabiyya da hula, hannun shi riqe da wayar shi, kallon Hajiya ya yi ya gan ta sanye da doguwar riga da hula, gefen ta Alhaji, ya kad'u sosai amma bai nuna halin da ya ke ciki ba,murmushi ya saki kamar ba abinda ke boye a ran shi, qarasa wa ya yi, tare da durqusawa har qasa ya ce.
"Barka da dawowa Daddy, lallai ka bamu surprise, ina fata ka dawo lafiya?"
"Lafiya qalou Little, Little ka girma ka zama babban mutum"
Murmushi ya yi ya sosa qeya.
'Iya girman jiki ka gani, Ni zan baka labarin girman da little ya yi' Hajiya ta ayyana a ran ta.
"Hajiya tunanin me ki ke?"
"Ni ? Wanne irin tunani kuma kana gaba na? Muje ciki, ka yi wanka kan ka fito na hada maka abinci, ban yi tsammanin ka ba da na hada maka abinci"
Alhaji na gaba Hajiya na baya, little kuwa da ke kallon yanda hannun ta ke maqale a jikin Alhaji ne ya bata rai, ya zauna a kujerar da ya saba zama.
Hajiya na kula da haka ta zame hannun ta daga qugun Alhaji suka shiga dakin.
Bayan ta taimaka mishi ya shiga wanka ta fita, da sauri ya ja hannun ta zuwa kitchen din ya manna ta a jikin fridge, wani irin kallo ya ke bin ta da shi, a ran shi yana mamakin sanda ta saka rigar jikin ta har da hula.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......