Cike da dariya Nusrah ta kalli Hajiya.
"Hajiya na miki alqawarin ba zaki taba kama Ni da cin amanar ki ba akan mijin ki, ko dan ki, Ni da ki ka ganni namiji shine abu na qarshe da nake tunani a rayuwa ta gaba dayan ta, ba wai dan Ni din ina girmama auren jinsi ko kuma soyayya da jinsi ba, Ah ah tsananin qiyayyar da na yi wa namiji kenan"
Wata iriyar ajiyar zuciya mai qarfi Hajiya ta sauke, bayyanar ta ya sa Nusrah kallon ta da mamaki, lallai matar nan ta yadda da maza sosai, irin wannan so da take masu haka?
Qarasa daura dankwalin ta Nusrah ta yi, sannan ta sanya Hijabi, ta dau ki ledar kayan ta, suka fita a tare, kitchen ta je ta debar masu tuwon shinkafa da tayi, miyar danyar kubewa da ya sha kifi irin na garin su OO🤣(ban Kama suna ba balle ace na ce ehe😙) gora biyu na zobon da ta haɗa masu Hajiyan ta debar mata, ta saka a wata leda babba mai kauri, Godiya ta yi sosai, driver ya dauke ta sai tasha.
Tana isa motoci na lodi ta samu ta haye, basu jima sosai ba ta cika, sai gida....
Ko da ta isa gida, kamar kullum gidan fess, Yadikko har ta sa an sai qasa da kudin da Hajiya Safiyya ta basu jiya, an siyo siminti, an aje, sauran su samu na ma'aikata, Wanda Yadikko ta raya a ranta da ana yi wa Nusrah albashin farko za su qarasa gyaran.
Da sallama ta shiga, Yadikko ta bar wajen qasar ta nufe ta, tare da amsar kayan hannun ta, zama suka yi a kan tabarma, nan fa suka hau Hira, Nusrah ta kwashe dik yanda ta gudanar da aikin ta a gidan da abubuwan da suka faru ta sanar da Yadikko, Amma Bata Bata labarin sharadin da Hajiya ta gindaya mata ba.
"Ni naga uwar dakin naki ma, kamar ba wata babba bace sosai ko?"
"Eh ai ko zata girmen bai fi da kadan ba, a qallah ta ban shekara Daya ko biyu, Kuma kin San akwai banbancin cima da wajen zama, Dole ta fini kyaun gani"
"Sam, ban ga haka ba, ai kin fita yarinta, in ba dan Ni da na sani ba wa zai ce kin ma taba haihuwa?"
Shiru suka yi, Nusrah ta shiga duniyar tunani.
'Tabbas jiki na Yana bani na kusan ganin da na, Kuma ina kusa da shi, kamanni na da Yaron Hajiya ta baci, Sai na yi bincike akan shi hankali na zai kwanta, gobe an ce na gyara dakin shi, zan bincike sosai har Sai na gano gaskiya, in Dan su ne na cikin su, tabbas Allah Mai yanda ya so ne Kuma gwani ne wajen halitta, in Dana ne, ban ce zan amshe shi ba, amma tabbas zan kasance da shi a wannan gidan har abada, ba zan laifin da zasu Kore Ni ba,'
"Wai Ni tunanin me kike ne haka? Tashi ki dauki abincin ki Kai ciki, Allah ya sa ban dafa komai ba, da Sai dai a dumama gobe"
"To Yadikko"
Ciki ta shige da abincin, sannan ta fiddo kayan da take ganin zata maida su kamar Uniform in zata aiki tana sawa, omo ta dakko ta sake fita, wanke su ta yi tass ta shanya, sannan suka zauna suka ci gaba da hirar su.
*************************
Washe gari da ta Isa tasha, driver na jiran ta, Dan haka tana zuwa ta fada mota Sai gidan Yaseer Dalhat Waya.
Aikin ba yawa kamar na jiya, Dan haka Bata wani Jima ba ta gama, tana gamawa ta dora girki, sannan ta nufi dakin little domin gyarawa, Hajiya ce ta Kai ta da kan ta, sannan ta sanar da ita irin gyaran da take son a yiwa dakin, Nusrah na ta mamakin irin son da Hajiyar ke yi wa dan.
"Lallai Hajiya kina ji da wannan yaron, Allah ya Raya Miki shi da imani, Amma har na fara tausaya mashi in qani ko qanwar shi ta iso duniya, zamu Sha kallon kishin babban saurayi"
Dariya Nusrah ta yi a daidai lokacin da ta qarasa bakin gadon, ta fara cire zanin gadon.
Hajiya kuwa qamewa ta yi, Dan Bata gane ina Nusrah ta dosa da maganar ta ba.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......