Bayan ta kammala takaba, Lauyan Alhaji ya Kai Mata ziyara, Hajiya Bata taba tunanin zata Sanya hijabi a jikin ta ba, tun da take, amma bayan rasuwar Alhaji ta maida lamuran ta kaff wajen ibada, rasuwar ta taba ta ba kadan ba, dik kayan ta damammu ta kwashe su, ta bawa Habi ta Kai ma yaran ta, dan su Yi ma mazan su kwalliya da su, sun Yi murna sosai, da sosai, Dan Kaya ne masu matuqar yawa da kyau, sabbin hijabai ta siya, take sanyawa, daidai da su Idi yanzu Basu ganin ta ba tare da Hijabin ta ba, ko babban mayafi.
Zaune suke, ta Sa Habi ta kawo Masa juice da abinci, juice din kawai ya Sha, sannan ya fara Mata bayani, Kamar yanda Alhajin ya ce.
"Alhaji ya jima da barin wasiyya, tin sanda ya gano cewar Yaseer qarami Dan shi ne da ya haifa ba ta hanyar aure ba, na mishi bayani matuqa Kamar yanda Musulunci ya ce, ba shi da gadon mahaifan shi, Amma zai iya diban wani sashe na dukiyar shi ya mishi kyauta da ita, amma ba kyautar da zai bar iyalan shi cikin wahala ba, wannan dalilin ne ya sa Alhaji ya yanke hukuncin cewa dik gidajen shi guda hudu da ke cikin garin nan na Adamawa ya bashi kyautar su, sannan gidan shi daya da ke Spain ya mallaka mishi, ga takardu da dik wata shaida da ake buqata, Alhaji ba shi da kowa, hakan ne ya Baki damar mallakar komai na dukiyar shi, Kama daga kamfanin shi na waya, da gidan shi da ke a China,da wannan gidan da kike ciki, da motocin shi, sai gonakin shi da ke a Gembu guda biyu, ki dauki Daya, Daya Kuma ya mallaka ta ga gidan marayu, kudaden shi da ke account kuwa ya mallakamin million biyu, sannan ya ce na Baki million biyu, million shida a Gina masallaci babba, Mai kyau, million Daya akai gidan marayu, wanna shi ne kasafin da Alhaji ya yi da jimawa, dik da Bai San wa'adin shi ya kusan cika ba, Allah ya gafarta mishi, ya mishi rahama, yanzu sai ki Kira yaron Alhaji, na maimaita wannan bayanin da na maki gaban shi, sannan na damqa mishi dik abinda ya ke na shi ne"
Hajiya idanun ta sun yi jawur, saboda kukan da ta ke ta Yi, da dikkan alamu Lauyan Nan shi daya ya yi kidan shi ya yi rawar shi, ba ta Gane komai, mutuwar Alhaji ita ce a gaban ta, ba abinda ya bari ba, dik duniya ba Wanda ta ke so sama da shi, ko da da take mu'amala da little son Alhaji Bai taba barin ranta ba.
Sake magana ya Yi, da ya kula Kamar shi Daya ya ke maganar shi, daga Kai ta yi da jajayen idanun ta, ta kalle shi,
"Ka yi hakuri ka ce Alhaji ya bar maka wasiyya ko?"
'Tabdi jam, matar Nan dik uban bayanin da nake Bata Gane komai?'
"Cewa na Yi Sai kin Kira Dan Alhaji sannan zan sanar da ke dik abinda ya bari a wasiyyar shi, cikin share majinar hancin ta da gefen Hijabin ta, ta kwalawa Habi Kira, Habi na zuwa ta zauna nesa da su, tana jiran Umarnin Hajiyan,"
"Habi dakkon wayata a daki na"
"To Hajiya"
Bayan ta kawo Mata wayar ne, Hajiya ta Danna lambobin little, Kamar ba zai dauka ba, sai ya tuna cewar Alhaji fa ya rasu, shi kadai ta riqa a dangi, Dan haka ya dauka, tare da komawa gefe,
"Assalamualaikum "
"Waalaikumussalam, little, Dan Allah in ka samu dama Ina son ka zo gida yanzu, lauya ya zo Yana son magana da mu dika"
Shiru ya yi, saboda da ya so yi Mata musu, Amma ya fasa, musamman da ya ji, ba wani gaishe gaishe ta yi bayanin abinda ya Sa ta Kira shi direct.
"Ok, bari na fito daga lectures zuwa Yamma, zan shigo, ki ba shi hakuri, da Yamma ya dawo"
"Ok, Allah ya kaimu"
Difff ta kashe wayar ta, little ya ji daɗin yanda Hajiyan ta sauya sosai,a qalla mutuwar Alhaji zata zama izina a gare ta, dama mutuwa na daga cikin ayoyin da Allah ya Sanya Mana Dan mu ji tsoron shi mu bauta mishi da gaskiya, sannan in Muna aikata ba daidai ba mu hankalta mu koma ga Allah.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......