ALMAJIRI NA...PAGE 46

1.6K 136 14
                                    

A gidan su Maryama kuwa, ana ta hidimar kai ta gidan miji, Maryama ta tashi da zazzaɓi a sakamakon kukan da ta kwana yi, an kada ta dambu taliya ta qi dai na kuka, Sumaye da Lamido tun suna lallashin ta yanzu sun zuba mata idanu, dangi ko ta ina zuwa suke yi masu murna, wasu kuwa qiriqiri suke nuna tsoron su akan lamarin auren na ta, a cewar su Yaseer ba mutumin da za a yarda da shi ba ne, musamman yanda suka ga ana barin kudi, kuma ga shi an ce ba za a yi wa yarinya kayan daki ba, abun ya na basu tsoro.

Wasu kuwa dariya suke, suna gulmammakin da ta je ya gama da ita zai sallamo ta, shi ya sa ya hana yi mata kayan daki, kar ya ba su wahala, (mutane ke nan, akwai wanda duk yanda kai baka damu da rayuwar shi ba, to shi ya damu da taka, akwai wanda a duniya jiran ka kawai ya ke ka gaza ya topa gubar bakin shi akan ka, akwai mutane masu fuska biyu, su taya ka murnar ci gaban ka a gaban ka, a bayan ka su zage ka, su kwashe wa abinda ka samu albarka, baqin cikin da suke maka su ji kamar zai kashe su, Allah ka haɗa mu da masoyan mu domin ka, ka nesanta mu da masoyan mu domin duniya da abinda ke cikin ta, maqiyan mu kuwa ka nesanta mu da su fiye da nisan sama da qasa)

Goggonayen ta da innonin ta ne suke ta gyara ta, da ta ga Sumaye ta gilma sai ta bare baki da kuka, abokan wasan ta kuwa suka samu na tsokana.

Qunshi baqi da ja aka tsara mata, daga Adamawa Amma ta aika da mai mata qunshi, kitso da kwalliya, kitso ne aka fara tun goshin azahar sai kusan la'asar aka gama, qanana sosai aka mata, kowa ya kalli Maryama sai ya yaba, Sumaye kuwa mamakin ganin yanda aka sauya mata diyar  ta ta ke, ba a barta a baya ba wajen yabawa, har wasu na ganin ta yi rashin kunya, a matsayin ta na diyar fari, bata bi ta kan su ba, ta yi ta yabawa, tare da yi mata addu'ar kariya daga sharrin mutane da mugun baki.

Wanka mai kyau Goggon ta ta sanya ta yi, ta daure mata gashin ta da band ash colour, bayan ta fito ne mai kwalliya ta zauna baje basirar ta a kan ta, ta sha powder ta Yi kyau qanwar Sumaye mai suna Inna Bod'ijo ta kawo wa Maryama abinci, tun safe kowa ya yi iya qoqarin shi ta ci abinci ta qi, dik da sun samu ta rage kukan, amma abinci ta qi shi,

"Dan dakata da kwalliyar ta ci abinci sai ku qarasa"

"Ni na qoshi"

Hannu Inna Bod'ijo ta Daga za ta make ta, ta duqunqune jikin ta, tare da sake shiriritar qara,

"In kowa na wasa da ke, Ni dai kin san ba wasa na ke da ke ba ko? Amshi kafin na daka ki, ba ruwa na da wai yau zaki gidan miji, muma ai baki raga mana ba,nima ba raga maki zan yi ba, amshi"

Tana hawaye tana komai ta karbi kwanon Inna Bod'ijo kuwa ta tokare a bakin qofa tana jiran kwano, Maryama na budewa ta yi arba da Farfesun kaza, wata yunwa ce ta murdo ta, yawun ta ya tsinke, daga kai ta yi tana murmushi ta kalli innar ta, ta washe baki

"Yannema bani abinci na na wuce da shi, tunda kin qoshi "

Juya baya ta yi, ta danna hannu cikin kwanon ta fara yagar kazar, dariya mutanen wajen suka dinga mata,ganin tana ci ya sa Innar ta barin wajen, tana dariya itama.

Bayan ta gama ci,ta sha madarar shanu, mai dumi,wadda aka dafa da kayan qamshi,ta wanke bakin ta tas, aka ci gaba da tsara mata kwalliya.

Ta yi sallar la'asar, ta na zaune tana kallon kan ta a madubi,tana ganin irin kyaun da ta yi, shadda ce ash colour ta dace  da irin kwalliyar da aka mata,  yara ne suka shigo da ihu suna murna, motocin daukan amarya sun iso,  tashi ta yi a guje ta haye saman gadon sumaye ta qudundune tana kuka.

Yadikko na tare da Hajiya Yelwa, little ya so biyo su amma suka hana shi, ya fake da ba su san waje ba, Yadikko ta ce zata gane, al'adu irin na Fulani asali suka gabatar, sannan aka fidda masu da amarya, sai turjewa ta ke tana kuka, Lamido ma yau sai da ya fidda kwalla, jin Maryama ya ke a matsayi guda biyu, diya kuma jika, saboda sun jima ba su haihu ba, sai da girma ya kama su, sannan suka samu Maryama , sun shaqu da ita ba kadan ba, bai san hawaye na zuba ba, sai da qanwar shi ta mishi magana, da sauri ya goge hawayen shi, yana murmushin dole, Sumaye kuwa ba ta ma fito ba, saboda bata son a yi abun kunya.

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now