ALMAJIRI NA....PAGE 34

1.8K 147 26
                                    


Nusrah cikin Bata fuska ta shige Alhajin, ta nufi dakin Hajiya Safiyyah, ta yi sallama.

"Shigo Nusrah, ki yi hakuri, muna ta Sanya ki wahala"

"Kar ki damu, domin Allah na ke yi, daga ranar da aka ga little ba zan sake kwana Daya inaa aiki a gidannan ba, alaqar mu ta yanke,ina sake maki godiya akan kula min da shi da ki ka yi a lokacin da ni n guje shi, wanne kayan za a hada?"

Tana magana ne fuskar ta ba yabo ba fallasa, Hajiya shiru ta yi, Jin ta take a muzance, a qasqance, nuna ma Nusrah kayan ta yi, ta taka, ta sakko da akwati, ta jera komai yanda ya Dace, sannan ta fitar da akwatin, Dr Muhammad na Nan zaune Yana karantar abokin shi, tunda ya zauna ya kasa tabuka komai, ya shiga cikin tsananin damuwa, ganin Nusrah ta fito, dauke da akwati ne ya Sanya shi saurin miqewa, ya je Dan ya amsa, sake akwatin ta yi ta juya ciki.

"Wooow she is hot"

"Muhammad ka kula da kalaman ka,"

"Yi hakuri aboki na, na ga yanda take Abu ne Kamar da bitterness "

"Ba hurumin ka bane,"

"Ok, ina patient di na? Ka je ka zo da ita, mu je na gama sa ta akan abubuwan da su ka kamata kafin ayi aikin gobe"

"Wanna shi ne hurumin ka"

Murmushi Muhammad ya yi, sannan ya miqe ya fita waje, a mota ya zauna, ya jingina kan shi da seat din motar, Yana tunano fuskar Nusrah,

"Masha Allah, DIK inda aka Kira Mai kyau za ta amsa, Amma akwai wani Abu a tattare da ita, Dan da ganin halin da take nunawa ba halin ta bane,"

Yana cikin magana shi Daya, ya hango su, suna fitowa,ta ruqo Hajiya, shi Kuma Alhaji Yaseer ya tsaya rufe gidan, a motar Alhaji ta saka Hajiyan, ita Kuma ta tsaya, Alhaji Yaseer ne ya tsaya Yana jiran ta shiga,

"Ni gida zan wuce saboda Kar dare ya Yi na rasa abun Hawa"

Muhammad ne ya fito daga motar shi ya jingina

"In kin rasa abun Hawa Ni zan maida ki gida"

"Muhammad stay within ur limit pls"

"Daga taimako?"

"Ke Kuma shige mu tafi"

"Naka a wanne da zaka ban umarni? Motar shi zan shiga, in Kuma ba zan shiga tashi ba sai dai na tafi gida"

Muhammad ne ya bude Mata motar shi cikin murmushin na yi nasara.

Alhaji Yaseer Kamar zuciyar shi zata Fado qasa, a komai Banda dukiya Muhammad ya fi shi, Muhammad mutumin kirki ne, irin su Nusrah ke so, akwai ilimin addini, zamani, da wayewa, ga uwa uba kyau, da iya zance, Wanda ya hada wadannan ya mallaki komai, in kudin ne ba a barshi a baya ba, Amma ya fi kowa sanin Nusrah dukiya Bata gaban ta.

Shigewa ta yi ta zauna, sai da suka fara tafiya taji tsoron shiga motar wani, Wanda Bata sani ba, kula da yanda take a takure ne ya San ya kunna karatun motar, cikin suratul Noor, qira'ar  Sa'ad Algamidi, wani irin dadin karatun ta ke ji, Bata taba Jin qira'a haka ba, lumshe idanun ta tayi, gashin idon ta Kamar an jera su, suka kwanta, lips din ta masu Dan Fadi, na motsawa saboda bin karatun da take.

"Masha Allah"

Shi ne abinda Muhammad Naseer ya fada,

'lallai wannan baiwar Allah ta hadu, ya Allah ka sa ita na ke jira ya sa na Kai wannan lokacin ban aure ba'

Jin tsayawar motar ne ya sa ta bude ido, ganin su ta yi a wani asibitin kudi Mai kyau, an rubuta

"Muhammad Naseer Special hospital"

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now