Nusrah ta Sha jinya sosai, saboda kewar mutanen biyu, Yaseer da Little,dik ta rame ta yi duhu.
Kun san dai yanda magana take a cikin mutane, sai ka yi a bu a daka ka binne, amma sai ka rasa wa ne ya tono ta ya fidda tsakiyar kasuwa, haka ce ta faru da labarin haihuwar Nusrah, wasu ma a fadan su 'yan biyu ta haifa, suna nan an boye su a cikin gidan, shine dalilin da ya sanya ba ta fita mutane, maganganu kala da kala na ta yaɗuwa a kan Nusrah, kuma duk ba masu dadi ba, fita waje ya garere ta, waqa kuwa akan cikin shege ta sha ta har ta godewa Allah, tun tana kuka har abun ya fara sanya ta surutai, ganin haka ne ya sanya Yadikko fara hada masu kayan su, dan komawa garin da suke a yanzu, inda asalin gidan iyayen Yadikko da suka gabata yake.
***********************
Bangaren Yaseer kuwa kasuwancin shi ya bunkasa, ya fara shiga manyan qasashen duniya, Sale ma a wajen shi yake sarin wayoyi yanzu,ya zuba yara uku a shagon da ya bude sabo, suke kula da lamurran shagon in baya nan.
Bai jima da dawowa daga China ba, saboda fara aiki da Company Apple da ya fara, zaune yake a wata kujera ta alfarma a office din shi dake cikin shagon mawadaci, duba ribar da ke shiga masa a shekara ya ke, wayar shi ce ta hau ruri, yana duba sunan ya ja tsaki ya ajiye ya ci gaba.
Bayan kiran da ya zarta biyar message ya shiga wayar shi, da kamar ba zai duba ba, ya miqa hannunsa ya dau wayar, bude wajen saqonni ya yi ya duba sunan da ke jiki.
Bahijja
Shine sunan da ke rubuce, saqo ne kamar haka:
'Dan rashin mutunci ina kiran ka ba zaka dauka ba ko? Ko ka qi ko ka so sai na haife maka abinda ke ciki na, kuma sai ka raine shi, dan kuwa a ranar da na haihu zan kawo maka tsiyar ka'
Murmushin mugunta ya sake, daga baya ya yi dariya tare da jingina a jikin kujerar ya fara juya ta,
"Sai ki kawon abinda kika haifa din in kin San inda nake, haduwar bariki rabuwar bariki, kina Kano ina Adamawa ta ina daki san inda na ke, bayan ko gari na baki sani ba, na so mu dore da hulda saboda ba laifi kin yi, amma inaaa ciki? Ko aure ban yi ba na tara yara? Sam ba zai yu ba"
Hayaniya ya ke ji daga waje, tashi ya yi tare da rufe komai da yake aiki da shi a tsaye, sannan ya fita, tsaye ya gan ta, ta sanya doguwar riga baqa, ta yafe kan ta da baqin mayafi sai qamshi take zubawa, doguwar rigar bata boye share din da take dauke da shi ba.
"Hajiya hakuri zaki yi, wayar nan a hannun ki ta subuce ta fadi ba a hannun mu ba, da a hannun mu ne sai mu biya,"
"Me ke faruwa anan?"Juyawa ta yi, Yaseer sai da ya hadiyi yawu, lumshe ido ta yi ta ware su akan shi, sannan ta bude baki ta fara magana,
"Waya ta ce ta fashe, dan nace su sauyan wata shine suke min ihu, ya miqon na miqa hannu zan amsa ta fadi, yace ni na yadda inni na yar akan mi zan ce ba Ni ce ba, zan masa qarya ne?"
"Ina wayar?"
Miqa mishi ta yi, tana yatsina fuska, hannun ta da ya sha lalle ya bi da kallo,
"Abdullahi, dakko mata wata,"
Cike da murna matashiyar ta kalle shi,murmushi ta sake mai kyau tare da godiya.
"Ba komai, Badamasi na fita, a rufe office,"
"To Alhaji"
Sa kai ya yi ya fita, motar shi ya nufa, ita ma fita ta yi dan komawa gida, tsayawa ta yi a bakin titi dan jiran abun hawa,Yaseer na gama tada mota ya ja ta sai gaban budurwar, kallon ta ya yi cikin yanayi na nuna kulawa yace,
"Baiwar Allah ina kika nufa ne haka? Ga rana kina tsaye?"
"Gida zani, kuma na ga ba abin hawa ma sosai,"
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......