Ya Jima a waje kafin ya samu ya koma gida, fuskar shi ba wani walwala, Maryama ya gani zaune qofar gida ta zabga tagumi, idanun ta sun yi jawur, da dikkan alama ta yi kuka ne, da sauri ya Isa gaban ta, ya durqusa, tana ganin shi ta miqe tsaye tare da buga tsallen murna, tana ta dariya, hawaye na zuba Mata.
"Ina ka tafi Hamma Yaseer, ina ta neman ka, naji Abbaa ya maka maganar komawa gida, ka fita cikin fushi, a zato na ko ka tafi ne ba Kai min sallama ba,"
Kallon ta kawai ya ke, Yana ganin yanda take zuba shagwaba, wani Abu ne yake tsaga qirjin shi Yana shigewa cikin zuciyar shi a game da ita, a baya ya zaci son Hajiya yake, Amma a yanzu n ya tabbatar da me ne ne so, tsakanin shi da hajiya alaqar su Bata da suna, cikin Shan numfashi, ya ja sunan ta, tare da zama a gefen inda ta zauna dazu.
"Maaaryaaamaaa, ke Kam kina da abun dariya, kin taba ganin d'a ya yi fushi da iyayen shi, har ya bar su ba tare da sallama ba? Abbaa uba ne a waje na, ba fushi na yi ba"
"Ka ce d'a baya fushi da iyayen shi, Amma gashi ka yi fushi da asalin iyayen ka, ka gudu, ka barsu, ba ka San halin da mahaifiyar ka ta ke ciki ba, a yanzu, Abbaa na son ka koma wajen su ne Dan ka samu Lada, Allah ya baka Ladan masu hakuri da yafiya, ko Mai suka maka a baya ka yafe masu, Kai ma Allah zai yafe maka abinda ka aikata na zunubi, musamman in ka tuba, ka Kuma bar aikata sabon"
Shiru little ya yi, Yana kallon qaramin bakin ta, tare da sauraron muryar ta da ke qara Masa qaunar ta, can ya Dan Bata Rai, sannan ya kalle ta, da alamar ta aikata laifi, da sauri ta nutsu, ta daina magana, tare da Dan ja baya kadan, tana wulla ido,
"Wai a ina ma kike Jin maganganun da mukai daga Ni sai Abbaa? Dan na tabbata ba shi ne zai fada maki ba, ba Kuma na Jin Sumaye zata sanar da ke, fada min"
A hankali ta fara takawa zata gudu cikin gida, Shima bin ta ya dinga yi, tana Jin ta Sanya qafar ta cikin gida ta Masa gwalo, ta taka da gudu zata shige, hannun ta ya ja ta koma baya, cikin tsananin tsoro da Jin wani irin Abu Kamar wuta ta ja ta, ta kwalla qara, ba Bata lokaci kuwa ya sakar Mata hannu, kunya ce ta Kama ta, ta hau dariya.
"Hamma Yaseer, ka ji wani Abu, Kamar wutar lantarki?"
Dariya kawai ya yi, ya kauda Kai,
"Fada min a ina Kika sani?"
"A can na ke labewa in kuna zaune a zaure, ina son Jin maganar ka, muryar ka akwai dadin sauraro, musamman in kana bada hadda"
Kama Baki ya yi, tare da tafa hannu, Yana salati, sai kallon ta ya ke Yana zaro idanu, alamar ta yi abun kunya,
"Laaa ilaha illallah, tabdi jam, maaaryaaamaaa ke ce kike sauraran murnar maza subhanallahi"
Cike da Jin kunya Mai tsanani ta shige gida da gudu, tana dariya, fuskar ta a rufe da tafukan hannun ta,shi din ma dariya ya dinga yi, saboda yanda ya Mata ya bashi dariya shi kan shi.
Da yamma bayan Lamido ya dawo daga wajen Saida zumar shi, suna karatu da Little, Little ya sunkuyar da kan shi, Yana Sosa qeya, Dan ya kula in bai magana akan abinda suka fara tattaunawa dazu ba, Lamido ba zai ba.
"Ammm Abbaa..naceee"
"Ihumm ka ce mi?"
"Dama akan maganar Nan ce ta dazu, nace na amince Zan koma, min Yi magana da Maryama, shawarar da ta bani ta matuqar yin tasiri a raina, inshaa Allahu Zan koma, Amma in neman alfarma"
"Masha Allah, da kyau, ka yi nazari Mai kyau, Kuma Allah ya muku albarka dika, me ne ne alfarmar da ka ke nema?"
"Abbaa Dan Allah na ce, imm ka bari ba yanzu ba, so nake sai na qara yin zurfi a ilimin addini, in ya so sai na koma"
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......