Wata uku kenan da Naseer ya gano Nusrah na dauke da juna biyu,amma bai sanar da ita ba, ya maida hankali sosai wajen bata kulawa ta musamman, Ita kuwa ta na mamakin rashin ganin al'adar ta da bata yi ba na watannin, sai ta dauki hakan da wani ciwo ne wataqila ke damun ta,sam bata san ciki bane,dan kuwa ba ta laulayin komai, sannan ba ta Jin kwadayin komai, sai dai a baya ita din Mai son Abu Mai sugar ne, Amma yanzu ko a tea ba ta qarawa, in ma zata Sha kenan, ta fi son Abu Mai gishiri, ko Mai Dan tsami tsami.
Ranar da Naseer ya ga dama ya sanar da su kuwa, gaba Daya familyn ya cika da murna, Nusrah kuwa matsananciyar kunya ke dawainiya da ita, ga jikan ta qarami, sannan itama a ce Nan gaba zata haihu? Kaiii wannan Abu da kunya yake, what if ta zo haihuwa ta Yi raki? Maryama ya zata na kallon ta? Abun duniya ya taru ya Mata yawa akai, ganin irin nauyin da ta dorawa kan ta ne ya Sa Naseer sanar da Ammaa, Yana tsoron Kar ta sawa kan ta damuwa ta hadu da wani ciwon, ko ma a rasa babyn.
Ammaa Bata Mata magana direct ba, sai ta tsiri cewa Maryama ta Kai ma Nusrah Lamido, ta ce zata Dan Yi wani abun, in ta na ganin shi akai akai, Kuma suna yawan haduwa da Maryaman wataqila za ta rage yawan Jin kunya da nauyin da ta ke ji.
Hakan ce kuwa ta faru, sai ga Nusrah na wasa da jikalle, har da su goyo, Yadikko ta ce yannema yanzu dai kunya ta qare ko, sai ta yi ta dariya.
Little ma ya Yi qoqari sosai wajen cire wa Nusrah kunyar da ta dorawa kan ta, in ba shi da makaranta daga shi har Maryama da Lamido za su sashen ta, su Sha hirar su,a Nan za KU ga iyayin Kaka, Kar a mishi wannan wancan za a mishi, da sauran ire iren abubuwan Nan.
Maryama ce tsaye a jikin murfin mota ran ta dik a dagule, ta turo Baki, Nusrah na tsaye da Lamido a hannu,
"Yanzu Yadikko ba Zaki Bari ki zaman ki anan ba, Abbaa na ya Saba da ke, in kin tafi zai kuka,nima zan Yi kuka, wa zai dinga Yi mishi wanka, Ni fa har yanzu ban iya ba"
"Haba Maryama , ai sai nai rashin hankali Kuma, kin haihu lafiya a gida, kin samu jego Mai kyau, Kuma wankan Nan kullum a gaban ki ake yi, Amma ki ce ba ki iya ba, ko da ke in ka ji ana qi gudu, to sa gudu ne Bai zo ba,da na tafi iyawa za ki, can gida yarinyar Nan Mai Taya Ni aiki ita Daya ya rage, wata da watanni ina Nan, Bai kamata ba"
"Ni dai gaskiya Yadikko bana so ki tafi"
Bubbuga qafa ta Fara ta qanqame murfin qofar,
"Wai ke Maryama yaushe Zaki daina bani kunya ne, Dan Allah dibi yanda Lamido ke kallon ki, ko kunya ba Kya ji" In ji Yaseer da ke mata dariya.
"Indai wanka ne Ni zan dinga mishi, shi kenan?" Kamar ba Nusrah bace tai maganar,ta na fad'a ta yi shiru.
Da sauri Maryama ta je kusa da Nusrah ta tsaya tana dariya, haqon ta ya cimma ruwa, Yadikko da ta Gama gano abinda Maryama ta Yi, girgiza Kai ta Yi tana dariya, little ya ja motar, suna ta Daga Mata hannu.
Maryama bangaren Ammaa ta Yi, Nusrah kuwa ta tafi da Lamido, suna shiga Ammaa ta ce,
"Yarinyar Nan kin iya drama ,cikin ruwan sanyi kin sa surukar ki zama qawar ki"
Dariya ta Yi, sannan ta ce,
"Ni bana Jin daɗin yanda ta ke Jin kunyar mu, to gwanda ma shi, tana sakewa sosai da shi, Amma ni kunya ta take ji sosai, Bata Hira da ni na minti goma, bangarena kuwa sau Daya ta taba shiga, Amma Kinga yanzu ta dalilin Abbaa na ta shiga ya fi sau a qirga, ko kukan shi ta ji za ki gan ta, ta dauke shi ta goye, shi ma ya ji dumin kakar shi"
"Maryama duniya, ohhh, Baki abun magana"
Dariya ta yi ta dale kujera, sannan ta tankwashe qafa,
"Ya basir din naki,da sauqi ko?"
"Ya yi sauqi sosai Ammaa, tinda Yadikko ta hadan maganin Nan tsiron da ya min ya koma,"
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......