ALMAJIRI NA.....PAGE 47

1.7K 141 14
                                    

Washegari da safe, bayan sun yi sallar asuba, little ya yi iya qoqarin shi dan ta amince da shi , taqi, da ya matsa mata ma kuka ta sanya mishi, gaba daya ya rasa inda zai saka rayuwar shi ,haka ya zauna ya na lallashin ta, dan dole amma ba dan ya so ba.

Gari na qarasa wayewa, yana bacci ta yi wanka ta yi kwalliyar ta cikin atampa riga da zani masu kyau, ta fesa turaruka masu sanyin qamshi da dadi, leqawa ta yi ta ga bacci ya ke yi, zumbura baki ta yi, Ita dai yunwa ta ke ji, ga shi bata ga wani alamar akwai kayan abinci ba a gidan, duk iya binciken da ta yi, tunani ta fara ko za ta shiga wajen Amma ko Mama ne?

Sake leqa shi ta yi, idanun shi a rufe, amma ya tashi tun sunkuyawar da tai na farko ya farka, amma baya son bude ido ya kalle ta, a yanda ya ke ji ko ta qarfi ne zai iya kwatar haqqin shi,kuka ta fara yi a hankali, tana jin yanda cikin ta ke qara yana murdawa, kitchen ta koma ta bude flask din da suka ci kaza jiyan, ta dinga bin qashin tana taunewa, ta dauki wani qashin za ta kai Baki little ya shiga sanye da jallabiyya, Yana brush Amma ta Kira shi ,ta ce su je cin abinci.

Sake baki ya yi yana kallon ta, ko a jikin ta, turo baki ta yi ta ce masa.

"Hammaa Yaseer yunwa na ke ji, dan Allah ka sama min abinda zan ci kar na mutu"

Hawaye ne suka fara zuba a idon ta, daf da ita ya je, ya amshe qashin ya mayar ya rufe, sannan ya rungume ta a jikin shi, yana jin yanda jikin ta ke motsawa a nashi tana kuka, cikin murya mai cike da buqatuwa y fara magana.

"Dan Allah yanzu da kika nemi abinci kika rasa ya kike ji?"

"Kamar zan mutu Hammaa dan Allah ka taimake Ni ka bani abinci yunwa nake ji"

Kuka ta sake sanyawa, cike da shagwaba,

"Maryama abinda na ke ji akan ki ya fi yanda ki ke ji a kan abincin nan, na roqe ki domin Allah tun jiya ki amince min mu raya sunnar Annabi kin qi, ke ba jahila ba ce Maryama dik da qananun shekarun ki ba abinda Lamido bai mana bayani akai ba, kin san komai, amma ki ke hana ni haqqi na, kin san dai yanda Allah ke fushi da duk wanda bata ba mijin ta haqqin shi ko?"

Shiru ta yi, cikin dabara ta kwace jikin ta, ta koma gefe kan ta a qasa, idanun ta na zubar da hawaye, tausayi ta bashi, dan haka ya kawar da abinda ke ran shi .

"Mu je mu ci abinci Amma ta kira Ni tun dazu, mu ake jira, ki wanke fuskar ki, kar ace na ci zalin ki, bayan ke kike cin zali na"

Lakace mata hanci ya yi, ya wuce parlour ya zauna yana jiran ta.

Tsaf ta fito, sanye da mayafi kalar kayan ta, suka fita, ya so ya ɗan riqe hannun ta, amma inaa tana can bayan shi, In ma ya tsaya su jera sai ta sake maqewa a baya.

Ta fara bashi haushi dan haka ya wuce abinshi ya barta a bayan, tunda haka ta ke so, suna shiga suka tarar Naseer ya ja ma Nusrah kujera suna qoqarin zama, da sauri Yaseer ya isa wajen su, ya durqusa ya gaida su, Maryama ma gaishe  su ta yi, Amma ce ta fito daga kitchen a bayan ta akwai masu aiki biyu maza, dauke da abinci, suka ajiye, nan suka hadu duka suka gaishe da Amma, zama suka yi, Nusrah ta miqe tana zuba ma kowa abinci, Maryama ta matsu a zo kan ta, qamshi da kuma kyawun abincin duk ya sa yunwar ta dagowa, Nusrah ta kula da matsuwar da Maryama ta yi, cikin danne murmushin da ke son kwace mata ta aje na little ta zuba mata, tana gamawa kuwa ta ce.

"AlhamdulilLAAH , na gode mama"

Ta danna hannu bayan ta yi bismillah ta fara ci, kowa sai da ya yi dariya saboda yanda ta yi, kamar ta jima bata ci abinci ba,kunya ta dan ji kadan sannan ta ci gaba da loda abincin ta.

"Acicin Sumaye kenan, ci ba qiba asarar hatsi"

Kallon shi ta yi da harara, ta kai nama bakin ta,

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now