Da sauri ya isa gare ta, zai rungume ta yanda suke yi a da, sai kuma ya dakata, murmushi tayi, Habi na tsaye a gefen su, zuciyar ta na zillo,tabbas akwai matsala,haka Little ya koma? Sai dai Allah ya kiyaye.
Kafadar shi Hajiya ta bubbuga, ta kama hannun shi don shiga ciki, wani irin sabon lamari little yaji, kamar yau ya fara taba hannun Hajiyah, ita kan ta ta ji sauyi, wannan hannun saurayi ne matashi, ba hannun little da ta saba sanyawa a nata ba qarami.
"Little abinci zaka fara ci amma ko? Dan naga alama baka buqatar wanka, kaga yanda kayi kyau kuwa ka zama babban magidanci,"
"Habaa Mum wanne irin magidanci, haryanzu ni little din ki ne, jina nake kamar dan shekara takwas da kk sani,indai ina gaban ki bana jin na girma"
Hajiya ce ta ce,
"Habi lfy? Naga kin tsaya kin qame kamar wata soja,akwai damuwa ne,"
Yawu Habi ta hadiya mai qarfi, sannan ta girgiza kan ta alamar ba komai,nan Yaseer ya gaida ta ta amsa, kitchen ta koma ta dakko mishi cake din da hajiya ce ta yi shi da kan ta, na murnar kammala karatun shi, nan aka kira Idi, da sabon drivern da Hajiya ta samu shekara biyu d suka wuce,mai suna Malam Hamza,tare da su aka ci aka sha, Hajiyah sanye da dan qaramin mayafi, sai daukan su hotuna Habi take ita da Little, murna sosai suke musamman little, yana matuqar jin dadin soyayyar da Hajiyah ke nuna masa kamar dan da ta haifa a cikin ta.
Bayan su Idi sun gama cin abinci ne suka sake taya shi murna sannan suka fita,Idi na ta tsokanar Little, dan shi kan shi ya yi mamakin ganin yanda ya koma lokaci kadan.
Hamma yayi tare da miqa, idon Hajiyah akan shi, dan kuwa ta kasa daina kallon shi, gashin kan shi mai laushi ta sanya hannu ta shafa,
"Bacci ka ke ji ko? Maza tashi kaje ka huta, kafin anjima sai ka tashi kayi sallah,"
"Ok Mum, thanks for everything"
"Yaseer dik abinda na maka, kar ka taba ji a ran ka taimako nake maka, a yanzu ka zama dole na, ina nufin kai d'a na ne, ina son ka sosai jini ne kawai bamu had'a ba, amma akwai soyayyar da takan wanzu tsakanin mutane da ta fi ta jini ma,so ka dai na min godiya,maza je ka kwanta"
Itama tashi tayi, ta kama hannun shi suka nufi hanyar dakin shi, ji yake kamar ya kwace hannun shi a nata, saboda yanzu ya san me ne ne sha'awa, tabbas dadin da yake ji in ta tab'a shi daban ne, baya son jin haka daga gare ta, cikin dabara ya zare hannun shi ya sosa qeyar shi da shi, sannan ya zira a aljihun wandon shi, koda suka isa d'akin ita ta bud'e tana murmushi, tare da kallon fuskar shi,kallon shi take taga ko ya yi farin ciki da sauyin da ya gani?
Sosai yaji dad'in yanda aka maida masa d'akin shi na matasa, godiya ya mata sosai, sannan ya rungume ta a jikin shi ya yi kissing kuncin ta, sai da ya aikata hakan ya yi saurin sakin ta ya yi baya yana ware hannaye da idanu,
"I am so sorry, ban san...."
"Shiiiii, i am ur mum, kar ka damu, sai anjima,"
Ja mishi qofar ta yi ta fita, kama kan shi ya yi ya zauna,bakin gadon shi, tare da furzar da iskar da ya cika a bakin nashi,
"What is wrong with me? Hajiya ce fa Yaseer, wadda take a matsayin uwa a wajen ka, me ye wannan ka ke ji game da ita, ta haife ka fa,ya salam"
Ta shi ya yi ya gyara kwanciyar shi, kallon gefen gadon ya yi, nan ya yi ido biyu da wani qaramin abu an yi wraping din shi da abun wraping gifts blue sai kyalli yake.
Rufda ciki ya yi ya miqa hannun shi ya ja wo, budewa ya fara yi, abinda ya gani ne ya sanya shi miqewa da sauri zaune, tare da sake wani kyakkyawan murmushi a fuskar shi,
"Wowww, wannan babbar ta Fa'iz ce,"
Waya ce mai kyau, da tsada, an gama hada ta har da caji an sanya mishi, nan da nan ya fara dubawa, SIM biyu ne a ciki, dik da bai tabbatar cewar akwai Data ko babu ba dannawa ya yi,ya shiga Vidmate da ya gani, nan da nan kuwa ya ga videos, wata qarar murna ya sake, ya fita daga dakin da gudu, a zaune ya tadda Hajiya ta lula duniyar tinani, ji tayi an zauna kusa da ita da qarfi, a razane ta kalli gefen ta,
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......