Lips din su ke gogar juna, wani irin abu Little yaji kamar wutar lantarki ta ja shi, inda ita ko Hajiyah wani baqon yanayi da bata taba shiga irin shi ba ke fisgar ta, daga yatsun qafar ta zuwa kowanne sashe na jikin ta, idon ta lumshe tana qoqarin karbar saqon da lips din little ke son bata, da sauri ya janye bakin shi ya miqe ya fara zagaye dakin, cikin matsanancin tashin hankali, kan shi ya dafa da hannu bibbiyu, idanun shi sun kada sun yi jawur,kallon ta ya yi ya ga ba wani alamar damuwa a tattare da ita, sai ma mamakin tashin da ya yi, ba shiri ya ja riga ya zira, ya fita waje, tare da rufe qofar da qarfi, key din motar ta ya gani a saman dinning, zara ya yi ya sanya takalmin shi ya fita, bai ko gama kwarewa a tuqi ba, amma haka ya shige, har zai murda key, ya yi wani tinani, ya fice a motar, bude qaramar qofar gate din ya yi, Idi na ta masa magana amma bai kula shi ba, tafiya yake ta yi a qafa, iskar da ke kadawa cikin daren na qara masa shauqi, da kwadaituwa wajen kusantar mace, ba kuma wadda yake hangowa a tare da shi sama da Mum din ta shi, qarfe tara da rabi ta gota kadan, bai san ya yi tafiya mai nisa ba, sai da ya ji wani dan qaramin almajiri na bara a qofar wani gidan da ba hausawa bane, sun tsaitsaya a bakin gate din su yaron na musu waqa irin ta almajirai, suna rawa suna dauka a wayoyin su, da ganin yaron a yunwace yake, amma basu damu da bashi abinci ba sai daukan waqar shi suke, yaro ya taqarqare yana rera waqar bara.
"Lanzika Inna lanzika"
"Minal kitabati min kulli manzilin"
"Na iya Inna na iya"
"Na iya kalmar duniya"
"Duniya ba gida bace"
"Lahira can gida yake"
"Iya kinji karatun dan Bura"
"Dan bura Malam Raziqu"
"Hanwawa da lawai lawai da karan gashin ta guda bakwai"
"Innata dangi na fadima"
"Na Annabi masu rikirkida"
"Abasu dami su mayar hura"
"Abasu dami su mayar tuwo"
"In an gama a 'yanmmana"
"Dan cakum iya dan cakum"
"Malmala goma ta yaro ce"
"Ni sittin naka sharbewa"
"Ga hamsin bisa lebu na"
"Ga sittin bisa hanci na"
"Ko qoshi ban hwara ba"
"Sai na gama da buhun dussa, in tai rahi in tunhwaye"
"Maula ta sidi maula ta balarabe,"
"Maula"
"Babban gida da dad'in bara yake"
"Maula"
"Waccan ta baka waccan ta hana maka"
"Malmala"
"Waccan ta dauko kulki na gaya ma ka"
"Malmala"
"In kibbigen ki na biyan malmala da qirin dawo"
"Mal.......
"Kaiiii...zo nan,"
Cikin wata iriyar murya mai dauke da fushi Little ya kira almajirin, wanda ya sa yaron kasa masa musu, da gudu ya sheqa, ya durqusa gaban little, shi kuwa, kallon yaron ya yi, dik ba zai wuce shekarun shi ba, a lokacin da Hajiya ta dauke shi ya na almajirantar shi.
"Kasan qarfe nawa yanzu? Ka tsaya wajen wadan can sun hana ka abinci mai makon kaje gaba, ka ke ta musu waqa, wanda ba lallai su ba ka abinci ba ma"
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......