Tun safe ta ke gyara jikin ta saboda sun yi da Yaseer za su fita, Indo kuwa har sake nuna mata inda hoda bai ji ba take, tsaf ta fito abun ta kamar yanda ta saba shigar doguwar riga yau ma ita ta saka.
Horn din motar shi ta ji, cikin azama ta fice suna sallama da Indo, ko da ta fita bata san sanda ta bude baki ba dan ganin kyau da Yaseer ya yi.
Qananan kaya ne a jikin shi wanda su kai matuqar yi masa kyau, ya sanya farin glashin shi a idon shi, kallon ta yake ya na murmushi, a hankali ta dauke idon ta ta isa motar ta shige.
Hanya ya dauka wadda ba ta san ina za su ba, Ita dai kawai suna tafe, sun yi tafiya da ta kai ta awa daya kafin ya tsaya gaban wani gida mai matuqar kyau (gidan da suke a yanzu kenan) sake baki Safiyyah ta yi, saboda a iya yawon ta bata taɓa shiga irin gidan ba, ko a gidan qawaye kuwa.
"Bismillah"
Daga kai ta yi ta gefe ta gan shi tsaye, ya bude mata qofar.
Shi da kan shi ya bude qaramar qofar gate, Suka shiga, kallon ko ina Safiyyah ta ke tana kumawa.
"Ina ne nan?"
"Mu shiga za ki gani"
Komai na gidan ya mata, ji ta yi kamar kar ta fita, kawai a Daura auren su daga nan ta tare, kallon shi ta yi cike da kashe ido, kallon ya shiga kowanne saqo da lungu a jikin shi .
"Gidan ki ne nan, a nan zamu zauna bayan aure"
Tsalle ta daka ta dale shi saboda murna, Yaseer kuwa difff ya yi saboda kasalar da ta saukar mishi.
Bayan ta ya fara shafawa, daga kan ta tayi taga yanda idanun shi suka koma, ba sauqi, ja tafara yi baya, tana kada masa kai alamar ah ah.
Shi kuwa kashe ido yake da alamar roqon ta aminta da shi , tana kaiwa jikin dinning table ta tsaya, nan da nan hawaye ya taru a idon ta, cike da tashin hankali ta fara magana .
"Dan Allah ka yi hakuri, kar mu yi haka da kai, ban taba zina ba(ta manta da soyayyar shan minti da take, ko an fada mata hakan ba zina bane oho) sauran sati daya auren mu, ka jira lokaci ya yi"
(Hattara mata masu bin saurayi ganin gidan da za a zauna, Dan mazan yanzu ko da qanwar ki kuka je in ya so Sai ya fyade ki a Kula)
Hannun ta ya kama ya fara murzawa a hankali, ya share mata hawayen da daya hannun,
"Yanzu da yau da sati dayan me ye bambanci? Ba fa gudun ki zan yi ba bayan mun gama, na yanke shawara ke zan aura, tunda nake ban taba jin ina son auren wata ba sosai kamar yanda nake ji akan ki, in ban aure ki ba mutuwa zan yi,"
Hawayen shi ta ji a qafar ta,da sauri ta daga kan shi ta ga yanda suke zuba, sosai ta tausaya mishi, amma tana nan akan bakan ta, ba zata bashi kan ta ba, to me zata bashi ba yan aure?
Janye jikin ta ta yi ta fara tafiya waje, da sauri ya ja ta jikin shi, a gaggauce yake kissing din ta, da qarfi ta kwace jikin ta ta yarfa mishi mari, zaro Ido ya yi waje ba alamar wasa ko son shi a fuskar ta,yatsan ta manuni ta nuna mishi ta kada shi sannan ta fice, Yaseer na nan a tsaye kamar an dasa shi.
Ta yi tafiya mai nisa tana kuka ta ji horn din shi, qin tsayawa ta yi ta qara sauri, duhu ya fara sauka amma ko a jikin ta, ga tsoron ba zata gane hanya ba ma na komawa gida .
Fita ya yi a motar ya sha gaban ta, kama kunnen shi ya yi, tare da furta mata kalmar hakuri, da kyar ya samu ya shawo kan ta ta shiga, da tana da zabi ko ta san hanya da a qafa za ta tafi.
Ko da suka isa gida sun tarar da Indo tsaye a bakin qofar da wasu matasa, sai masifa take dangane musu
"Dalla can ku tafi, gayyar na ayyana gayyatar tsiya kawai, gayyar wa gairamu , me kuke da shi da za ku auri Safiyyah har ku bamu? To ku sani sauran sati bikin ta, qafar wani bana son sake gani........yauwaaaaaa ga su nan sun dawo ita da mijin nata"
Dukkan su juyawa su ka yi dan ganin su , sun jima kafin ta fita, gyara jakar ta ta ke, wadda ta zuba kudin da Yaseer din ya bata, ta fito daga motar , Indo na rakube ta fito fili sosai , ta hau daga ma Yaseer hannu, Safiyyah kuwa shigewa gida ta yi ko kula samarin da ke faman yi mata magana ba ta yi ba.
Yaseer ne ya fita daga motar suka gaisa da Indo, ya miqa mata kudi yan dari dari kimanin dubu biyar, kamar zata kwanta dan godiya, nan fa ta samu ta ci gaba da zagi tare da wanke matasan ta shige gida, ko da ta shiga ta ga bata ga mutumiyar ta ta ba sai ta nufi dakin ta,shessheqar kukan ta ne ya sanya Indo Isa gaban ta da sauri ta zauna.
"Me ya faru Safiyyah? Kin san bana son damuwar ki fa, sanar da Ni me ya faru?"
Dagowa ta yi tare da zayyana mata komai tun fitar ta, dogon tsaki ta ja ta daidaita zaman ta tare da karkata baki tace
"To Ni ba na zaci wani abun bane ba ma, ina ce ya kawo komai na aure, hatta da lefen ki ga su can, sadaki da shafa Fatiha ne kawai fa ya rage, so ki ke ya fasa, nan nan ba qananan yaran nan ke lagudar ki a banza ba, ko sisin azziqi ba bu, ba gwanda shi ba"
Baki sake ta ke kallon Indo, lallai Indo ta fita son kudi, ita ce fa da take mata nasiha, Amma tinda Yaseer ya fara neman auren ta halayen Indo kafff sun sauya, kenan dama itama Tana da son abin duniya haka?ba ta Kula ta ba ta koma ta kwanta, ta ci gaba da kukan ta.
Muskutawa Indo ta yi dan ta yi magana cinnaka ya manna mata cizo a duwais wani ihu ta saka ta miqe tsaye,
"Azabatul ula tsohuwa ta ji belet, haska min shege sai na kashe shi zan ji dadi"
Safiyyah na jin haka ta san cinnaka ne ya mata aiki, dariya sosai ta dinga yi sannan ta qi haskawa da wuri, qarshe dai barin dakin ta yi tana masifa.
Bayan auren Yaseer da Safiyyah, Yaseer ya ji dadin yanda ya same ta da budurcin ta duk da raunin da ya yi, ya san ta wajen soyayyar shan minti ne amma ba wanda ya taba kwanciya da ita.
Ya ji dadin hakan, ko ba komai a halayyar shi, bai taba zaton samun mace irin wannan ba, Safiyyah ta ga gata kuwa, wanna dalilin ne ya sa yake girmama ta, dik son da take mishi Bata bashi Kan ta ba kafin aure.
Bayan an kwana biyu Yaseer ya koma ruwa wajen neman matan shi, har ya Gama dokin ta, dik da son da yake mata na nan, na musamman ne,Amma ya na sha'awar qara aure.
Haduwar Safiyyah da Habi ne ya sa ta koyi xuwa gidan bokaye da malaman dibbu, Dan kawai Kar Yaseer ya qara aure, har da makirci da sharri ba Wanda ba suyi ba.
Har Indo ta koma ga mahaliccin ta bata taɓa raka Safiyya gidan boka ba, duk son kudin ta kuwa.
**************************
Little ya taso ya gan shi a gidan almajirai, Kuma ya tabbata shi din ba haifaffen gidan bane, Duba da duka zagi da Kuma gorin da malam da daliban shi ke masa.
Abinci baya isar shi, Sai ya fita ya nema, dik qanqantar shi Sai ya nemowa qolayen makarantar wani zubin harda malam ma, in Suka ci su Dan rage Masa kadan, wata rana ya je ya sake bara, wata Rana haka zai xauna da yunwa.
Daga baya da ya ji azaba da wahala ta ishe shi shine ya gudu.....
CI GABAN LABARI.........
Ku dakace ni a next page inshaa Allahu, ku qara hakuri da ni, abubuwan ne Sai godiya na yi busy sosai.
Much love to u all.😍❤️
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......