Idi ne riqe da murfin motar ya bude ma uban gidan na shi bayan ya shigo gidan, qarar motar Alhajin ne ta sanya Hajiya Safiyyah saurin sauka daga jikin Little, shi kuma ya shige dakin shi, zama tayi tare da ɗaukan wayar ta kamar ba abinda ya faru.
Qofar parlourn aka buga ta tashi cikin yangar ta da kullum qirqirar wata take, ta bude qofar, ganin Alhajin ne ya sa ta amshi Jakar hannun Idi da kayan da ke hannun shi tana mamakin ganin kaya irin wadannan a hannun mijin ta, me zai da irin kayan nan?
Bayan ya zauna ya cire hular shi ne ya zamo gaba gaban kujerar ya kalli Hajiya Safiyyah da tun shigowar shi ta gane me ya faru, yaje asibiti bai ga mara lafiya ba.
"Hajiya wai ni me ya sa kike yanke hukuncin abubuwa ba tare da kin min bayanin su ba, a qalla na cancanta ki min waya ki min bayanin ya ake ciki game da matar da ni na kade ta, ah ah kawai sai da na je likita ke sanar da ni komai ya kamata kenan?"
Yanda ya mata magana ta san he is serious dan haka ta sanya fuskar tausayi nan da nan idanun ta suka kawo hawaye, cikin murya mai rawa kamar wadda take shirin fashewa da kuka ta fara magana.
"Dan Allah da son Annabi ka yafe ni , ka yi hakuri akan duk abinda na ke aikatawa ba tare da na yi shawara da kai ba, ko na sanar maka, ban yi da wata manufa ba sai dan na hutar da kai, a gani na ayyukan da ke gaban ka sun sha ma kai, kuma tunda ka iya ka kira ni ka sanar da ni me ya faru ka yadda dani ne kuma ka yarda zan iya zartar da komai ko baka nan, amma ban san abun ba haka ba ne, ka yafe min"
Kukan da take riqewa ne ya kwace mata, ba bata lokaci kuwa Alhaji ya zube gaban ta, tare da jan ta saman cinyar shi, suna zaune a nan qasan ya kwantar da kan ta a qirjin shi yana shafa bayan ta, Ita kuwa ta yi luf tana shessheqar kuka tare da murguda baki da fari da ido , da ka gani ka san na mugunta ne, haqon ta ya cimma ruwa kenan.
"Haba Safiyyah daga magana sai ki kawo zancen ban yarda dake ki yanke hukunci ba? Ni dai ba haka nake nufi ba, ina nufin ina laifi dan kin sanar dani, tunda abun ya shafi rayuwar wata"
"Ka yi hakuri, na yi la'akari da yanda ka shiga damuwa ne, na yi zaton ka dawo gida ne dan ka kwantar da hankalin ka sannan ka koma, bana son kiran ka na rusa maka kwanciyar hankalin ka, shi ya sa ka yi hakuri"
Wasu sabbin hawayen ta matso, hannu ya sa ya fara share mata su, sannan ya yi kissing kuncin ta.
"Kema kin san ba yanda za a yi baki a waje hankali na ya kwanta, da kwanciyar hankali na ke nema wajen ki zan tsaya ko? (Mata muji tsoron Allah akan komai, dubi yanda ya aminta da ita amma take cin amanar shi)"
"Haka ne, to ka yi hakuri, ka san ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, ni na rasa iyaye na, ba zan so ita ma ta rasa na ta ba, a yanda ta ce mana kamar ta bar mahaifiyar ta a gida ba lafiya, kuma ka ga tace min hawan jini gari mahaifiyar ta, in Bata koma ba ba a san me zai same ta ba, gwanda ta koma da ciwon akan ta zauna basu hadu ba ta zaci ko mutuwa diyar ta tayi ko?"
"Haka ne, amma ta ban tausayi baby, da na san garin su da na je na basu hakuri na musu ihsani, kuma na bata kayan ta da ta manta a waje na,"
Zabura Hajiya ta yi ta sauka a jikin shi, wani mugun kallo ta watsa masa,
"Ka je garin su? Akan me? Me zai sa ba zaka aika ni ba sai kai ne zaka? Ban yarda ba to, Ni dai bana son irin wannan, sanin kan ka ne yanda nake matuqar son ka da kishin ka mace indai sunan ta mace bana son ta rabe ka nesa nesa, ka aje kayan indai na samu dama zan yi bincike a kan ta na aika mata har inda take"
Fuuuu ta shige daki tare da banko qofar sai da ya rufe ido tare da toshe kunnen shi, ya qanqame jikin shi .
Little ne ya leqo Dan ganin me ya faru yaji qara kamar an rufe qofa da fada.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......