Sun Jima a tsaye kowa da abinda yake saqawa, Amma Kamar wadan da aka daurewa bakunan su ba Wanda ya iya furta ko da kalma daya.
Cikin zuqatan su suke magana.
'wannan Kama haka, ko dai ido na ne, saboda tsabar kishin da na Sanya wa rai na, ba zan biye wa zuciya ta ba zan dauke ta in har ta amince ko driver Sai Yana Kai ta Tasha kullum, in Kuma sun amince ma har kwana ta yi, har lokacin da zan ji sauqi'
'wannan wace ce, haske kawai zan nuna mata, Amma muna Kama sosai,... silly me...haka Allah ke halittar shi me zai hada ni da ita, da ganin ta ba wata babba bace, bare na ce ko ta haifen'
'Ya Allah ka nuna min Yaseer dina, ba dan wannan yafi Yaseer dina ba zan iya zuwa da gudu na rungume shi na ce Yaseer d'ina ne, Amma wannan babba ne, ko dai girman jiki ne? Koma me ne ne ga su a gabana zan ji ko me ke tafe da su'
"Bayin Allah lafiya? Na ga dikkan KU kun tsaya cirko cirko Kamar zakaru"
"Babbbarka da rana, baqi ne daddaga garin Adamawa" cewar Hajiya Safeeyah da ta dawo daga cikin rud'anin da ta shiga.
"Bismillah'n ku ku zo ku zauna Mana"
Tabarma Yadikko ta shimfida masu, Nusrah Sai satar kallon Little take, shi din ma kallon ta ya ke,
"Ikon Allah, wannan yaro naki tubarkallah Masha Allah, rainon qasar waje ne da ganin shi ko Hajiya, yaro Kamar Rana Bata taba shi, kuyi hakuri na cika KU da surutu Nusrah dakko musu madara,...me ke tafe da ku bayin Allah?"
Kallon Yaseer kawai Yadikko ke yi, tana sakewa, cikin zuciyar ta tana ayyana kamannin shi da na Nusrah Wanda kowa zai iya tabbatar da kamannin, Sai dai da ganin wannan yaron a gidan hutu ya tashi, Yaseer din da ta yadda a gidan almajirai ta yadda shi.
Madara Nusrah ta aje masu a cikin kwarya daban daban, sannan ta samu waje ta tsugunna Suka fara gaisawa cikin harshen fullanci,
"Baiwar Allah ya jikin naki? Dik da na ga kin samu sauqi a ido, ban sani ba ko akwai inda ya ke maki ciwo, ki yafe mu bamu samu zuwa sake duba ki ba, Mai gidan ne baya qasar shi ya sa,"
Cikin hausar ta da fulatanci ta cinye ta amsa ta da
"Na ji sauqi sosai, ba ciwo ta ciki, kurjewa ne dama Sai dinkin Kai na, Kuma kin gani ya warke,ba bu matsala, ai na fada maki na yafe ma kowa"
"Allah sarki, kina da zuciya Mai kyau,mun gode...wannan ita ce mahaifiyar ki da ki ke ta damuwa Zaki dawo gare ta"
Murmushi Nusrah ta yi ta ce
"Kwarai kuwa, ita ce, Banda Kamar ta dik duniyar Nan, ba San iya zuwa ko ina na kwana Daya ba tare da ita ba, rayuwa ta na hade da ta ta ne"
"Allah sarki lallai akwai soyayya Mai qarfi a tsakanin ku,"
Juyawa Hajiya ta yi taga yanda Yadikko ke kallon Nusrah cike da so da qauna, tare da kulawa, Nan ta sake tabbatar da irin soyayyar da ke a tsakanin su, kwana ba zai Yu ba, Sai dai zuwa ta dawo.
"Baba na so da qoqon bara ta a gare ku, ina fatan zaku cika min shi da buqata ta,"
"Baiwar Allah ke kuwa me kike nema haka, bayan ni'ima da kk ciki?"
Murmushi Hajiya Safiyyah ta yi sannan ta ce
"Tabbas ba abinda zan cewa Allah Sai godiya, ya azurta ni da miji da d'a ga arziqi ba abinda zan ce mishi Sai godiya, ina neman alfarma ne, in ba damuwa Dan Allah ki bani aron diyar ki a matsayin wadda zata dinga taya ni aikace aikacen gida, saboda rashin lafiya da na ke fama da ita , aiki ya min yawa, ga yaro na yana zuwa makaranta, Mai gidan baya Nan, aiki na min yawa, ko nawa kuke so KU sanar da ni zan baku"
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......