Hajiyah Safiyyah da Little ba su da aikin da ya wuce faranta ma junan su rai, wasanni kala2 suke irin na masoyan da suka shaqu da juna.
Hajiyah Safiyyah ce sanye da riga doguwa mara hannuwa, ta kama ta ta saman qirjin ta, dik yanda ta motsa sai suma sun motsa,idanun ta daure da baqin dankwali, sai laluben inda zata ji Little take dan ta kama shi, shi kuwa yana can zaune a saman frizer din su ya zuba mata idanu, yana kallon yanda jikin ta ke rawa, ta fara gajiya,
"My little ina kk ne? Ni na gaji gaskiya"
Buga qafa ta fara kamar wata qaramar yarinya, sauka ya yi ya taka wajen ta cikin sanda, ya rungume ta ta baya, ya fara mata cakulkuli, suna ta zuba dariya tana ya bari kar wani ya jiyo su a waje, zubewa su ka yi a saman kujera,ta kwanta a saman jikin shi, ta zura hannun ta za ta kunce daurin ya riqe, hannun shi ya sa yana shafa kuncin ta zuwa lips din ta, kwantar da kan ta ta yi a hannun shi dake taba ta, saboda yanda ta ke ji.
Sauran kadan ya manna bakin shi a na ta,suka ji qararrawa na bugawa alamar akwai baqo ko baquwa, da sauri ta sanya hannu ta kunce daurin da ke daure a idanun ta, kame2 suka fara, sun rasa me zasu yi, ganin yanda ta rude ne ya sa ya ja ta jikin shi, ya qura mata idanu,
"Kwantar da hankalin ki, i am with u,ki bude muga ko waye, u told me to act normal, so act normal"
Iska mai qarfi ta furzar sannan ta shiga daki ta saka riga mai dogon hannu ta daura dankwalin da suke wasa da shi, fita ta yi dan bude qofar ta ga Little kwance a doguwar kujera yana kallo, yana latsa waya kuma a lokaci daya, as if bai ma ji ringing bell din da akai ba.
"Little kana nan kana kallon nan naka da baka gajiya ko? Kana jin qarar qararrawa amma kana zaune abun ka"
Bude qofar tayi Habi ta bayyana, cike da murna ta fara gaida Hajiyar, tayi kewar ta sosai,Hajiyah ma murmushi ta yi, ko ba komai Habi ta taimaka mata a baya, da ita ake qulla komai na makirci.
"Sannu da dawowa Habi, zaki dawo baki min waya ba? Bismillah shiga,"
"Ahhhh little da kana zaune nake ta danne dannen bell?"
"Bar dan rainin wayo, in ya fara kallo yanzu baya ji baya gani,bari katin ya qare ba zan sake sawa ba, makaranta zai tafi,"
"Habaa Hajiyah, ki hakuri, ai dan gidan nawa ba shi da matsala, kina ganin kyakkyawan saurayi a gida iwar haka ai mu godewa Allah, yaran yanzu da basu son zaman gida, sun fi son aje ayi ta qarya wajen abokai da 'yan mata, balle masu kyau irin shi, suna can suna lalata yaran mutane, suna yaudarar su da kyaun su, kuma ma shi da da bai damu da kallo ba, yanzu ma na rage lokaci ne dan baida abun yi, da ya shiga makaranta zai daina,
Little ne ya numfasa, cikin ran shi ya ce,
'Redio mai jini ta dawo'
"Ina yini Inna Habi"
"Lfy qlou dan Inna Habi, na same ka lfy?"
"Lafiya qlou, me kk kawon tsaraba?"
"Me ka aje min?"
"Ai ban san za ki dawo ba yau,"
Bude ledar hannun ta tayi, ta ciro masa quli mai sugar da kayan qamshi, cikin baqar leda, ta dakkowa Hajiyah ma nata, sannan ta zauna,
"Hajiyah Alhaji bai dawo ba ko?"
"Eh bai dawo ba, ki je daki ki huta dan ba wani aiki, anjima zamuyi magana,"
"To Hajiyah, Allah ya kaimu,"
Dakin ta shiga, taga maka makan jakunkuna a gefen katifar dakin, guda uku, bata san na me ne ba, bata da hurumin tambayar masu gida, bayi ta shiga bayan ta aje jakar ta, ta watsa ruwa ta fito, ta dade batai wanka mai dadi irin wannan ba.
YOU ARE READING
ALMAJIRI NA
RomanceYaseer ya fara rayuwa a matsayin almajiri, amma haduwar shi da Hajiya Safiyyah,zai sauya rayuwar shi daga cikin qunci zuwa walwala da yalwa, sakamakon soyayyar da zasu fara gudanarwa a cikin sirri.......