ALMAJIRI NA.....PAGE 50

1.8K 135 6
                                    

Asibitin Naseer ta tafi direct dan neman address din gidan shi wajen ma'aitan wajen, da kyar ta samu aka bata saboda qaryar da ta musu na yawan tashin da ciwon ta ke yi, tana so ta je wajen shi, tunda bai fito ba, sun so ta jira shi ta nuna musu sauri ta ke, tana gama jin inda gidan ya ke ta fice, ba bata lokaci ta hau titi, kamar wadda za ta tashi sama, haka ta ke zuba gudu a titin.

Ko da ta isa gidan, ta yi horn Mai gadi ya Dan jima kafin ya bude mata qofa, bai taba ganin ta ba, dan haka ya ke tunani ko ya fara zuwa tambayo ko wace ce sannan? Daga baya dai ya bude ta shige.

Gidan fess Kamar goge tsakar gidan ake tsabar tsafta, motoci ta gani guda uku, ta gane ta little a ciki, dan haka hamdala ta yi, ta nufi wata mace tana tsugunne tana kwashe shara, daga gefe,

"Barka da rana"

Dagawa matar ta yi ta kalle ta, sannan ta ce,

"Barka dai, wajen wa ki ka zo"

"Na zo wajen masu gidan ne"

"To, to bari na kai ki wajen Hajiya Ammaa, duk suna can da baqi,"

Gaba matar ta yi, Hajiya Safiyyah na biye, bayan sallama da matar ta yi kamar sau biyu, kafin su ji, Maryama da ke kujerar kusa da shiga parlourn ta amsa, tare da juyawa ta kalle su, Ammaa ta musu izinin shiga Little n ganin Hajiya ya miqe tsaye, cikin mamaki ya ke kallon ta, me ta zo yi anan kuma? Ta bayan kujerar ya zagaya zai bar wajen, Hajiya ta zube a gaban shi, idanun ta na zubar da hawaye.

Baqin kuwa ba wasu bane face Lamido da Sumaye ,sai yau Allah ya nufa suka zo ganin mazaunin Maryama .

"Meye haka? Me kika zo yi nan? Wai me ya sa ba ku gane wa ne? Kar ki ce komai, na riga na fada maku, duk abinda kuka min na yafe maku, meye kuma na zuwa inda na ke, bana qaunar ganin ki a rayuwa ta,"

"Little please hear me out, ban zo dan na qulla wata alaqa da kai ko da ahalin ka ba, har abada Ni kai na ina jin kunyar sake hada ido da kai, yanzu ma da ka
Ganni gaban ka, dole ce ta sa, kai wa Allah little ka riqe mahaifin ka a matsayin uba, na sani shi din babban mai laifi ne, amma yana cikin halin quncin rashin ka, wanda hakan ke matuqar ja min matsala, yanzu haka ciwo na ya kai matuqa ta yanda zan iya samun shanye War barin jiki any time, damuwa ta min yawa Little, Dan Allah ka taimake Ni ka koma ga mahaifin....."

"Never! Ba zai yu ba, ba zan taba komawa wajen ku ba har abada, ki je ki san ya zaki ki lallaba mijin ki, ba kin san yanda zaki lallaba maza su fada tarkon ki ba?"

"Yaseer! Meye haka! Me ke damun ka ne! Kai baka yafiya ne?" Ina ji Nusrah da ta hasala da halayyar d'an nata.

"Mama dan Allah kar ki shiga maganar nan, kun kasa fahimta ta dukan ku, wai shin me ya rage a tsakanin mu? Me zan musu? Na ce na yafe wa kowa Ni, kuma na nemi yafiyar kowa, to kowa ya fita daga sabgar rayuwa ta nima, ba za ku gane abinda na ke ji a zuciya ta ba ne, ta yaya kuke tsammanin zan dauke shi a matsayin uba? Wanda musulunci ma bai ba shi wannan damar ba?  Ta yaya kuke tunanin zan ci gaba da mu'amala da su bayan abubuwan da suka faru a tsakani na da ita, da wanne ido ko matsayi zan dinga mu'amala da su?"

"Ka ba su matsayin wanda suka riqe ka"

"Maryama!"

"Ka ba su matsayin wanda suka tallafa wa rayuwar ka a baya,"

"Maryama ba zaki daina shiga maganar nan ba ko!"

"Ka ɗauke su kamar mariqan ka, wanda suka tallafawa rayuwar ka a baya, bayan haka kar ka ba su wani matsayi, Ni ma ba zan so ka koma hulda da su ba, amma ka dubi Allah, kai ma ka yafe musu, ka tausaya ma halin da ta ke ciki"

Shiru ya yi, Lamido ne ya dafa shi,

"Haba Yaseer, yau ko dan darajar riqo da ilimin da baiwar Allah nan ta baka ai zaka yafe mata ko, komai bata rawar ta da ta yi, a qalla dai tana da wani gudunmawa ta alkhairi da ta taka a rayuwar ka,kar ka kalli daya bangaren to, ka kalli bangare mai kyau da ta qunsa, ba a ce ka yi ta mu'amala da su ba, a koda yaushe, a qalla dai ko waya ne kana yi, kuna gaisawa da shi Alhajin, ko dan samun saukin ta itama, ka yi wa Allah ka manta da komai, In ba mu mantawa da baqin cikin baya, za mu yi ta ɗora ginin farin ciki ne ya qi Mana qarko"

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now