ALMAJIRI NA......PAGE 42

1.8K 138 7
                                    

Maryama wani sabon yanayi ke shigar ta, Jin soyayyar Yaseer ta ke na sauya salo a cikin ran ta, soyayya ce Mai qarfi tare da qauna, ga uwa uba girmamawa da kunya, hannun shi ya sa a hankali ya riqe na ta, zabura ta Yi, ta sake qara, saurin toshe bakin ta ya yi, suna zare ido, Daga baya Kuma suka fashe da dariya, Maryama har da Kama ciki Dan dariya,

"Hammaa Yaseer Wai Kai ma kana Jin wannan abun Mai Kama da wutar lantarki ta ja mutum, in ka taba Ni"

Shiru ya yi kan shi jingine da jikin katangar da suke, Yana kallon ta tare da murmushi, son ta na shiga kowanne lungu da saqo na jini da tsokar shi, ji ya ke jikin shi ya mutu sosai, yanzu ya Gane banbancin sha'awa ta Zina, da sha'awa ta aure, sha'awa ta Zina Kamar wuta a cikin audiga ta ke, Wanda kashe ta roqon Allah ne zai fi tasiri akai, dik wani Mai aikata Zina, in ya dage tsayin daka da roqon Allah, ya Kuma Sanya tsoron Allah, ba bu shi ba bu ita, musamman in ya gujewa abubuwan da suke Jan shi zuwa ga zinar, sha'awar aure kuwa Abu ne da ke hade da wani sinadari na hakuri, Wanda ko da mutum na da matar ko mijin ta taso mishi, ya zamana matar na jinin al'ada ko mijin ba shi da sha'awar kusantar iyalin shi, ko ba shi da halin kusantar su, zai iya hakuri har zuwa wani lokacin, ga babban misali a wajen Lattin din Yadikko .

Matsanancin son kasancewa da Maryama ne a zuciyar shi, Amma ji ya ke zai iya jira har sanda aka kammala mallaka mishi ita, hannu ta Sa ta shafi gefen fuskar shi, da sauri ta janye hannun tana yarfa shi.

Kukan shagwaba ta sa mi shi, cikin sauri ya Kama hannun nata, ta sake janyewa da sauri har da miqewa tsaye, bin bayan ta ya yi ya tsaya Yana tunani, shin ya rungume ta ko kuwa,

'kaiii inaa, Ina rungume ta zata sa ihun da wataqila har maqota sai sun leqo Jin me akai mata'

Gaban ta ya tsaya, Yana leqa fuskar ta cikin hasken farin watan,

"Maryaman Hammaa ya akayi?me kike so?"

"Ni dai bacci na ke ji, Kuma da ga yau ba zan sake taba ka ba, Kar jini na ya qare, an ce in wutar lantarki na Jan mutum jinin shi qarewa ya ke, yanzu ma sai na Sha madara kafin na kwanta,"

Little me zai Yi in ba dariya ba, wannan yarinyar Sam Bata San me duniya ta ke ciki ba, she is so innocent,

"Sai da safe, in ka Gama dariyar ta ka"

Cike da shagwaba ta Fara tafiya, ya ja mayafin ta, daidai kunnen ta ya Kai lips din shi, bata san sanda ta lumshe idanun ta ba, saboda jin wani sabon yanayin da ya tada tsigar jikin ta.

"Maryama na in kina shagwaba irin haka, zan sa maki shocking  fa"

Juyawa ta yi da sauri Dan ta kalle shi, fuskar su ta hadu waje Daya, rintse idon su suka yi, Maryama ta sake manna fuskar ta a tashi, Jin yanayin da ya shiga ne ya sa shi saurin janye fuskar shi, ya juya baya,

"Sai da safe Maryama, maza ki kwanta da wuri Kar mu rasa sallar asuba akan lokaci ko?"

Kasa amsa mishi ta yi, wannan shocking din ya fi kowanne shigar ta, qafar ta ta Mata nauyi, haka ta ja jikin ta zuwa dakin su, ta tarar Sumaye ta Mata shimfida, Dan haka kwantawa ta yi, ta na taba fuskar ta, da ta ke ji Kamar an Kara a garwashi Dan dumi, wannan sabon lamari ne a tare da ita, tunda ta ke bayan Lamido ba ta taba taba wani namiji ba (ke fa?) Little ne namiji na farko da ya shiga rayuwar ta, Wanda ba muharramin ta ba, a baya Lamido ya Yi iya qoqarin shi Dan ganin ya katange su Daga aikata ba daidai ba.

Washegari  bayan sun yi sallar asuba,  little ya shirya zai tafi, saboda ya kwana da tunanin halin  da maman shi ta ke ciki, da kyar Sumaye ta dakatar da shi ta dama Masa fura da madarar da aka dafa, ta Sa mishi sugar ya shanye ya yi hamdala, tare da gode masu akan karamcin da suka mishi na bashi maryama, Lamido ne ya ce ya shiga ya tashi Maryama su Yi sallama, cikin Jin kunya ya shiga dakin, yaga bacci ta ke, murmushi ya yi, ganin yanda ta baje abun ta, ba tare da ta San wani zai shiga ya gan ta a haka ba, da ta San zai shiga da ba tai daidai da jikin ta haka ba, jakar makarantar ta ya hango a gefe, ya tashi ya dakko, takarda da biro a ciki, rubutu ya Mata kadan ya ninke ya aje Mata a gefen ta sannan ya hura Mata kiss ya fita.

ALMAJIRI NAWhere stories live. Discover now