Farka warta ke da wuya ta jiyo magana "Bari naje na dubata ai ban san ba tada lafiya ba" Muryar namiji tajiyo tayi saurin mik'ewa daga kan kujerar da take kwance ta fara k'ok'arin janyo hijab, kafin ta mik'e ta janyo hijab ta saka tuni har ya shigo ya kalle ta idanuwanta sunyi mici-mici da ganinta kasan tasha bacci, yayi tsaye a gabanta fuskarsa cike da walwala. cikin mamaki ta kalle shi, Nauman ne d'an wajen safiya(yayar mahaifinta), tayi kasak'e tana kallonsa sabida tsananin mamaki da tayi, yayin da shi kuma ya jingina da bangon d'akin tare da nad'e hannayensa a k'irji yaci gaba da kallonta. Ba komai ne ya bawa Zarah mamaki ba face tsahon shekarun da ya d'auka rabon shi daya zo gidan, sai gashi yau kuma ya bayyana, Sai da Nauman ya d'auki wasu 'yan dak'ik'u kafin yace "Zarah ya jikin" tace "jiki da sauk'i ai na warware, daga nan bata sake cewa da shi k'ala ba, ta kauda kallonta daga kansa yayin data had'a idonta da nasa ya saki wani murmushi shima ya kauda kallonsa kad'an yace "amma ai da saura, Allah ya sauwak'e ya k'ara lafiya, ni zan wuce daman Abbah ne ya aiko ni sai naji ance ba kida lafiya nace bari na shigo na duba ki Allah k'ara sauk'i" a hankali ta iya cewa da shi "Amin Yaya Nauman, ka gaida gida" Nauman yace "gida ya ji" daga nan ya wuce ya tafi yabar Zarah da tunane -tunane da zancen zuci, ta sak'a wannan ta kunce wancen daga can ta watsar da zancen da zuciyarta take sak'a mata ta mik'e ta nufi toilet dan d'auro alwalar azhar, bayan ta fito ta shinfid'a sallaya ta tada sallah. Fara sallarta keda wuya mahaifiyarta ta shigo Hajjiya Usaina tana magana "Ashe har kin tashi? na zata har yanzu baccin kike baki tashi ba" ta nemi wata sallayar ta shinfid'a itama ta tada sallah.
Can kuwa Nauman bayan ya bar gidan bai zame ko ina ba sai wajen mahaifiyarsa Safiya ya sameta zaune a tsakar gida kan tabarma tana tankad'en garin masara sai da yayi sallama sannan ya shiga, d'ago kai tayi ta kalle shi "wa alaikassalam har ka dawo ?" ya tsuguna kusa da inda take "wallahi na dawo Mama, ina abinci na?" dariya ta fara yi "wanne abinci kuma, acan baka ci ba? Shuru yayi yana sosa k'eya taci gaba da magana "ai nasan a rina kai me cewa ba kai ba cin abincin rana, jeka duba kitchen ka d'auka yana nan a jan roba" dariya yayi ya mik'e ya shiga ya d'auko abincin ya zauna nan kusa da ita ya fara ci "baka bani labarin yadda kukai ba" yana cin abincin yana magana "zan baki labari mama bari ciki na ya d'auka" Safiya tayi murmushi "ai shik-kenan gama ci d'in.
YOU ARE READING
BAK'AR GUGUWA
RomanceLittafi ne me cike da abubuwan ban mamaki, al'ajabi, cin amana, da rugujewar zumunci da dai sauran su.