Chapter 10

43 5 2
                                    

    Bata dad'e da futa ba ta shigo hannunta d'auke da ruwa a cikin wani cup jikinta na k'yarma ta mik'awa hajjiya, a hanzarce hajjiya ta karb'a ta fara yayyafawa Zarah amma har yanzu shuru babu labari dan bata ko motsa wa al'amarin daya k'ara bawa hajjiya tsoro kenan hankalinta ya k'ara tashi zuciyarta ta fara tafarfasa ji take kamar tayi kuka sai dai shi kansa kukan ma yak'i zuwar mata, ta ma rasa me zata yi, ta sake yayyafa mata ruwa nan ma bata motsa ba bare asa ran farfad'o warta, jamila da ke tsaye tana kallo Zarah da manyan idanuwanta wa 'yanda suka yi jawur kamar gauta, cikin tsananin tsoro da fargabar abinda zai je yazo yasa Jamila d'ora hannu aka ta fara rusa kuka da sauri hajjiya ta kuma cewa "k'aro wani ruwan jamila je ki k'aro yi sauri" k'arfin hali hajjiya kawai tayi har ta iya magana amma zuciyarta a raunane take sai dai bata san nuna wa sabida Jamila,wannan yasa take dakewa. Sak'e-sak'e ta fara yi cikin zuciyarta na cewar "ko dai na kira wayar abban Zarah na fad'a masa? Kai! In na fad'a masa hankalinsa zai tashi kar nasa ya tawo a gigice ayi biyu babu, innalillahi wa inna ilaihirraji'un, wai Zarah ta rasu kenan?, dan Allah Zarah kar ki mutu yanzu" da sauri ta kawar da wannan tunani yayin da ta tsurawa Zarah idanu tana ganin ikon Allah har yanzu ta kasa ganewa shin mutuwa tayi ko kuwa bata mutu ba?  Jamila ce ta shigo da ruwa me yawa a wata k'aramar roba hajjiya bata ko kula da shigowar ta ba sai ji tayi ta kwara akan Zarah tana fad'in "Dan Allah zarah ki tashi" cikin muryar kuka da tsananin tashin hankali take maganar daga nan ta fuce daga d'akin tana kuka. Ganin halin da jamila ke ciki yasa hajjiya kasa jurewa wasu kwalla masu tsananin zafi da rad'ad'i suka fara kwaran yowa kan kucinta tasa hannu ta share wasu zafafan hawayen suka sake kwaran yowa, nan take idanuwanta suka yi jawur ta kuma saka hannunta ta share fuskarta, addu'a ta fara yi cikin zuciyarta yayin data k'urawa Zarah idanu tana jiran ganin motsawarta.
    Sai da Zarah ta d'au tsahon lokaci a kwance ba tare data motsa ba, futar Jamila ke da wuya Zarah ta fara motsawa a gigice cikin murna hajjiya ta fara kwalawa jamila kira "Jamila! Jamila!! Kina ina? Maza tawo Zarah ta farka" a guje jamila ta shigo tana murna fuskarta cike da hawaye tanata faman gogewa da mayafinta wanda rolling d'in da tayi da shi tuni ya jima da warewa, jin muryar Hajjiya da Zarah tayi yasa ta bud'e idanuwanta ta kalle su cikin mamaki ganin sunyi cirko-cirko a gabanta, jikinta duk a jik'e da ruwa tayi zunbur ta mik'e kad'an ta jingina da fuskar gadon, tunaninta d'aya meya jik'a ta haka? Ta kalli jikin ta ta kalli Hajjiya, washe baki hajjiya tayi "Sannu Zarah kin tashi?" itama Jamila murna take ta matsa kusa da Zarah ta Zauna "Zarah" mamaki ne ya kama Zarah har yanzu ta kasa gane me ya faru suke ta murna haka a hankali ta kuma mik'ewa sosai ta zauna tace "lafiya momy?" ta dubi jamila "Jamila lafiaya?" Hajjiya na murmushi tace "ba komai zarah" cikin rashin fahimta zarah tace "amma kuma naga kamar kuna cikin murna?, to me ya jik'an jiki na?" jamila ce tayi caraf tace "ke ba komai wani al'amari ne ke dai tashi kije ki sallah kizo kisha labari" tab'e baki kad'an Zarah tayi tare da fad'in "hmm ai ni nayi sallah tun asubha" hajjiya ta mik'e tace "sai kizo kiyi breakfast to" Zarah tayi murmushi "sai nayi za'a ban labarin? Ko dai ya'ya ne zai dawo?" Jamila ta kuma yin caraf tace "ke dai tashi muje kici abinda zaki ci labarin ya biyo daga baya" ganin Zarah ta wats-tsake tamkar ba ita ba yasa hajjiya ta bar musu d'akin tayi waje zuciyarta cike da farin ciki da addu'ar godiya ga Allah daya sa d'iyarta farkawa. Abinda zarah har yanzu bata kula ba a fuskarsu shi ne cikin idanuwansu da suka yi jawur tamkar gauta duk da suma d'in sunk'i barin su had'a ido da ita dan kar ta fahimci abinda ya faru da ita, tashi tayi ta zauna sosai tace "kinga nifa sai na watsa ruwa tukunna zanyi breakfast sai na fi jin nutsuwa sosai, wai yaushe ma kika zo jamila da sassafe haka?" Jamila tayi dariya "yanzun ne safiya? Toh shad'aya ai ta juma da yi, ni ban dad'e da zuwa ba, yanzu dai ki tashi kije kiyi wankan ki fito ki breakfast d'in sai kizo musha labari" Zarah tayi murmushi "indai wannan ne abu ne me sauk'i yanzu zanyi na gama dan kuwa nima ina da labari in kin bani sai na baki na wajena" Jamila tace "to shik-kenan ina nan ina jiranki" tashi Zarah tayi  tsaye kafin ta d'auki towel ta shiga toilet tace "wai ni wannan ruwan daya jik'ani fa?" jamila tace "ke dai ki shiga ki fito" Zarah ta tab'e baki kad'an bari dai na fito d'in" tana shiga  jamila ta mik'e ta koma falo_____

BAK'AR GUGUWAOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz