Washe gari kuwa Safiya ce zaune a bakin gado cikin d'akinta tana nunke kayan wankin da suka bushe, Nauman ne sanye da wata sky blue d'in shadda wadda akai mata d'inkin tazarce, ya yaye labulen d'akin dake mak'ale a bakin k'ofa ya shigo ciki. Safiya na ganin d'an nata tayi murmushi tare da cewa "har ka fito kenan?ai yanzu nake zancen ka dan ina so mu tattauna da kai" kallonta yayi sosai "Ea! Mama na fito,tattaunawa kuma?" cikin sakin fuska ta ce "kwarai kuwa ina so mu tattauna ne akan maganar da muka fara da kai samu waje ka zauna" samun waje yayi ya zauna kan wata k'arama kujera dake gefen d'akin "ina jinki Mama" ta saki zanin hannunta da take k'ok'arin ninkewa "kan maganar Zarah ne duk yadda za kai ina so kai k'ok'ari ka shawo kanta kaji abinda nace maka ko? dan hausawa na cewa da biki a garin wasu gwara a garinku a garin naku ma cikin gidan ku dan haka da ace wani ya aureta gwara kai ka samu ka aure ta dan kun fi dacewa da juna in har ka aureta shik-kennan burin mu ya gama cika dan kafi kusanci da ita akan kowa " wani irin kallo yayi sannan yayi murmushi "haka ne mama na gane kuma in dai wannan ne ba zan baki kunya ba sai ta zama mallaki na" dariyar jin dad'i tayi "haka nake so" wannan shi ne abinda ta dad'e da k'udurcewa a zuciyarta kuma ita kanta tasan Nauman ba zai bata kunya ba wajen samo zuciyar yarinyar, shuru yaji tayi na d'an wasu dak'ik'u banda murmushi ba abinda take a hankali yace "bari naje idan na dawo ma k'arasa Mama?" tace "shik-kenan daman abinda naso fad'a maka kenan, in yaso daga bisani sai na samu naje wajen shi Mahaifin nata muyi maganar auren naku" ya sake sakin murmushi "zanje na k'arasa wancen aikin da nake sabida na yi musu alk'awarin nan da gobe zan gama musu gashi ban k'arasa siyo kayan aikin ba" ya mik'e Safiya ta bishi da kallo "Allah taimaka malami uban malamai ba komai sai ka dawo" dariya ya saki "Mamana mamana" har ya futa daga d'akin ta sake kwala masa kira ya dawo "ba na manta ba yau d'an uwanka zai dawo daga k'auye sai ka hanzarta dawowa" "zan dawo da wuri insha'Allahu" "sai ka dawo" sannan ya futa. Har cikin zuciyar Nauman babu soyayyar Zarah ko kad'an dan be tab'a jin yana sonta ba bema tab'a tunanin yaso ta ba, ko zuwan da yayi mahaifiyarsa ce ta bashi umarnin ya same ta su tattauna ta dalilin aiken da mahaifin zarah yayi masa ya kai kaji zuwa gidan sa, bayan da suma ya basu nasu d'anyun kajin a sannan ne mahaifiyarsa Safiya ta umarce shi da yaje ya samu Zarah idan ya kai ya fara ganinta su gana lokacin da yaje yaga ta bishi da kallo saroro kamar bata sanshi ba, sosai yaji zafi a zuciyarsa sai dai kuma be nuna hakan ko a fuska ba, sai ma yaji damuwar ya kawar masa da sauri dan a nasa tunanin har yanzu Zarah k'aramar yarinya ce, be tab'a tsammanin Zarah ta girma ba dan ya dad'e rabonsa da yaje gidan lokacin da idanuwansa sukayi arba da ita a san nan ne yaji sonta ya cake masa zuciya take yaji tasa zuciyar tayi na'am da ita, jin magan-ganun mahaifiyarsa ya k'ara bashi kwarin gwiwar k'ara sonta hak'ik'a Zarah yarinya ce irin macen da duk wani d'a namijin daya ganta sai yaji ta mamaye masa zuciya cikin sauri.
Zarah fara ce kyakkyawa kamar ita tayi kanta tana da dogon hanci siriri irin na fulani sai manyan idanuwanta wa 'yanda suka dad'a fito da kyawun fuskarta, gashin girarta me yawa a kwance, bakinta dai-dai misali, fuskarta 'yar k'arama ita ba doguwa ba, ba zagayayyiya ba , dogon wuya gareta , gashin kanta har gadon bayanta, jikinta dai-dai misali ba tada jiki kuma ba za'a kirata siririya ba, mai matsakaicin tsayi, tana da yawan murmushi kallonta gwanin ban sha'awa hak'ik'a wanda ya same ta ba k'aramin dace yayi ba yayi babbar sa'a dan tana da ilimin addini dana zamani duk da cewa bata ci gaba da karatun boko ba bayan secondary data gama tana da matuk'ar k'ok'ari, tun tana Yarinya k'arama ajin farko ita take zuwa ta d'aya har kawo girmanta bata tab'a fad'uwa ba ko kuma wani ya wuce ta. Tafiya yake yana tunanin Zarah saura kad'an mota ta bege shi yaji an janyo shi da sauri_____________

YOU ARE READING
BAK'AR GUGUWA
RomanceLittafi ne me cike da abubuwan ban mamaki, al'ajabi, cin amana, da rugujewar zumunci da dai sauran su.