Chapter 9

30 5 0
                                    

    Jamila ce k'awar Zarah sanye da doguwar riga irin d'inkin zamani blue, sai wani k'aramin mayafi pink color wanda tayi rolling da shi, a hankali ta shigo falon fuskarta cike da walwala yayin da Hajjiya Usaina ke tsaye dab da bakin k'ofar d'akin Zarah tana jiran ganin me shigowa, k'arasowa kusa da inda Haj.usaina ke tsaye tayi, Hajjiya na ganinta ta saki fuskarta "ashe! kece  na zaci wata bak'uwar ce" a ladabce Jamila ta durk'usa k'asa ta gaida Hajjiya "Ina kwana Mummy?" amsawa Haj.usaina tayi tare da cewa "ya Mamar taki, fatan tana lafiya?" kanta a k'asa tace "lafiya lau tace ma na gaishe ki, ya jikin Zarah?" fuskarta a sake Haj.Usaina ta bata amsa "jiki yayi sauk'i ta warware" Jamila na fara'a tace  "Alhamdulillah Allah ya k'ara sauk'i, tana ciki ne?" "Ea! Tana ciki" bayan da tayi mata nuni da d'akin dai-dai lokacin da Jamila ta mik'e tana k'ok'arin k'arasawa wajen Zarah, hajjiya ta kuma cewa "k'awar taki ba ta tashi ba yanzu nake shirin taso ta sai naji sallamarki, ko jikin nata ne? Allah masani, dan naga bata saba kaiwa irin wannan lokacin tana bacci ba,yanzu k'arfe goma har da arba'in shuru bata tashi ba, Jamila tace "bari na taso ta Mummy, Allah yasa ba jikin bane" "toh Amin" daga nan Hajjiya ta wuce ta nufi kitchen" ita kuwa Jamila kai tsaye d'akin Zarah  ta wuce, k'ofar d'akin ta gani a rufe sai da ta fara Knocking taji shuru ba'a bud'e k'ofar ba sannan ta saka kai ta shiga tana shiga ta tarar da Zarah kwance tayi kane-kane akan gado tab'e baki kad'an Jamila tayi tare da cewa "Uhm kaga manya har yanzu baccin ne ba'a tashi ba? lallai bacci yayi dad'i", janye bargon data rufe k'afarta da shi ta fara yi sannan ta k'arasa kusa da inda take kwance ta kalle ta sosai taga alamar baccin nata yayi nisa tunda gashi har ta shigo amma bata san ma ta shigo ba, tak'i ta tashi duk maganar da take shuru tak'i motsawa, kai mata duka kad'an tayi a bayanta "Sarkin bacci ai sai ki tashi tunda gani nazo, wannan bacci haka kamar gari be waye ba" duk abin nan da Jamila take har yanzu Zarah bata motsaba, tsayawa tayi chak! Tana kallon ta "wannan wanne irin bacci ne haka babu alamar motsawa?" zuciyarta ce take sak'a mata, take wani matsannacin tsoro ya fara ziyartar zuciyarta gabanta ya fara fad'uwa yana bugawa da sauri-sauri a gigice tace Innalillahi wa innah ilaihirraji'un a guje ta fito wajen Hajjiya wadda ke k'ok'arin bud'e fridge, ganin yadda Jamila ta fito a firgice yasa Hajjiya Usaina ta saki murfin fridge d'in data ruk'e da sauri ta maida kallonta ga Jamila "lafiya, kika fito a razane?"   cikin d'imaucewa da sanyin jiki gami da rawar murya jamila tace "Mo..Mo..Momy tak'i tashi na tashe ta tak'i tashi" nan take fuskar Hajjiya Usaina ta canja ta taho a hanzarce "muje ciki" suka d'unguma suka koma d'akin Zarah. Yadda Jamila ta bar Zarah har yanzu a haka take bata ko motsa ba, Haj.usaina ta matsa kusa da Zarah ta d'aga hannunta ta mayar ta ajjiye ta kuma tashinta "ke Zarah wannan wanne irin bacci ne haka? Ki tashi mana" har yanzun ma shuru bata san ma sunaiba wai kunu a wani gida, Haj.usaina itama tsoro ya fara kamata suka kalli juna da Jamila nan take sak'e-sak'e ya fara zuwar mata  zuciya na cewar "meya samu yarinyar nan? Kodai suma tayi ne? Ko kuma ta mutu? yanzu in aka ce mun zarah ta rasu ya zanyi? Tabbas zan shiga halin damuwa sai dai dole na barwa Allah komai tunda daman shi ya bani ita, kai...! Ina! bama mutuwa tayi ba" da sauri ta kawar da wannan tunanin da take akanta ta kalli Jamila dake tsaye "D'ebo ruwa ki kawo" jikin Jamila na rawa ta futa a guje__________

BAK'AR GUGUWATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon