Gaban Zarah ne ya yanke ya fad'i raas!ya runk'a bugawa da sauri-sauri ji kake wani dum-dum-dum! kan kace me tuni fuskar Zarah har ta sauya sai kace wadda aka kama da wani gagarumin laifi idanuwanta sunyi zuru -zuru kamar mara gaskiya, tayi k'asa da kanta kamar bata ji me ake cewa ba, mamaki duk ya kama Hajjiya Usaina, dole hajjiya tayi mamaki tunda kuwa tasan d'iyarta ba zance take futa ba, sai kuma gashi an aiko kiranta musamman yadda taga Zarah ta sha kwalliya take zuciyarta ta fara raya mata cewar "ko dai Zarah daman tasan da zuwansa? Ba mamaki ta sani idan har bata sani ba taya zata yi wannan kwalliyar?hmm... Yaran zamani kenan"hajjiya ta fad'a a zuciyarta jiyo muryar yaron tayi yana ta magana "Me za'a ce masa?" "kace tana zuwa" Da sauri Zarah ta d'ago kanta ta kalli Hajjiya dan ta bata mamaki bata tab'a tsammanin Mummy zata ce haka ba,ta kuma yin k'asa da kanta hajiya ta kalle ta tace "ba kiranki ake ba ki tashi kije mana" shuru zarah tayi sai da Hajjiya ta sake magana da k'arfi "Kin wani sun kuyar da kai kamar me d'aukar darasi sai kace ba da ke nake ba kwalliyar da kikai dan wa kika yi? Daman ai dan shi kika yi sai ki tashi kije " d'ago kai zarah tayi da sauri "wallahi mummy ni ban san da zuwan ko..... " bata bari ta k'arasa maganar da zata yi ba hajjiya usaina ta dakatar da ita "kinga ya isa haka ni dai ki tashi kije ba k'arin baya ni na nema ba ko da d'in ma da nake hana ki ai sabida karatun ki ne kuma yanzu kin gama saura karataun gaba kya yi a gidan mijin ki, ki wuce kije" kunya ce ta lullub'e Zarah kamar wata sabuwar amarya ta kasa mik'ewa sai da kyar ta mik'e ta shiga d'aki ta d'auko hijab har k'asa ta saka sannan ta fito, abunka da farin shiga a hankali ta wuce tana kallon k'asa har ta futa, duk abun nan da take Hajjiya Usaina na kallonta ta gefen ido tana dariya cikin zuciyarta sabida tasan dole taji kunya tunda ba tab'a barinta zance akai ba.
Kafin ta k'arasa waje ta fara sak'e-sak'en abinda zata ce da shi dan ita kanta bata san ma me zata ce da wanda yazo wajen nata ba, a haka ta futa ta tsaya a gate d'in gidan bata ga kowa ba, tsayuwarta keda wuya ta hango wani d'an farin saurayi, mai matsakaicin kyau tsayin sa dai-dai misali sanye da wata shadda wanda akayi mata d'inkin zamani daga nesa tamkar ba d'inkawa akai ba kai kace a haka aka siye su, rigar iya gwiwa ce me k'aramin hannu kamar 'yar shara milk color sai kuma dogon wando coffee color hular ma kalarta daban golden wadda tasha zane irin na kayan da rigar da wandon da hular duk zanensu iri d'aya ne kala ne ya ban-banta, da gani dai kamar combination ne. shigarsa tayi kyau sosai sai dai ita tunda take bata tab'a ganin irin wannan kalar shigar ba ta sake kallonsa sama da k'asa yayin da yake k'arasowa kusa da inda take tsaye hannunsa sanye da bak'in agogo, mamaki ne ya cika Zuciyarta nan take kalaman Najib na baya suka dawo mata cikin kunne inda yace mata "karki damu da rashin ganina zaki ganni nan bada dad'ewa ba amma lokacin da zaki ganni ba zaki san nine ba tabbas zan zo har inda kike" murmushi kawai tayi yayin da tazo dai-dai nan a tunaninta shi kuwa saurayin tuni ya k'araso inda take ganin tana murmushi ya sashi mayar mata da nasa murmushin tare da fad'in "barka da fitowa fatan kin fito lafiya ba tare da gajiya ba" sai da ta d'anyi shuru na wasu 'yan dak'ik'u sannan tace "lafiya lau sai dai ban gane ka ba, ko zaka iya fad'an meya kawo ka wajena?" murmushi ya k'ara yi sannan yace "haba Zarah babu abinda zai kawo ni wajenki wanda ya wuce so da k'auna" har yanzu ita dai ta kasa tantance muryarsa ji take anya ba Najib bane yake son yi mata b'adda kamanni? Sai dai kuma muryar kamar ba ta Najib ba babu mamaki ko dan a waya ne yasa ta ban-banta da ta fili? haka zuciyarta ta shiga raya mata magana yaci gaba da yi "biki ce komai ba gimbiya Zarah" ta kuma kallonsa yayin data dad'a wani tunanin sabida shi kansa sunan Gimbiya Zarah Najib wataran yana fad'a mata shi, dai-dai lokacin ta kuma cewa "Dan Allah ka fad'an kai waye? kasan dai babu yadda za'ai na soka ba tare da na san ka ba ko?" Ya dad'a gyara tsayuwarsa "haka ne zaki sanni sai a hankali kafin ki san sunana ki fara amincewa da soyayyar da nake miki mana" "ka tab'a jin anso mutumin da ba'a san sunansa ba? Koma an tab'a to banda ni dan ni ba zan so wanda ban san sunansa ba" suna cikin hira ta hango motar Mahaifinta da sauri tace "kaga sai an jima karka janyo Abbah yayi mun fad'a " daga nan ta wuce ta koma ciki shi kuma ganin hakan yasa ya juya ya futa. Tana shiga falo ta tarar da Hajjiya zaune tana kallon TV kai tsaye ta wuce d'akinta bayan mahaifiyar ta ta tambaye ta, "wa nene yazo wajen naki?" a hankali tace "wani ne"daga nan tayi wuce warta d'aki tana shiga wayarta tayi k'ara_______________

YOU ARE READING
BAK'AR GUGUWA
RomanceLittafi ne me cike da abubuwan ban mamaki, al'ajabi, cin amana, da rugujewar zumunci da dai sauran su.