Chapter 11

45 5 0
                                    

    Bata wani b'ata lokaci ba wajen yin wankan ta fito, tana fitowa taga d'akin babu kowa, sakin baki tayi hannunta ruk'e da k'ofar toilet d'in ganin Jamila bata nan ta b'ata rai kad'an fuskarta cike da damuwa tunanin ta d'aya jamila tayi haka ne dan ta gudu shiyasa ta damu data shiga wankan, ta jinjina kai yayin data saki k'ofar toilet d'in ta k'arasa dai-dai inda wani k'aramin towel yake a sak'ale cikin d'akin ta d'auko don tsantsane jikinta tana gama tsane ruwan jikinta ta nufi gaban dressing  mirror ta d'auko body spray ta fara feshe jikinta da shi sannan ta zauna kan kujerar da take gaban madubin ta fara shafe jikinta da mayuka masu k'amshi da wasu body spray d'in masu launin k'amshin furanni daga nan kuma ta fara makeup tamkar wata amarya sai da ta d'an d'auki lokaci kafin ta gama sabida kayan makeup d'in da tayi amfani da su suna da yawa sannan ta nufi wardrobe ta duba kayan da suka dace da jikinta wanda suka fi kwanta mata a rai ta saka. Ga duk wanda ya ganta ba zai tab'a cewa itace Zaran da aka sha fama kanta yanzu ba, sai da ta gama shiryawa tsaf sannan ta nufi falo nan ta tarar da Jamila zaune tana kallon wani film me suna "Yankan Zance" ta saki murmushi ganin jamila bata tafi ba dan bata yi tsammanin tana nan ba, a hankali ta k'arasa inda jamila ke zaune kan k'aramar kujera magana ta fara yi dan ta lura hankalin jamila duk ya tattara kan TV'n da take kallah "sarkin kallo ana ta sana'ar ko?" juyowa jamila tayi ta dubeta "Zarah ba dai manyance ba sai kace wata babba yanzu ma na fara kallon 'yar rainin hankali" tana fad'a tana kallon Zarah, ta tsura mata idanu kamar yau ta fara ganinta sai da ta kalle ta tun daga sama har k'asa sannan tace "uhmm.. Hajjiyata kinyi kyau fa kamar a sace" dariya Zarah tayi "da gaske nayi kyau?" cikin zolaya Jamila tace "toh baki kyau ba 'yar rainin hankali ai kema kinsan kinyi kyau d'in ne kamar ba ke ba, haka daman kika iya kwalliya Zarah?" ta jinjina kai Zarah ta kyalkyale da dariya "bana son wulak'anci in bata yi ba kawai kice mun bata yi ba wannan ai wayo ne" jamila tace "ke wallahi kinyi kyau naga baki tab'a irin wannan kwalliyar ba, dan nasan halinki kina da kayan kwalliyar sababbi ma in nace kiyi cewa kike ba zai miki kyau ba yanzu kuma naga kinyi baki munin da kike tunanin zaki ba" samun waje Zarah tayi ta zauna tana dariya "cewa nayi bari na gwada irin wadda naga ana yiwa amare tun sanda na cewa abbah ya siyo mun ya siyo mun ban tab'a gwada wa ba, shi yasa nace bari dai yau nima na gwada ko zan iya tunda yanzu dai kwalliya ita take ci in ka iya ka huta" sakin baki jamila kawai tayi tana kallon zarah tana bayani tamkar ba ita ba sharp d'in bakinta ya k'ara fitowa sosai idanuwanta sun dad'a canjawa, Zarah ta b'ata rai kad'an cikin raha tace "ke wai meye? kin wani tsuramin ido, bana son wulak'anci kamar baki tab'a ganina ba" ajjiyar zuciya Jamila tayi kad'an tare da dariya "tsabar had'uwar da kika yi ne wai kin zata wasa nake? Allah wallahi tayi miki kyau kamar ba ke ba in kuma aje a tambayi Mommy ne toh sai muje kyafi yarda dan nasan mommy da wuya ta iya ganeki" ta tuntsire da dariya, Zarah na harararta tace "ni dai a kyale yanzu dai bani labari" jamila ta kuma dubanta tana dariya "ai dole kice a kyale ni nama san dan wa kikai" tayi mata gwalo, Zarah ta harareta kad'an "Dan wa nayi? Fad'a mun" jamila ta kuma dariya "ni dai na san ko dan wa kika yi, yanzu ki fara samu kiyi breakfast  d'in da baki yi ba" Zarah tace "kyale zanyi ba dai na fito ba fara bani labarin da kuma na yanzu da kika d'auko dan wa nayi kwalliyar?" duk wannan abun da jamila take so take ta mantar da Zarah kan labarin da take son ji amma sai gashi Zarah bata manta da zancen ba, a hankali jamila ta kuma cewa "ki fara zuwa kici abincin kin san rashin cin abincin safe shi yake kawo Ulcer ki raba kanki da zama baki karya da wuri ba dan gujewa Ulcer dan ba tada dad'in sha'ani kana ji kana gani a hanaka cin abu me mai sai lallai manja yanda na tsani manja in ba a alala ba ko miyar ganye" Dariya Zarah tayi tare da fad'in "yayi likita bokan turai when did you become a doctor ban sani ba?" dariya jamila tayi "Bana son wulak'anci, Why are you making jest of me,just for the fact I said? This is known to all." Zarah tace "Naji yanzu dai muje dining ki taya ni ci" harararta jamila tayi kad'an sanan suka tashi suka k'arasa area dining wanda tuni hajjiya ta gama shirya musu shi tun kan jamila ta fito falo, sai a sannan Zarah ta kula da idon Jamila da yayi jawur cikin mamaki Zarah ta tambayi Jamila "meya samu idon ki yayi jaa?" kauda idonta jamila tayi tace "dazu ne ina tafiya naji wani abu ya fad'an ido dana zo sai na wanke idon har yanzu be washe ba kenan?" Zarah tace "ayyah sannu naga yayi jaa, mu ci ki bani labarin dan ina sane da shi ban manta ba"___________

BAK'AR GUGUWAHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin