Chapter 6

45 6 0
                                    

    A wannan dare Zarah bata iya runtsawa ba sabida yawan tunanin Najib da ya addabi zuciyar ta wanda shi ne sanadiyar kasa yin baccin na ta, sai da ta shafe tsawon wasu awanni tana jiran bacci ya d'auke ta amma ina! Sam babu shi babu alamarsa, ala dole ta mik'e ta nufi toilet dan d'auro alwala haka ta shiga ta fito ta sallaci nafila raka'a biyu dan neman mafita wurin ubangiji. Hak'ik'a Zarah tayi nisa cikin soyayyar Najib irin wanda ba zata iya musulta shi ba, duk da cewa bata tab'a ganin fuskarsa ba amma zuciyarta ta amince da shi d'ari bisa d'ari a matsayin mijin da zai zama uban 'ya'yanta,  sai dai kuma a yanzu ya ruga daya b'ata mata rai duk da cewa babu yadda zatayi ta iya cire son da take masa daga cikin zuciyarta ko a d'azu ma daurewa tayi da har ta iya fad'a masa muna nan kalamai babban abinda yafi k'ona mata zuciya be wuce na k'in fad'a mata gaskiya da yayi ba tunaninta d'aya shi ne akan me Najib zai k'i yarda da ita ya runk'a zarginta alhalin ita ta yarda da shi ta amince masa, me yasa yake son gwada ta? Wannan kad'ai yafi zuwar mata zuciya ji take tamkar Najib bai yarda da ita bane wata zuciyar kuma takance mata anya ba kuma abokinsa bane suka had'a baki da shi dan ayi mata haka? da sauri take kawar da wannan tunani, ko tayi k'ok'arin kawar da tunanin da take akansa sai taji ta kasa, haka dai ta kasance a wannan dare, tashi tayi tsam dan canja kayan jikinta ta saka na bacci sannan ta kashe fitalar d'akin ta hau gado ta kwanta tayi addu'o'inta wanda ta saba a duk sa'ar da zata kwanta bacci sannan ta tofe jikinta gaba d'aya , duk da rufe idon da tayi baccin be zo mata ba sai ma hoton abinda ya faru da yamma take gani da kuma wayar da suka yi da Najib sune kad'ai suke dawo mata idanuwanta.
   B'angaren Najib kuwa tun lokacin da ya kira Zarah bata d'aga ba ya shiga damuwa da tunani halin da zai shiga muddin ya rasa Zarah, bak'in cikinsa d'aya be wuce k'in d'aga wayarsa da tayi ba dan shi ji yake daya rasa wayarta gwara ya rasa komai nasa sabida tsananin son da yake mata baya tab'a son yaga ranta ya b'aci,sai kuma gashi yau ta jefe shi da zafafan kalaman wa 'yanda bata tab'a furta masa irin su ba, me yasa Zarah zata kashe wayarta ba zata tsaya ta saurare shi ba?. Zuciyarsa ce take raya masa haka,  take wasu kwalla masu zafi da rad'ad'i suka gangaro daga cikin idanuwan sa zuwa kan kuncinsa yasa hannu ya share tabbas in ya rasa Zarah ji yake zai iya rasa kansa gaba d'aya babu abinda be sak'a cikin zuciyarsa ba amma be samu amsar da yake son samu ba takaici da bak'in ciki ne ya kama shi ji yake zuciyarsa tana masifaffen zafi, ya saki ajjiyar zuciya mai k'arfi yayin da yake dukan kansa da hannunsa ji yayi duk duniyar tayi masa zafi babu wani dad'i a cikinta babban farin cikinsa bai wuce ace yau Zarah tana cikin walwala da farin ciki ba. Yana cikin wannan hali Ameer ya shigo hannunsa ruk'e da littattafai,  ya tarar da Najib zaune cikin tagumi ya had'a kai da gwiwa tamkar wanda akaiwa mutuwa, k'arasawa yayi kusa da inda yake ganin halin da yake ciki a hankali ya dafa kafad'arsa cikin mamaki yace "Lafiya kayi tagumi haka, meya faru? Kasa cewa komai Najib yayi sai da Ameer ya maimaita sau uku sannan Najib ya samu damar yin magana tare da kallon Ameer d'in "Ina cikin damuwa Ameer ban san ya zanyi ba ka fad'an mafita dan Allah" samun waje yayi ya zauna kusa da Najib d'in sannan yace "wai meya faru? Kayi mun bayani mana menene?" a hankali Najib yake maganar kamar me ciwon baki yana yi yana tsayawa "Tak'i d'aga wayata tak'i ta saurare ni, ya take so nayi? Nayi mata bayani amma bata sauare ni ba" duk bayanin da Najib yake Ameer sam! Be fahimce shi ba ya k'ura masa idanu "ka tsaya kayi mun bayanin komai ni ba gane me kake cewa nake ba" "akwai
matsala babba" cikin mamaki Ameer ya sake kallonsa "Matsala kuma? wacce irin matsala,meya faru?" a sanyaye Najib ya runk'a magana "Zarah tak'i d'aga wayata" guntun tsaki Ameer ya saki "shurme kawai wallahi ni na zata ma wani babban abune ya faru ashe wannan zancen zaka fad'an inda sabo ai kun saba sai ka jira ta sakko tukunna kwayi wayar" Ameer ya mik'e daga kusa da Najib ya ajjiye littattafan hannunsa gefe guda yayin da zai fad'a kan katifar dake k'aramin d'akin   ya kwanta. Tunda ya fara maganar Najib ya bishi da wani irin kallo na takaici haushin magan-ganun Ameer d'in yaji cikin b'acin rai ya kalle shi "haka ma zaka ce? ba zaka iya bani shawara ba ko? Hmmm..." Dariya Ameer yayi yace "toh ni me zance? Shifa wannan al'amari naku inda sabo kun saba duk cikin so ne" ganin yadda Najib ya d'aure fuska babu ko walwala yasa Ameer Saurin cewa "yanzu dai fad'a mun meya faru?" ran Najib a b'ace ya kau da kai daga kallon Ameer tare da fad'in "Ba sai ka ji ba"  Ameer ya kuma dariya "haba Abokina ka fad'an mana meya faru? kasan dai ba kada abokin daya kamata ka fad'awa damuwarka sama da ni ko?" a fusace Najib yayi magana "sanin hakan da kayi yasa ina fad'a maka kake watsi da maganar ya zamar maka abin dariya?" daina dariyar Ameer yayi yace "Sorry to fad'an ni ai na zata irin wanda kuka saba ne tunda nasan hali" nan dai Najib ya kwashe labari baki d'aya ya sanar da Ameer shuru Ameer yayi har sai da ya gama zayyane masa komai sannan yayi ajjiyar zuciya "ttabbas dole ka shiga damuwa sai dai ni abinda zance kayi hak'uri domin laifi dai naka ne koma menene kaine ka jawo tun kwanaki na fad'a maka kaje ka sameta ta ganka kak'i, ban tab'a jin irin wannan soyayyar ba ace tsawon shekaru ana yi amma ita bata tab'a ganinka ba kai ka ganta ka kuma santa dole ne hakan ya kasance da ace tun farko ka bayyana mata kanka da hakan be faru ba" kasak'e Najib yayi yana sauraran abokin nasa yaci gaba da magana "shawarar da zan iya baka matsayina na abokinka kuma hanya mafi sauk'i shi ne kaje ka same ta kayi mata bayanin komai dan ta fahimceka in har ka yarda da abinda na fad'a maka wannan itace hanya mafi sauk'i ni a ganina" ajjiyar zuciya Najib ya saki me k'arfi sannan ya kalli abokin nasa "haka ne ni kaina nayi wannan tunanin sai dai kuma gani nake zuwan ma a yanzu zai iya kawo wata maysalar tunda na fad'a maka tak'i tsayawa ta saurare ni bare kuma in naje ta fito har mu tattauna ta fahimce ni ina ganin gwara na bari nan da kwanaki naje " gyad'a kai Ameer yayi "koma mene ni dai shawara na baka matsayina na aminin ka" ya mik'e daga kan katifar daya kwanta "wai ni akwai abinci ne ma yunwa nake ji wallahi" ya fara dube-dube a d'akin ba tare da Najib yace masa komai ba, yana cikin dube dube ya janyo wata k'aramar kular abinci wadda aka ajjiye ta daga can gefe wajen kusurwa sai plate da aka kifa akai nan ya janyo ya bud'e yaga gurasa ce da miya ya zuba ya fara ci yabar Najib da tunani yana ci yana magana "Gwara ka gaggauta zuwa wajenta ko ka samu ka lallab'a ta ta daina damuwa rashin d'aukar wayar masoyi ai babbar matsala ce muddin matsalar hakan babba ce . Mik'ewa Najib yayi ya fuce daga d'akin Ameer ya bishi da kallo "wai ina zaka ne ? kayi mun magana mana " be tsaya sauraran sa ba yayi fuce warsa._________

BAK'AR GUGUWAWhere stories live. Discover now