Chapter 23

21 4 0
                                    

*B̆ĂK̆'ĂR̆🤦🏻‍♀ĞŬĞŬW̆Ă*
🧶🧶🧶🧶🧶
       🧶🧶🧶🧶
   🧶🧶🧶
           🧶🧶
             🧶

S⃠t̾o̾r̾y̾ & W⃠r̾i̾t̾t̾e̾n̾
         *ცყ:✍🏻*
R⃠αвí'αt ѕвѕ
         *(ცıɠ ɠąι)*

*©-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
(wє ѧяє ṭһє ɞєśṭ ѧṃȏṅɢ ѧʟʟ wяıṭєяś)📚
https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/

_ғaтan alĸнaιrι ga мaĸaran wannan lιттaғι ιna ganιn ѕaĸ'onnιn ĸυ nagode._
*_ѕannυ da ĸ'oĸ'arιn poѕтιng ѧтĸ_*
_нaѕѕan тanĸo_

*fαδῖlα αlῖϒῠ ϻῠsα (ϻα δῖlαlα ) αshα kαrαtῠ lαfῖϒα ❤*


*P⃠age➡23*


     Da sauri Hajjiya ta mik'e ta fita sabida jiyo muryar yaron da tayi a dab da bakin k'ofar d'akin koda ta futa sai ta ganshi a tsakiyar falo da sauri tace "wa yake kiranta?" yaro yace "inji wani a waje" sai da ta d'anyi shuru na 'yan wasu dak'ik'u kafin tace "kace tana zuwa" sannan yaron ya wuce ya futa,  komawa tayi cikin d'akin bayan da yaron ya futa tana shiga ta kalli Alhaji wanda ke zaune fuskarsa a d'aure ya had'e girar sama data k'asa babu alamar ko walwala cikinta, al'amarin da yayi matuk'ar bawa hajjiya mamaki kenan tunda kuwa kafin fitarta ba haka fuskarsa take ba, to meya janyo masa hakan? tambayar da ta yiwa zuciyarta kenan wadda ba tada amsar ta, yayin data koma can gefe guda ta samu waje ta zauna, Alhaji yayi zunbur ya mik'e tsaye kamar wanda aka sokawa allura zuciyarsa cike da takaici da damuwa banda hasala babu abinda zuciyarsa ke yi, ba komai ne ya sashi hakan ba face ganin yadda samari suke zarya wajen 'yarsa amma kuma ita ta gagara fudda gwani cikin su, wanda kuma hakan zai k'ara bawa mutanen unguwa damar fad'ar albarkacin bakin su, a hakan ma ya ake ciki? duniyar nan da ta zama abar tsoro ba'ayi ba ace anyi ina kuma ga anyi ko an gani? Musamman idan akace ka d'ara wani kana da d'an abin hannunka k'ok'arin mutum yaga ya b'ata maka suna ko dan ya samu damar yi maka dariya, a kullum burinsa be wuce na kai ka rasa abinda kake da shi ba, shi kuma ya samu koda kuwa be samu ba burinsa na yaga ka rasa ne ka zama kamar shi ko ma shi ya fika, k'agar zance da sharri a wannan duniyar ba komai bace in aka shirya wani zancen har ka mutu ba zaka wanku a idanuwan sauran jama'a ba, Alhaji Kabeer na tsaye yake ta ayyana hakan cikin zuciyarsa daga bisani kuma ya fara magana "zanje ni na duba naga kowaye idan ma shi ne yazo shik-kenan idan kuma ba shi bane ko wanene yazo to yazo a sa'a domin kuwa shi zan baki tunda ke ba zaki iya fudda wanda kike so cikin su ba" da sauri Zarah ta fidda manyan idanuwanta ta kalli mahaifinta gabanta nata fad'uwa k'irjinta kamar ya fashe, itama Hajjiya da ke gefe guda tana kallon Alhaji fuskarta ce tayi saurin sauyawa cike da mamakin abinda Alhajin yake fad'a, kasa jure hakan tayi dan bata son abinda zai tab'a Zarah bata son ganin damuwarta duk da cewa tasan Zarah ce ta jawo koma mene tunda kuwa ya bata dama har tsawon sati guda, amma bata yi amfani da wannan damar ba sai dai ba zata iya bari a yanke wannan d'anyen hukuncin ba domin kuwa yayi tsauri da yawa tunda ba wani zai zauna mata da mijin ba ita zata zauna da shi, zancen da zuciyarta take ta sak'a mata kenan da sauri Hajjiya tace da shi "A'a! Alhaji kada kayi haka" kamar bamu muka haifeta ba" sai a lokacin Zarah ta samu salama cikin zuciyarta musamman yadda taga mahaifiyarta na k'ok'arin goya mata baya taja ajjiyar zuciya kad'an yayin da Hajjiya take ci gaba da magana "Me zai hana a bata wata damar? Tunda wannan itace dama ta farko idan har aka kuma bata wata bata kawo ba sai a zab'a mata kowane kum.... " tun bata k'arasa maganar da take k'ok'arin furtawa ba, cikin fushi Alhaji Kabeer ya katseta da cewa "Kinga dakata! da Allah duk na lura ke kike sata tayi duk abinda take yi tun lokacin dana saki ki tambayeta kika k'i tambayarta ba mamaki shima yaron da kuke magana babu shi kece kawai kika tsara hakan sabida gudun b'acin ranta ko? Shiyasa dana tambayeki sana'arsa da inda yake kika kasa sanar da ni sabida babu shi, bana son a mayar mun da gida kamar kasuwa wannan yazo ya tafi wancen yazo ya tafi kamar gidan bariki" fuskar Hajjiya dana Zarah cike da mamaki suke kallon Alhaji da sauri Zarah tayi k'asa da kanta wasu hawaye masu tsananin zafi da rad'ad'i suka sake ci gaba da sakkowa kan kuncinta, tama rasa me yake mata dad'i babu wanda ya jawo mata hakan face Najib dan inda be kashe wayarsa ba da duk hakan bata faru ba dan haka laifinsa kawai take gani, Najib ka cuceni duk halin da zan shiga anan gaba kaine sila, ta fad'a cikin zuciyarta yayin da shash-shek'ar kukanta yake bayyana. Hajjiya ta bud'e baki zata yi magana kenan Alhaji ya kuma dakatar da ita "karki kuma cewa komai" sannan ya maida kallonsa ga Zarah wadda ke ci gaba da sharb'ar kuka wanda sautin kukan yake bayyana ga iyayenta yace "zaki iya zuwa kiga ko waye amma ki sani cewa wannan itace rana ta k'arshe dana baki damar ta ba zan sake baki wata damar ba. A wannan dare zan zab'a miki mijin da zaki aura muddin kuwa babu shi, dan haka kije ki dawo ina jiranki" da sauri Zarah ta kuma d'ago fuskarta data cika da hawaye ta kalli mahaifinta da runannun idanuwanta kallo d'aya zaka yiwa Zarah kasan tabbas tana cikin tsananin damuwa, kasa motsawa tayi daga inda take zaune dan tasan koda taje wajen me kiran nata ba Najib bane, ba zai wuce Sagir ko Nauman ba wanda a yanzu ya fara shiga rayuwarta yake neman dagulamata tunani, dama ace Najib ne data futa sai dai tasan babu yadda za'ayi Najib yazo, mutumin da wayarsa take kulle ina shi ina zuwa? Maganar da take ta yawo cikin zuciyarta kenan dai-dai lokacin da Alhaji ya kuma cewa "idan kuma ba kida niyyar zuwa to ni zanje amma ki sani muddin na fita kowanene yazo wajenki na fad'a miki shi zan baki tunda ke kinfi son hakan" da sauri Zarah ta sake duban mahaifin nata wasu kwalla masu zafi da rad'ad'i suka sake saukkowa kan kuncinta, tunaninta d'aya da kuma addu'ar da take cikin zuciyarta be wuce na kar Allah yasa Nauman ne, gwara ace wani ne daban amma ba shi ba, idan Nauman ne bata san ya zata yi ba, taja ajjiyar zuciya ta kuma cewa idan kuma Sagir ne fa ya zan yi? koda yake ai gwara Sagir sau dubu akan wani Nauman, ta share kwallar da take shirin saukowa kan kuncinta sai dai kuma har yanzu bata motsa daga inda take ba ji take kamar ta had'iyi zuciya ta mutu sabida tsananin takaici da damuwa, banda bin mahaifinta da kallo babu abinda take yi, fuskar Hajjiya Usaina cike da tausayin Zarah tayi k'asa da idonta dan ba tada damar cewa komai kamar tace da Zarah tayi sauri ta mik'e taje gudun kada a zab'a mata wanda bata k'auna amma ina! Tana tsoron kada Alhaji ya sake dakatar da ita wannan yasa ta kasa cewa komai sai bin Zarah da kallo kawai da take. To wai me ma zanje nayi, gurun wa zanje? Gwara na barwa Allah komai na hak'ura da Najib d'in Allah ya zab'an mafi alkhairi, tunda shi Najib d'in gashi yana so ya sani cikin matsala, me kuma zaisa naci gaba da sauraran jiransa? Koda yake duk ni naja koma mene da ban masa haka ba da shima be mun hakan ba ta runk'a fad'a cikin zuciyarta tana ci gaba da kuka ganin ba tada niyyar tashi yasa Alhaji tafiya da kansa dan ganin wanda yazo wajen Zarah yana zuwa dab da bakin k'ofar d'akin ya ji Hajjiya Usaina ta kwarma uban ihu.__________



*KUYI HAQURI DA WANANNAN BA YAWA, IN NA SAMU LOKACI ZAN CI GABAR MUKU INA GANIN SAK'ONNIN KU NA GODE👍🏻*





*💅🏻B⃠ıɠ ɠąι ¢ɛ✍🏻*

BAK'AR GUGUWAKde žijí příběhy. Začni objevovat