Chapter 5

52 6 0
                                    

   Da sauri ta kai hannu ta d'au wayar Najib ne a sanyaye ta latsa wayar ta kai kunne ranta a b'ace ta tab'e baki kad'an tace "Hello! Ka kyauta" yana dariya yace "Da me na kyauta gimbiya ta?,  zuciyarta cike da takaici tace "hmm...  Da abinda kayi mana" dariya ya kyakya ce da shi tamkar wanda akaiwa albishir "kin kasa fad'an komai sai kuma b'ata rai kike wai meya faru? Allah sa dai ba wani laifin na k"ara yi ba" ranta har yanzu a b'ace yake tace "da b'adda kamannin da kayi" cikin rashin fahimta yace "b'adda kamani a ina baby na?" mamaki ne ya k'ara kamata ganin yadda yake magana kamar be san meya aikata ba a hankali tace "wai kana nufin baka san me kayi ba? Ko kuwa kana nufin kace mun zuwan da kayi yanzu ba zan iya gane Kaine ba?" da sauri ya mik'e daga kwanciyar da yake ya dad'a gyara zamansa dan yanzu kuma be fahimci ina ta dosa ba, dan besan me take nufi ba " baby na ina naje kuma?" wani takaicin ne ya k'ara kamata "bari kaji na fad'a maka na ruga dana gama gane ko kai waye, ko kana tunanin ni irin 'yan matan nan ne masu soyayya da samari sama da d'aya ko kuwa kayi haka ne dan ka gwada soyayyar da nake maka? Kana tunanin ba dan Allah nake sonka ba sai dan abin duniya" ranta a b'ace ta runk'a fad'a masa zafafan kalamai cikin rawar murya ya runk'a yi mata magana "haba baby wai meya faru ne? Be kamata ki kama ni da laifin da ban
san na aikata ba, ya kamata ki fad'a mun abinda ya faru" "daga lokacin dana d'auki wayarka  na fara gane Kaine ba wani ba ko kana nufin kace mun ba Kaine kazo yanzu ba" mamaki ne ya k'ara kama shi "wallahi baby ba ni bane" "hmm ni na yarda da kai ashe kai baka yarda da ni ba" marairaicewa yayi "ya kamata ki fahimce ni wallahi nace miki ba ni bane" shuru tayi masa sabida ta kasa yarda da magan ganunsa zuciyarta kad'ai take saurara idan har ba shi bane taya zai kirata bayan sun rabu kuma taya zai kyalkyale da dariya? Haka taci gaba da wannan tunani kamar me shirin yin kuka ya sake magana "baby na ba zan yi miki k'arya ba rantsuwa fa nake miki " ko sauraransa bata yi ba ta jiyo hajjiyarsu na kwala mata kira ta katse wayar ta ajjiye gefe ta futa a guje, tana fitowa falo mahaifinta ta gani zaune kan d'aya daga cikin kujerun falon da suka kewaye tuni har ya shigo ta durk'usa k'asa tayi masa sannu da zuwa cikin fara'a da walwala yayin  data danne zuciyarta sabid͠a takaicin da Najib ya saka mata.  Alh. Kabir yace "yauwa ya jikin naki?" tana murmushi tace "Abbah jiki yayi sauk'i na warware " dariya Abbah yayi tare da cewa "aifa jiki yayi sauk'i ga fuska nan tasha kwalliya toh Allah k'ara lafiya" dariya duk-kaninsu suka yi sannan suka ce "Amin".  Komawa d'aki Zarah tayi ta tarrar da Missed calls har biyar text message  guda uku nan ta duba taga Najib ne takaici ya kamata ko karanta sak'on bata yi ba ta kashe wayar gaba d'aya ta zauna tunani dole ne taji haushin Najib tunda suke bata tab'a ganinsa ba yanzu kuma yazo yace ba shi ne yazo ba toh taya kalamansu ya zamo iri d'aya sunan da yake fad'a mata taya shi wannan ya sani idan har ba shi ne ba, zuciyarta ce take ta raya mata tayi zaune ta had'a kai da gwiwa ba shiri ta tashi ta nufi toilet dan d'auro alwalar magriba dan tuni magriba har tayi.
   Can kuwa Hajjiya Usaina sai da ta gama had'awa mijina nata komai a sashin sa yayi wanka yayi sallah ya samu yaci abinci sannan ta zauna kusa da shi dan tab'a hira suna cikin hira Hajjiya ta kalli mijina nata tayi dariya "akwai abinda ya faru d'azu" d'ago kansa yayi ya kalle ta sosai "ina jinki" "hmm d'azu ba ka aiko Nauman ba?" "eh! Meya faru?" hajjiya ta k'ara gyara zama "bayan da yazo yake tambaya ta Zarah ko tana nan? Nace eh ba tada lafiya sai ya shiga ya duba ta d'azu kafin ka dawo kuma ina tunanin shi ne ya dad'a dawowa,  anya babu wani abu a tsakaninsu kuwa?" Alh. Kabir ya k'ura wa matarsa idanu sannan yace "Idan har tana son shi shik-kenan zan aura mata shi muddin bata san shi ba zan mata auren dole ba dan ina son 'yata ta samu kwanciyar hankali duk da cewa mahaifiyarsa 'yar uwa tace bana son na d'auki yarinya ta na had'a ta da 'ya'yanta amma in tana sonsa haka Allah ya tsara ba tsumi babu dabara ba zan hana ba" "Hajjiya tace "Gaskiya ne Allah dai ya zab'a mata mafi alkhairi dan yadda na ganta tasha kwalliya ba mamaki tana sonnsa a tunani na sanda ya shiga duba ta k'ila anan ya fad'a mata zai dawo" "koma dai mene Allah zab'a mata miji na gari " hajjiya tace "Amin"._____________

BAK'AR GUGUWAWhere stories live. Discover now