Zarah na zaune ta kasa ko motsawa Tunanin Najib ne yake addabar ta, har Hajjiya Usaina ta k'arasa sauran ayyukan da zata yi sannan ta shigo falo ta tarar da Zarah zaune cikin tunani, kallon zarah ta fara yi sannan tayi murmushi kafin tace "ki zuba abinci kici ki sha maganin ki," A shagwance tace "Mummy bana jin yunwa sai dai ko zuwa an jima" harararta Hajjiya tayi "Da yaushe kika ci abincin da har kika k'oshi? Ko a baccin kika ci ban sani ba?" marairaicewa zarah ta sake yi kamar wata k'aramar yarinya "Allah Mummy bana jin yunwa" sake harararta Hajjiya tayi "haka kuma zaki zuba kici, in baki ci ba dame zaki sha maganin ko dan kinga kin fara samun sauk'i sai kuma ki fara wasa da shan maganin? Shi ciwo in kana so ya tafi gaba d'ayansa sai kasha magani a jere ba wai ka runk'ai masa shan wasa ba yau ka sha gobe ka barshi, kin san dai ba zaki sha tsurar magani ba tare da abinci a cikin ki ba ko?" kasak'e Zarah tayi tana sauraron Mahaifiyar tata taci gaba da cewa "ki tashi ki d'ebo ki zuba kici in kuma ni kike so na d'ebo na baki a baki kuma to, sai na tashi na d'ebo " Dariya Zarah tayi "Haba Mummy a'a yanzu zan zuba, amma ni wallahi ba yunwa nake ji ba kinsan mummy baki na har yanzu bana jin dad'insa" ta mik'e tsaye "A haka zaki tura shi kina ci a hankali yana tafiya har ki samu ki cinye zaki fi jin kwarin jikin ki dan yanzu ma duk wanda ya ganki ya san jikin ki babu kwari" murmushi zarah tayi ta wuce ta nufi inda kular abincin take ta zubo kad'an a plate ta nemi wuri ta zauna Hajjiya ta kalli abincin "yanzu wannan abinci ne? Ki zuba abinci sosai kici ba wai ki zubo d'an wannan ba indai kina so kiga kin warware sosai " "Mummy bari na cinye wallahi ji nake ba zan iya ci ba" "Daurewa zaki ki ci ".
Haka dai Zarah taci abincin har tasha maganinta da kyar daga bisani kuma ta shiga toilet dan watsa ruwa tana fitowa gaban dressing mirror ta nufa dan yin kwalliya wani body Lotion ta fara d'akowa me d'an karan k'amshi da ganinsa me tsada ne, sai da ta gama shafawa sannan ta fara makeup a fuskarta tana gamawa ta nufi wardrobe ta duba kayan da zata saka kasan cewar yamma ce yasa ta d'auko wasu kaya marasa nauyi riga da skirt wanda aka yi su da wani material bak'i d'inkin ya dace da jikinta dan yayi mata kyau sosai.
Sai da ta gama shiryawa tsaf! Sannan ta fito falo ta tarar da Hajjiyarsu zaune tana kallon wani film me suna "Zargi" Hajjiya Usaina na kallonta tace "Lallai jiki yayi sauk'i tunda gashi har fuska tasha makeup Alhamdulillah sai godiyar Allah" dariya Zarah tayi "Jiki ya warware mommy ta nemi waje ta zauna zamanta ke da wuya suka jiyo sallamar wani k'aramin yaro wanda be wuce shekaru tara ba, Hajjiya ta amsa da k'arfi yaron ya kuma magana "wai ana sallama da Zarah " sau uku Hajjiyarsu na maimaitawa "Zarah! Kuma?" yaron yace "Ea inji wani a waje "__________
VOUS LISEZ
BAK'AR GUGUWA
Roman d'amourLittafi ne me cike da abubuwan ban mamaki, al'ajabi, cin amana, da rugujewar zumunci da dai sauran su.