Zarah 'ya ce ga Alh.Kabir babban d'an kasuwa ne d'an asalin garin katsina, kasuwanci ne ya maida zamansa garin kano har yayi aure acan. Yana da katafaren gida wanda yake zaune a unguwar Salanta, gida ne wanda aka yi shi irin ginin zamani aka kuma k'awata shi da kayan alatu na alfarma da ababen more rayuwa masu ban sha'awa da d'aukar ido, yana d'auke da falo biyu babba da k'arami babban yana da d'akuna hud'u ciki, sai kuma wani k'aramin falo me d'aki biyu, gida ne da aka kewaye tsakiyarsa da shuke-shuke kala-kala daga waje kuwa bishiyu ne dogaye wanda inuwarsu ta rufe adon ginin da akaiwa bangon gidan, ga duk wanda ya shiga gidan Alh.Kabir yasan an kashe kud'i ciki banda tsabagen sanyin AC da ya mamaye ko ina wanda aka saka a kowanne d'aki na cikin gidan, da kuma su kansu shuke-shuken da aka zuba suke bada nasu launin sanyin. Iyayen Alh.Kabir sun dad'e da rasuwa tun bayan auren sa da shekara biyar bisa hatsarin mota a hanyar su ta zuwa kaduna. Alh.Kabir su bakwai ne, hud'u sun rasu sai kuma shi da Safiya wadda yake bin ta, sannan k'aninsa Mustapha wanda shi ma yake binsa. Duk cikinsu Alh.Kabir ya fisu wadata sai dai kuma yana taimakawa 'yan uwan nasa iya bakin gwargwado, duk da cewa suma d'in ba wai sun rasa bane gaba d'aya suna da nasu rufin asirin sai dai rashin godiyar Allah kawai. Alh.Kabir yana da mata guda d'aya Haj. Usaina auren soyayya ne tsakaninsu da juna suna da yara uku da suka haifa tare Imran shi ne babba wanda yayi karatunsa a Bayero University Kano inda yake k'arasa service d'insa a garin katsina yana da shekaru ashirin da tara da haihuwa bayan hajjiya Usaina ta haife shi bata k'ara haihuwa ba sai bayan shekara goma sannnan ta haifi d'iyarta mace suka saka mata suna Zarah yanzu tana da shekaru goma sha takwas da haihuwa wadda ita ma a yanzu tuni ta kammala nata karatun na secondary, Yesmin itace k'arama mai kimanin shekaru sha hud'u da haihuwa a yanzu tana aji na uku a secondary (Jss tree), tun tasowar Yesmin ba'a gidansu take zaune ba tana zaune ne a gidan k'anwar mahaifiyarta Haj.Saratu sakamakon ba tada 'ya mace sai d'a namiji suka rok'i da a basu Yesmin ta zauna tare da su, tun bayan yayeta aka bawa Haj.saratu Yesmin take zaune har kawo girmanta, lokaci-lokaci akan kawota hutu gidan iyayen ta.
Alh.kabir mutum ne na gari mai kirki wanda yasan mutuncin mutane ba shida kyama ko jiji da kai akwai shi da tausayi da kuma taimako duk inda yaga wanda yake da buk'atar taimako yana iya bakin iyawarsa dan ganin ya taimaka masa, duk da dukiyar da yake da ita mutum ne me sauk'in kai ba shida zafafawa ko wata k'arya cikin al'amuransa ko na iyalinsa. Alh.Kabir ya bawa yaransa tarbiyya ta gari kuma suma yaran sun tashi da wannan tarbiya.Tun lokaci da Zarah tak'i d'aga wayar Najib zuciyarta take mata zafi ita kanta ta rasa me yake damunta, abu d'aya kawai ta sani wanda zuciyarta take sak'a mata a kowanne dak'ik'a cewar "Duk yadda suke da Najib amma yak'i yarda da ita sai ya gwadata? Najib ya gama b'ata mata rai gaba d'aya, tun da be yarda da soyayyar da take masa ba". Wannan abun shi yafi tsaya mata zuciya wanda kuma shi ya hanata samun bacci a daran ranar dan har asubha ta kai bata runtsa ba sannan ta shiga toilet ta d'auro alwala tatyi sallah tare da addu'o'i sannan ta koma ta kwanta. Washe gari kuwa Haj.Usaina ce zaune a falo bayan da ta kammala had'a breakfast tana jiran fitowar Zarah har k'arfe goma na safe amma shuru babu alamar fitowar Zarah, ganin shurun yayi yawa yasa Hajjiya Usaina ta tashi tsam! ta shiga d'akin Zarah dan duba lafiyarta kasancewar bata saba kaiwa lokacin bata tashi ba, tana k'ok'arin shiga d'akin Zarah kenan ta jiyo sallama daga waje ta amsa da k'arfi sannan ta futa dan ganin me shigowa_____________
KAMU SEDANG MEMBACA
BAK'AR GUGUWA
RomansaLittafi ne me cike da abubuwan ban mamaki, al'ajabi, cin amana, da rugujewar zumunci da dai sauran su.