Chapter 12

33 5 0
                                    

*B̆ĂK̆'ĂR̆🤦🏻‍♀ĞŬĞŬW̆Ă*
🧶🧶🧶🧶🧶
       🧶🧶🧶🧶
   🧶🧶🧶
           🧶🧶
             🧶


 
S⃠t̾o̾r̾y̾ & W⃠r̾i̾t̾t̾e̾n̾
         *ცყ:✍🏻*
R⃠αвí'αt ѕвѕ
         *(ცıɠ ɠąι)*

ɪɴᴀ ʏɪ ᴍɪᴋɪ ʙᴀʀᴋᴀ ᴅᴀ ᴢᴜᴡᴀ ᴏɴʟɪɴᴇ ᴋ'ᴀɴᴡᴀᴛᴀ ᴛᴀ ᴋᴀɪɴᴀ ʜᴀᴊᴀʀᴀ sʙs ᴅᴀ ғᴀᴛᴀɴ ᴢᴀ'ᴀ ғᴀʀᴀ ᴄʜᴀᴛ ʟᴀғɪʏᴀ, ᴅᴀ ғᴀᴛᴀɴ ᴋᴜᴍᴀ ᴀɴ ɢᴀᴍᴀ ᴇxᴀᴍs ʟᴀғɪʏᴀ ᴀʟʟᴀʜ ʙᴀᴅᴀ ɴᴀsᴀʀᴀ ᴀᴍɪɴ🤲🏻 ᴀʟʟᴀʜ ᴋ'ᴀʀᴀ ᴍᴀɴᴀ sᴏʏᴀʏʏᴀʀ ᴍᴀ'ᴀɪᴋɪ ᴀᴍɪɴ.👏🏻

*fαδῖlα αlῖϒῠ ϻῠsα (ϻα δῖlαlα ) αshα kαrαtῠ lαfῖϒα ❤*


*P⃠age➡12*


    Can kuwa d'aya b'angaren Najib ne kwance a d'aki ba shida lafiya jikinsa d'auke yake da matsanan cin zazzab'i me zafi, Aamir ne ya shigo d'akin a tsora ce cikin tsananin damuwa yana salati "subhanallahi... Har yanzu zazzab'inne?" Najib dake kwance kan katifar da aka dire a k'asan d'akin yabi Aamir da kallo, da gani kasan ba shi da lafiya. Da kyar Najib yake magana cikin sanyayyiyar murya "har yanzu shi ne da zarar ya sauka yake dawowa" jikin Aamir ne yayi sanyi ganin irin halin da abokinsa yake ciki kamar ba shi ne wanda suka sha hira jiya ba, ya k'araso inda Najib yake kwance yayin da ya durk'usa kusa da shi ya saka hannu ya tab'a jikinsa yaji jikin akwai zafi da alama akwai zazzab'i a tare da shi cikin tausayawa yace "ka kuwa sha magani?"  har yanzu muryar Najib bata futa sosai a hankali yake magana kamar me ciwon baki yace "Na sha Aamir, ina jin matsanan cin ciwon kai" tausayin Najib ne ya k'ara kama shi ya kuma cewa "ko dai muje asibiti?" girgiza kai Najib yayi Aamir ya kuma magana "Be kamata ace mun zauna tun daren jiya da zazzab'i a jikinka ba ya kamata muje asibiti tunda maganin be saukar da shi ba" kallo Najib yabi Aamir da shi ba tare da yace komai ba sai ma tunanin da ya addabi zuciyarsa kawai yake wanda be wuce na Zarah ba, Aamir ya sake magana "ka yi shuru, ya kamata mu samu ma fita, an sani a cikin gida kuwa?" Najib yace "bana so a sani a gida" da sauri Aamir ya had'e girar saman idonsa yana kallon Najib "akan me baka so a sani a gida? ba kada lafiyar zaka ce kada a fad'a?" Najib ya kuma cewa "bana so hankalin su ya tashi ne" gyad'a kai Aamir yayi "idan baka so aji a gida wannan ai mai sauk'i ne kawai ka tashi muje asibiti lafiyarka tafi komai" girgiza kai Najib ya sake yi yana magana da kyar "ka kyale kawai gwara ko mutuwa zanyi na mutu na huta nasan  na mutu tunda a yanzu na rasa me sona Zarah ta daina sona ta daina k'auna ta mene amfanin rayuwa ta tunda na rasa farin ciki na?" tsayawa Aamir yayi yana kallon Najib yana magana har yanzu Najib a kwance yake yana wannan magan-ganun,  fuskar Aamir cike da tausayi da kuma mamaki yace "wai daman har yanzu baka manta da maganar Zarah ba? Ko ma dai ita kasa a ranka kaje kake k'ok'arin janyowa kanka ciwon daya fi k'arfinka? Ya kamata ka gane ita fa rayuwar yanzu data baya da akai zamanin iyayen mu ba d'aya bace, idan ka mutu kana tunanin ita zata fasa aure ta zauna haka kawai ne? Ko kuwa kana tunanin zata bika inda kaje ne? Toh bari kaji wallahi kana mutuwa wuyarta ayi sadakar bakwai da zarar ta samu wani maye gurbinka za ta yi da shi, idan ma zaka daina wannan tunanin gwara ka daina ka dawo hayyacinka cikin sauri" yana gama fad'a ya mik'e ya nemi waje ya zauna, binsa da kallo Najib yayi har sai da ya gama magana cikin rashin jin kwarin jiki ya mik'e zaune a hankali ya jingina da bangon d'akin tare da fad'in "bana tunanin Zarah zata yi mun haka bana tunanin zata iya mantawa da ni soyayyar mu daban take data sauran mutane ba irin soyayyar daka sani bace ta asha ruwan tsuntsaye, ya kamata ka fahimci haka" ran Aamir a b'ace yace "toh! sarkin soyayya ai yanzu ma naga alama tunda gashi ta kasa d'aga wayarka tun jiya kake abu d'aya amma shuru halin ma da kake ciki bata sani ba duk a cikin soyayyar ne? Wannan ya nunan cewa tana matuk'ar sonka, koda yake ai banga laifinta ba tunda ka kasa bayyana mata kanka, toh bari kaji malam tun wuri in zaka canja tunaninka gwara ka canja ka fara sanin inda ka dosa ka bayyana mata kanka ka gane sonka take ko ba sonka take ba, ni dai iyakar shawara na baka kada nan gaba wani abu ya faru kace ban fad'a maka gaskiya ba, sannan zancen zuwa asibiti ka tashi mu tafi a duba ka". Shuru Najib yayi kamar be ji me Aamir yake fad'a masa ba, shi kansa yasan magan-ganun da Aamir ya fad'a gaskiya ne sai dai kuma baya tunanin Zarah zata iya juya masa baya amma ya rasa gano musabbabin data k'i d'aga wayarsa hasalima ta kashe wayar gaba d'aya kuma baya tunanin ta karanta sak'on daya tura mata, tun lokacin da zarah tak'i d'aukar wayarsa ya shiga cikin halin k'unci da damuwa ya kasa ci ya kasa sha wannan shi ne musabbabin daya jawo masa saukar zazzab'i a jikinsa wanda har ya kaishi da ciwon kai mai tsanani, maganar da Aamir yake yi masa ne ya dawo da shi daga guntun tunanin daya tafi a hankali yace "taya zanje gidan su? Alhalin tak'i d'aga wayata tak'i ta saurare ni dole sai ta karanta sak'on dana tura mata zan iya zuwa gidan su muddin bata d'aga wayata ba bazan iya zuwa gidan su ba" mamaki ne ya kuma kama Aamir gami da takaici "kai ina ruwnaka da d'aga wayarta ni ina ganin abinda yafi sauk'i kawai kaje gidansu ka samu ka tattauna da ita ku fahimci juna, ni wallahi na zata jiya futar da kayi gidan su ka tafi ashe ba can kaje ba, ko kiran daka yi mun jiya da dare  na zata cewa zaka yi kun sasanta sai naji kace mun zazzab'i ne yake damun ka, ashe baka je ba, hmm.. sai ka kuma d'aukar ACT ka had'a da paracetamol kasha ba mamaki maleria ce, idan kuma ka shirya zuwa asibitin ne ka taso muje dan ni yanzu akwai inda zani, ba yadda Najib zaiyi ala dole ya tashi da kyar har sai da Aamir ya taimaka masa ya mik'e tsaye, suka fuce daga d'akin zuwa mota Aamir ne ya jaa motar, shi kuma Najib ya zauna a gaba suna tafe Aamir na k'ara yi masa magana "wallahi ka samu kaje wajenta na futa hakkinka" A hankali Najib yace "Zan k'ok'arin ganin nayi hakan" furta hakan keda wuya Najib ya fara yamutsa fuska tare da ruk'e ciki yana fad'in "cikina Aamir cikina" da kyar yake maganar hankalin Aamir yayi matuk'ar tashi cikin hanzari ya k'ara gudun motar yana cewa "lafiya? meya samu cikin naka?" da kyar Najib yake magana "ciki na Aamir ciki na innalillahi..."_____________


*💅🏻B⃠ıɠ ɠąι ¢ɛ✍🏻*

BAK'AR GUGUWAWhere stories live. Discover now