*B̆ĂK̆'ĂR̆🤦🏻♀ĞŬĞŬW̆Ă*
🧶🧶🧶🧶🧶
🧶🧶🧶🧶
🧶🧶🧶
🧶🧶
🧶S⃠t̾o̾r̾y̾ & W⃠r̾i̾t̾t̾e̾n̾
*ცყ:✍🏻*
R⃠αвí'αt ѕвѕ
*(ცıɠ ɠąι)**©-Aɴᴀ ᴛᴀʀᴇ Wʀɪᴛᴇʀs Assᴏᴄɪᴀᴛɪᴏɴ ✍🏻*
(wє ѧяє ṭһє ɞєśṭ ѧṃȏṅɢ ѧʟʟ wяıṭєяś)📚
https://mobile.facebook.com/Anatarewritersassocian/ғaтan alĸнaιrι ga 'yan groυp dιn мυ na *ғιĸrar мarυвυтa* тare da мaĸaranтa wannan lιттaғι na *вaĸ'ar gυgυwa* alĸнaιrιn allaн ya ĸaι мυĸυ. 🥰
*fαδῖlα αlῖϒῠ ϻῠsα (ϻα δῖlαlα ) αshα kαrαtῠ lαfῖϒα ❤*
*P⃠age➡25*
"Kwanakin baya kamar ta tab'a suma ko?" da sauri cikin muryar kuka Hajjiya tace "sau biyu ma tana yi, yanzun ma suman ne ko?, Yaushe zata farfad'o likita?" Alh.kabeer yayi caraf yace "doctor me yake faruwa da ita? Ka fad'an please" shuru doctor Shu'aib yayi ya bud'e wata k'aramar akwati da yazo da ita ya kuma d'ebo wasu kayan gwaje-gwajen duk suna kallonsa har yayi ya gama Hajjiya da Alhaji suka kasa hak'uri suka kuma tambayar lafiyarta, Jikin doctor Shu'aib a sanyaye yace "With all tests and diagnosis,I have not established the nature of her illness, sai dai da za muyi hak'uri mu d'an jira har zuwa wani lokaci" duk wannan jawabin da yake Haj.Usaina kallonsa kawai take tana ci gaba da kuka, banda fad'uwar gaba babu abinda ke faruwa da ita, sai kuma kanta da yake k'ok'arin sarawa, sun shafe tsawon lokuta suna jiran farfad'owar Zarah amma Ina! Shuru kamar an shuka dusa, babu alamar farfad'o warta, idan kuwa dai-dai ne tunanin da Haj. Usaina take akan Zarah to duk suman da tayi a baya ba kamar wannan ba domin kuwa ya banbanta da wancen hatta tsawon lokacin data d'auka shima ya banbanta da lokutan data d'auka a baya, hankalin Haj.Usaina dana Alh.Kabeer ne ya k'ara mugun tashi cikin rawar murya Haj.Usaina take magana "likita dan Allah ka sanar da mu idan mutuwa tayi gwara mu sani ba zamu hana Allah ikonsa ba" taci gaba da kuka mara k'ak'k'autawa, tausayin Hajjiya ne ya kama Alhaji ya danne zuciyarsa yace da doctor Shu'aib "ya kamata ka sanar da mu halin da ake ciki" doctor Shu'aib ya k'ara kallan Zarah bayan daya ja wani dogon ajjiyar zuciya yace " Ina ganin ya kamata mu d'auketa zuwa asibiti dan yi mata wasu gwaje-gwajen tunda acan muna da wasu kayan aikin da ba za'a iya tawowa da su nan ba ina ga hakan zai fi" koda jin hakan sai jikin Haj.Usaina ya k'ara sanyi gabanta yaci gaba da bugawa babu k'ak'k'autawa yayin data dad'a fashewa da wani iri matsanancin kuka haka taci gaba da yi ba tare data tsaya ba, babu yadda Alhaji beyi mata dan ta daina kukan da take ba, amma bata saurareshi ba dan ya ruga daya gama tarwatsa mata rayuwa muddin akace yau Zarah ta rasu. Gajiya yayi ya kyaleta duk da cewa shima tasa zuciyar a raunane take daurewa kawai yake kasance cewarsa shi namiji ne, tana kuka Haj. Usaina tace "Dan Allah likita ka fad'a mana gaskiya idan ta mutu ne ka sanar da mu doctor babu wani kame-kame da zaka yi" shuru doctor Shu'aib yayi daga bisani yace mu d'aukota muje can d'in zaifi" nan Haj.Usaina ta ruk'e Zarah tana kuka tana cewa "babu inda za'a je mun da yarinyata idan ta mutu ne gwara a samar dani anan ba sai munje can ba" Alh.Kabeer ne yayi mata magana ganin yadda take wasu abubuwa kamar wata zautacciya, ko shi da yake jin rad'ad'i a zuciyarsa beyi haka ba sai ita, duk da cewa yasan ita uwace dole zata fi jin zafin hakan, a hankali yace da ita "ki bari mana muje can d'in a duba ta tunda ya fad'a da bakinsa ai ba zai k'i fad'a mana ko menene ya sameta ba in har bunciken da yayi ya nuna masa" k'in bari tayi a tafi da Zarah dan ta ruga data gama gane cewar ta mutu ne ake son b'oye mata, da kyar Haj.Usaina ta bari a tafi da Zarah asibiti tana matsanancin kuka na rashin 'yarta da tayi tunaninta d'aya bata san taya zata iya cire son Zarah daga cikin zuciyarta har ta daina tunaninta ba, idan Zarah ta mutum shikkenan ba wata 'ya mace a wajenta ga Yesmin ta ruga data dank'awa k'anwarta Haj.Saratu, jin maganar Alh.Kabeer da ta ji yana cewa "ruk'ota mu tafi" yasa Haj.Usaina dawowa daga guntun tunanin data tafi mayafinta ta d'auko ta lullub'a idanuwanta duk sunyi jahur sun kuk-kumbura sabida tsananin kukan data ci, ana cikin haka suka ji murya kamar daga sama ba Hajjiya da Alhaji kad'ai ba hatta doctor Shu'aib sai da ya razana gaba d'ayansu suka baza idanuwa dan ganin abinda ke faruwa cikin tsananin mamaki suke kallo ba komai bane face muryar Zarah da suka ji tayi magana, Haj.Usaina ce ta fara ruk'e Zarah tana murna ganin ta farfad'o bata mutu ba tana ruk'unk'ume ta kamar wadda ta b'ata tsawon shekaru ba'a ganta ba sai yanzu, murna da farin ciki duk tabi ta cika zuciyar Haj.Usaina tama rasa ta Ina zata fara shafa Jikin Zarah take tana cewa "Sannu Zarah, Sannu kinji" wasu hawayen farin ciki ne suka runk'a gangarowa kan kuncinta, shima Alh.Kabeer murna yayi ganin 'yarsa ta farfad'o, doctor Shu'aib ma farin ciki yayi da ganin farfad'owarta sai a sannan yake sanar da Alh.Kabeer "suma tayi" Alh.kabeer yaja doctor Shu'aib waje suka futa inda yake tambayarsa kan matsalar Zarah, a hankali yake magana, "amma doctor wai me yake kawo mata wannan matsalar ne?, Ko dai tana da wani ciwo wanda ba mu San da shi ba?" Doctor Shu'aib yayi ajjiyar zuciya kad'an sannan yace "a bunciken da nayi mata ba tada wani ciwo tun ba yau ba na saba dubata a duk sa'ar da ba tada lafiya, kuma ansha yi mata testes kala-kala ba'a ga wata kwayar cuta a jikinta ba", al'amarin daya k'ara d'aurewa Alhaji kai kenan, taya hakan zata faru? Wannan wanne irin ciwo ne da ba shida magani?, ko dai yarinyar nan k'arya take, Ita take shirya komai? yana cikin zance da zuciyarsa Doctor shu'aib ya katse shi da cewa "karka damu ko ba yau ba zuwa monday za'a iya kawota sai ayi mata wasu gwaje-gwajen har mu shawo matsalar," nan dai suka ci gaba da tattaunawa har suka yi sallama, doctor Shu'aib ya tafi. Duk wannan abun daya faru Imran be san ya faru ba, ko bayan daya shigo sashin babu wanda ya sanar da shi abinda ya faru, itama Zaran babu wanda ya sanar da ita komai dan kar hankalinta ya tashi, koda ta farka taga idanuwan Haj.Usaina sunyi jahur kamar gauta sun kuma yi b'ulu-b'ulu kamar me ciwon ido data tambayeta cewa tayi abune ya fad'a mata cikin idon da kyar aka samu ya futa, kuma ta yarda.
Washe gari da sassafe tun basu gama breakfast ba suka jiyo sallama cikin falo inda kallonsu ya koma ga me shigowa___________*💅🏻B⃠ıɠ ɠąι ¢ɛ✍🏻*
ČTEŠ
BAK'AR GUGUWA
RomanceLittafi ne me cike da abubuwan ban mamaki, al'ajabi, cin amana, da rugujewar zumunci da dai sauran su.