☆☆☆☆
Can kuwa Zarah tun kan ta idar da sallah̸ wayarta dake kusa da ita ta fara k'ara cikin hanzari ta idar da sallar ta kai hannu ta d'auka tana duba fuskar wayar taga sunan Najib ya fito da sauri ta mik'e tayi waje tsakar gida ta zauna kan step sannan ta latsa wayar ta karata a kunne "Hello!" daga can d'aya b'angaren ma akayi magana " H'ello! baby na ya kike" ya jikin naki ? fatan dai kinji sauk'i kamar yadda nake so" murmushi ta fara yi sannan ta mayar da martani "lafiya lau jiki yayi sauk'i yayi kwari dan har na fika k'arfi ma" saka dariya yayi "kema kin san wannan zancen wasa ne babu yanda zaki ki fini k'arfi a yanzu dan nasan har yanzu jikin ki be gama kwari ba" "hmm kaji ka toh zamu gwada aga wanda yafi amma dai ni nasan koda an gwada ni zan fika" dariya ya sake yi "kin cika zolaya ni dai yanzu ki tabbatar mun da lafiyarki ko hankalina ya dad'a kwanciya kar na shiga damuwa" "wai baka yarda naji sauk'i ba ?" "Eh mana" "hmm da gaske naji sauk'i ka yadda mana, oh! ni nama manta nace in ka kira ba zan d'aga ba" a shagwab'ance tayi maganar, ya saukar da murya "haba baby na me yasa zaki d'au wannan tsattsauran wukuncin me yayi zafi?" sake shagwab'ewa tayi "ba kaine ba jiya muna waya kace zaka sake kira kuma kak'i sake kira" "oh! my god, kinsan na fad'a miki Abbah ne ya kirani lokacin kuma bayan ya aiken na dad'e acan dana dawo ban san ma sanda nayi bacci ba, am sorry my baby ai ni na daban ne a wajenki karki fushi mana" tayi murmshi mai ratsa zuciya tamkar yana ganinta "shik-kenan to ya wuce amma dan dai kaine da wani ne ba zan hak'ura ba" shima murmushin yayi "yauwa baby na ko ke fa , har naji sanyi a zuciyata, wai yaushe zanzo naga wannan kyak-kyawan murmushin naki a zahiri ne?" "duk sanda kake so am free, kasan nafi son ganinka fiye da yanda kake son ka ganni" suna cikin waya Hajjiya usaina ta fito da sauri zarah tace masa "zan kira anjima" tayi sauri ta katse wayar sabida ganin Momynta da tayi ta fito, murmushi hajjiya Usaina ta saki ba tare da zarah ta kula ba, tayi kamar bata ganta ba ta wuce. Zarah taji dad'i a ranta ganin Hajjiya bata kalli inda take ba sai take tunanin Hajjiya bata ji wayar da take ba, har Hajjiya Usaina ta wuce sai kuma ta dawo da baya tace "zarah" gaban zarah ya yanke ya fad'i a firgice tace "Na'am" "kin kuwa gaisa da yayan naki daya shigo?" zarah tayi ajjiyar zuciya "Ya Nauma? eh! mun gaisa da shi" hajjiya tayi murmushi ta wuce, sannan itama zaran ta koma cikin d'aki ta zauna kan kujera.
☆☆☆
Najib yaro ne Matashi me hankali da nutsuwa, bayan kyau da Allah yayi masa irin wanda kowacce 'ya mace take son ganin d'a namiji da shi yana da ilimi na addini da kuma na zamani boko, ya dad'e yana son Zarah tun tsawon shekaru uku da suka shud'e suna tare sai dai babban kuskuren da Najib yayi a wajen zarah be wuce na rashin bayyana kansa da ya kasa yi wajen nata ba tunda kuwa har kawo i-yanzu be tab'a nunawa Zarah fuskarsa ba dan ita kanta ba zata ce ga yadda kaman ninsa suke ba, face abu d'aya data sani da shi ya iya soyayya kuma muryarsa nada dad'in saurare ga kowacce 'ya macen da taji dole ta tsaya ta saurare shi, don ya cancanta dan shi kansa har zuciyarsa babu wata 'ya macen da yake so sama da Zarah babu kuma wunin lokacin da zaiyi ba tare da yaji muryar Zarah ba, a kullum yana saka wa zarah credit na d'ari biyar duk da cewa ita hakan baya gabanta abunda yake gabanta be wuce soyayyarsa ba cikin zuciyarta.

BINABASA MO ANG
BAK'AR GUGUWA
RomanceLittafi ne me cike da abubuwan ban mamaki, al'ajabi, cin amana, da rugujewar zumunci da dai sauran su.