agreement

71 13 0
                                        

Hk ko akayi washe gari muka shirya muka tafi ruma , nida elder  da farha har ma da Abba , da muka Isa kurfi ni na nuna musu hanyar da xamu bi sai ga mu gidan , muna xuwa na fita dagudu sanadiyyar ganin baffa da nayi ya fito , xuwa nayi na rungume shi nace baffana Ina wuni yace lpia qlau ayisherh kece hk , nace eh baffa yaushe ka dawo, shiru yayi sannan yace ai yanxu nayi kusan shekara hudu da dawo , tace baffa shine bk neme ni ba yace na neme ki ayisherh Amma bansan ya akayiba daga ranar bansake tunawa Ina da ' ya aduniya ba sai yanxu da na ganki , farha ce ta riqo hannu na sai alkcn natuna tare da mutane naxo , baffa yace wannan fa tace baffa ba ita kadai ba da mutane muka xo , baffa yace to bari na Shiga daga chan ciki sai ki shigo dasu , xuwa nayi na musu iso xuwa cikin gidan mu , gidan ya Kara kyau dan an Chanxa ginin da kuma fentin gidan , xuwa mukayi muka xauna , Abba na shigowa gani nayi baffa ya tsaya Yana kallon shi , shima din kallon shi yake yi sai naji baffa yace alhj Ibrahim Abba yace Ahmad , Nan muka fara kallon kallo , xaunawa Abba yayi , sannan suka gaisa sai baffana yace dama Ashe da rabon mugana , Abba yace eh wlh gashinan dae mun sake haduwa  yanxu ma yar ka ce ta hadamu , baffa yayi dariya ce da Kuma danka ne Muhammad Adeel , yace wlh kuwa Nan adeel ya gaishe shi . Abba ya hadu da baffa ne Ranar da adeel ya bata baffana ne ya tsince shi ya kawo shi har gida , Abba ya Mishi godiya ya bashi wasu maqudan kudi baffa yaki kar ba , Abba yace to tunda ka ki karba in kana da yarinya mace Karama inaso inta girma kabani ita na hada ta aure da Dana Muhammad Adeel , baffa yace ba damuwa insha Allahu sannan yatafi lkcn kuwa baa Dade da haihuwa ta ba. Abba ne ya katse baffa daga tunanin ta yatafi yace inaso kabar min ayisherh gurina Dan Allah da Kuma farha , baffa yace bakomae alhj na bk ita tunda ni kona hanaka ita karshe dai wurin ka xt koma Kar kashin ikon wani , murmushi Abba yayi yace ngd , nikuwa nakasa fahimtar mgnr baffa , bani ba ko adeel Bai fahimta ba , bayan anyi sallar laasar muka koma na tambayi baffa Ina Inna yace taje wuni gidan hajiya nace to baffa agaida ta insha Allahu xan dinga kawo muku xiyara , muka koma gida farha na kwance kan cinyar adeel a parlor na xo na ce , farha tashi muje ki kwanta kin tashi tayi na juya , adeel yace farha auntynki tayi fushi gidan su xt koma ai ko tashi tayi da gudu ta kamo hannuna tana girgixa min Kai nace to muje ki kwanta Bina tayi muka wuce dama adeel so yake ya tafi tashi yayi yatafi gidan shi , wayar shi ya ciro ya Kira Umar , Umar nadawo fa tun jiya Umar yace Dan Allah fah , ni Ina nan Zaria , adeel yace yaushe xk dawo ya ce sae next week  yace ohk toh fira suka Dan taba sannan ya kashe  wayar , juyawa yayi Yana ta tunanin maminshi kwanannan Yana yawan tunanin ta 😞 .
Wacece mamin adeel
Mahaifin adeel alhj Ibrahim , Matan sa uku   , Fatima ( Mami) , Aisha ( ammi) ,  sai Kuma hassana ( aunty) .
Mami yaranta biyu  Muhammad ( adeel)  sae asmau ( Yasmin) .
Ammi kuma yarinyar ta daya Fatima Wadda taci sunan Mami Amma ance Mt ( farha) .
Aunty Kuma bt taba haihuwa ba , Mami ta Bata ne shekaru 21 da suka wuce lkcn Yasmin nada shekara 1 a duniya Wanda haryanxu Bata dawo ba . Ammi ta dauki su adeel kamar yaranta , inba angaya mk ba bxk taba cewa ita ta haife su ba , Yasmin nada shekara uku ta haifi farha , hk yasa adeel ya Rada Mt suna da sunan mamin shi sannan ya dauki son duniya ya daura wa farha sbd jinta yake kamar maminshi da ya rasa Yana da eleven years old , yanxu gashi lkcn da aka haifi farha Yana da 22 years  , ita Kuma aunty  tun  kafin mamin adeel ta haifi Yasmin aka auro  ta  amma in akwai wadda Bata so to tabiyo bayan mamin an auro ta da 2 years Mami ta haifi  Yasmin  , da aka haifi farha Kuma tunda Mami Bata Nan sai tsanar ta dawo Kanta amma Bata taba nunawa ba agaban Abba , sannan tana son adeel Amma shi baya sonta sbd tun tana Karama abbansu ya aurota , kamar Wanda aka yiwa asiri  gashi tun lkcn ta iya makirci kasancewar ta yar jinin sarauta mahaifin ta shine sarkin daura , farha na da shekara uku ciwon hauka yasameta bayan shekara uku  da kamuwa da hauka Abba da aunty  suka tafi England sae bayan shekara hudu suka dawo   .
Wannan kenan Ina fatan kun fahimce wacece mamin adeel , itace mahaifiyarshi ta asali .

            **********
Kubiyo ni a next chapter  Dan Jin yadda  rayuwar Nan xt kasance
Lurv u all
Tnx for reading
❤️❤️❤️🌹

Ayisherh💕Where stories live. Discover now