After 4 years
Shirye shiryen bikin farha kawae akeyi , Mami ce ta shigo dakin ammi tace ammin adeel , adeel yace abaki waya Yana ta kiranki bakya dauka , ammi tace oh kedae Bari wlh kingawayar na sakata silent sbd mutane , daedae lkcn wayar tasakeyin ringing dauka tayi hello ammi meyasami wayarki Ba'a dauka , tace adeel wlh abubuwane suka min yawa shiysa yace ohk dama yau su Ashna xasu zo a gyara musu guri , tace to shikenan sai sun xo , ammi Kar abarsu da yunwa fa tace nikam Kar ka dameni da wani Kar a barsu da yunwa , ita ashna me tasani dudu du Bata fi wata hudu aduniya ba , yace to in baa ba mamanta abinci ba ya xata bata abinci , ammi tace naji su ahlam fa , yace su tare xamu xo sai Ranar Monday tace su affan fa yace duk muna tare daga ayisherh sai ashna xasu xo yau , toshikenan Allah ya kawo su lpia, ameen ya fada sannan ya kashe wayar
Ashna👇Ashna new born babyn su adeel last four months da suka wuce aka haifeta, yarinyar akwai wayo sosae , da misalin karfe 7:30 suka iso mota biyu sukoyo daya ta guards din ta daya kuma ita kadai sai ashna kawae ne aciki ita ke driving bayadda batayiba adeeel ya biyo ta yace sai Monday aiki ya Mishi yawa dayake tun bayan haihuwar su affan suka koma Abuja da xama , yanxu shekarar su hudu da wata hudu acan su Mami Basu taba ganin ashna ba sai dai a hoto , da isar su sunaiha ta karbi ashna Aiko ta fara kuka dama ita Bata yadda da mutane , miqawa ayisherh tayi tace wannan Bata da yadda kamar fadeel dayana yaro sunan second born din sunaiha , ayisherh tace wlh ko su ahlam sai ta ga dama take yadda dasu gara su affan tana yadda suyi Wasa,tace Wai kice kina aiki , wlh kedae Bari , wurin Mami suka fara xuwa Mami kallonsu takeyi da mamaki ita dai tayi waya da adeel Bai gaya Mata xasu xo ba da ko abincine an musu , ayisherh saukar yaushe , ammi tafada tana mai gyara karbar ashna kin yadda tayi , Mami tace to fah wannan kishiyar bata yadda da mutane , eh wlh Mami , Mami tace shine ko gayamana baayi sai muganku kwatsam , ayisherh tace hk yace idan yafada Miki xamu xo xakice sai anxo dasu ahlam shikuma bayaso abarshi shikadae gida sai Monday xai xo, ohh tanan ya bullo xai xo yasameni ai , ayisherh tace Amma ai ya fadawa ammi har angyara Mana daki tace lallama adeel.nifa yasa na ba ammi waya dayake dakin ana surutu shiyasa bangane me suke cewa ba Amma ai yau Saturday jibi xai xo yasameni , tashi tayi ta shiga dakin ammi , ammi tace maraba da kishiyata kawo ta Mika ta tayi Amma sai ta fara kuka , ammi tace yau munshiga uku yarinya yar wata hudu tasan mamarta to sai kita xama , Kara lanqwabar da Kai tayi tana tsutsar yantsunta guda biyu na tsakiya , ammi tace yarinya ko kyau , Yasmin dake xau tace Nan kadae fa ammi namesake Dita tafi kowa kyau , ammi tace saiki fadawa wadan da Basu da namesake , dariya Yasmin tayi tace ai ingaya Miki ashna tafi afnan kyau ai affan da afnan duk an baro su baya masu kyau.dai sun ahlam ne da ashna , ammi tace koma minene nidai yanxu kaisu dakin adeel.na da Yana can an gyara ,tace to tashi sukayi suka nufi part din adeel na cikin gidan parlor ne da 3 bed room ,Shiga sukayi wanka sukayi tare ita da ashna sannan ta chanxa musu Kaya , parlor ta fito Wanda dama already an aje mata abinci ci tayi taxo tayi sallar magrib da ishai ,ta hau gado.ta kwanta ashna tafara kuka Wanda dama yarinyar acici ce , bayan ta bata abinci sannan sukayi waya da adeel tayi waya da su ahlam sannan ta kashe wayar ta gyara ma ashana kwanciya sannan ta kashe musu fitila suka yi barci.
YOU ARE READING
Ayisherh💕
Fantasythe story is all about how lifes goes on with one girl ,the story is full of challenges, pains, and love