Wasiyar Aure 01

3.6K 375 10
                                    

Wasiyar Aure😭❤❤

Written by; Najaatu shehu naira

FKD Fans Writers 《《 01 》》

Inkinsa kokasan bazakayi votes ba, dan Allah karka karantamin littafi,
Littafina bana kudi bane amma ina bukatan Votes, Allahsa zamu fahimta juna....

Karfe biyar da rabi na yamma,
Cikin watan Ramadhan, magrib ya kawo kai,
Gida ya game da kamshin kayan abincin da 'yan aiki ke kaidakawo sunayi domin bude baki,.

Rayhana nazaune da zungureran cikinta haihuwa koyau kogobe a katafaran Parlour ta na'alfarma da yaji maka-makan kujeru da tabkeken Tibin bango plasma,
Idonta nakai tana kallon maimaicin shirin Tarkon Kauna na Arewa24,
Madina 'yar shekara uku dawatanni tazo dagudu ta tace "Ummi Abbanmu nakiranki wai kizo yanzun" tana fada tajuya takoma da gudu.
Rayhana ta yamutsa fuska ta turo baki cikin mita tace "Wlh Diamond bazai barni na hutaba, mutun shikenan kira kamar tsohon makawo",
Cikin 'Yan dabaru ta tashi,
Tinkis-tinkis tana tafiya kamar baza taiba takai dakinshi,
Ahankali tabude taja ta'tsaya bakin 'kofar domin tantance ta'inda yake duba da duhun dakecikin dakin.

Hamza nazaune kan katafaran Royal bed dinsa da yaji ado,,
Ganin ta tsaya tana neman inda yake,
Ya'kara hasken lantarkin dakin yana murmushi yace "saifa kice yanzu baki ganniba ko?"
Harara ta gallamai kan tai fara'a tace "ni narasa matsalarka da haske, daki kullun cikin duhu kamar mara gaskiya",
Lumshe ido yayi daidai zata zauna ya bude kafada yace "kwanto nan",
Murmushi tasaki taimai fari da ido tace "anki din, meyema dalilin kirana Diamond ina kwance ina hutuna",
Dasauri yarike baki yagirgiza kai yace "haba Ummin Munawwara kamar bakyason lada, toh da kwanciyar da kikaje kinayi dako shafamin gemuna kike Allah kadai yasan yawan ladan da zaki samu",
Kamar zatayi kuka ta juyo tace "Haba Haba Diamond kasanfa wahalar da cikinnan kebani, bazaka tausayamin ba, shine babu wani kwakkwaran dalili zaka tasoni",
Nandanan jikinshi yayi sanyi, yasa yatsunsa cikin nata cikin rarrashi yace "am sorry Beauty insha Allahu zaki haihu lafiya, kiyi hakuri bada gangan nayiba, tunaninkine yahanani sakat anan, tunda kika sama cikinnan kike guduna, nazama kamar gauro"
Yanda yake shishshigemata yana maganar yasa ta janye jikinta ta yamutsa fuska tace "pls Diamond kasan ni wlh banson kamshin komai naka, kayi hakuri nasan tunda cikina ba yaron ciki bane yakamata nadaina amma abun ya'ki",
Ta matse dan guntun hawayen dake shirin sauko mata tace "am sorry Diamond bada gangan nakema ba",
Kan faffadan kafadarsa ya janyo kanta yasa cikin rarrashi yace "ya'isa maisaurin kuka, karki damu idan ansha ruwa muje Mall mu'kara duba wasu turaruka 'kila mudace inba hakaba zan hakura kawai harsai kinhaihu kinji?, Ni aguna lafiyarki ne kangaba".
Ta 'dago kanta sukai ido hudu, ta lumshe ido tace "Diamond watan azuminefa karka karya azuminka, baruwana wlh",
Tsam ya saki hannunta ya kauda kai yace "fine naji,".
Tamike tana dariyar mugunta tace "katashifa lokacin sallah yakusa",
"Okay" kawai yace atakaice,
Yatashi yashiga bayi ya dauro Alwalah tana zaune yace "Beauty natafi masallaci",
"Allah kiyaye hanya", tafada,
Ya gyadakai yatafi...

Karfe tara yazo dakinta taci kwalliya cikin doguwar riga yace "Beauty kinshirya?",
Tsam ta tashi tace "eh muje",
Lokaci daya ya hade rai yace "toh meye na kwalliya kuma, ni bansan haka da tsohon darennan kije kina fainter fuska wasu dama neman mata kekaisu wajan ba siyayyan Allah da Annabi ba",
Sanin hali irin na Hamza da masifa suna iya kaiwa harwajan baidaina fadaba,
Ta dauki wiper ta goge fuskan,
Ta juyo ta dagamai hannu tace "shikenan?"
Washer yasaki fara'a yana murmushi yace "eh muje, ina Munawwara, bada ita zamuba?"
Girgiza kai tayi tace "a'a tanada Assignment tanacan tanayi",
Ya gyada kai yace "toh muje tunda ba dadewa zamuyiba muma",
Yana maganar yarigata gaba yafita,

Daga bakin Gate ta tsaya, yafito da motar cikin Parking Lodge yatsaya tashiga sannan yaja,
SIDI and Son suka shiga,
Yaje yayi parking suka fito tana tafiya tinkis-tinkis yana binta ahankali,
Zasu shiga 'kafarta ta ri'ke,
Taja ta tsaya ta kalleshi tace "yanzu Diamond saina shiga ne? Wallahi 'kafata tarike, kaje kasiya kadawo",.
Dasauri ya girgiza kai yace "kinsan danki za'ba kallan kamshin da kikeso mukazo.
Ya dur'kusa yace "toh mi'kar da 'kafan kan kafa'data",
Dasauri tasunkuya ta'dagoshi tana murmushi tace "so kake ido yadawo kanmu, karma kadamu yasaki, mushiga",
Ya 'dago yana kallonta cikin kwayar ido cike da kauna da bege, ya girgiza kai yace "muje kawai",
Dasauri tasha gabansa tace "mainene",
Ya lumshe ido cikin siririyar murya mai narkar da zuciya yace "naga kina maganar mutanene, nikuma Beauty babu abunda bazan iya mikiba, ko'agaban duniyane"
Tafin hannunta tasa tahau shafa bayansa suna tafiya tace "Diamond ya'isa karkayi kuka 'kafarma tasaki wlh" tanayi tana dariya,

WASIYAR AURE😭❤❤completeWhere stories live. Discover now