👨👩👧👦ZAMAN YA'YA👨👩👧👦
*Based on true life story*
Story &written by Mmn muhibbat Abdullah👩👧👧
Dedicated to *TASKIRA MEMBERS*
PAGE 1
*DUK BUDURWAN DA TAKE FATAN SAMUN MJI NAGARI TA GAMA DA IYAYENTA LPIA*
*****Zaune suke a babban parlournta suna jajanta abunda ya samu diyarsu AFIFA mata ne su 4 zaune suna hawaye sbd iftala'in da ya afka ma Afifa na wayar gari da akai tana dauke da juna biyu wanda bana aure ba,Haj balki mahaifiynta ta mike ta wanke ta da mari tace yanzu duk bakin cikin da nake shaka sbd ku duk bakin ckn dana ci kafin zuwanku duniya da bayan zuwanku duniya,abunda zaki saka mani dashi kenan afifa kin bani kunya kin tozartani sbd wannan abun bakin ciki ne gareni da masoyana ace duk tsawon shekaru ina zaune dan kar in fita ku wahala Amma da abunda zaki saka mani kenan😭rike zuciyar ta tayi domin tana fama da ciwon zuciyarAbubuwan da ta hada tsawon shekarun zaman aurenta .Riketa haj salma tayi daya dg ckn matan da suke xaune a palour sbd kmr zata fadi sbd laluratta, tace balki kiyi hkr kaddarar mu ce ta rayuwa da take dibarmu tana walagigi damu har muka tsinci kanmu a wannan yanayin.
Ma'u ce ta kamo su ta zaunar dasu domin su samu nutsuwa ta share ma haj balki hawaye ta kalli afifa dake durkushe gaban iyayen nata tana hawaye,tace mata"Afifa ki ji tsron Allah ki gaya mana cikin waye tana hawaye tace wlh mama yaudarana yayi na Arif ne(shi ne wanda aka saka masu biki) tace lkcn da muka je gdnsu gaida mamanshi shi ne ya saka mani Abu ckn lemo Ma'u daga kai tayi ta kalli balki tace kina aikin me kika barta fita da saurayi ?
balki ta daga idonta da suka kumbura tace tare fa da mima kanwar ta sukaje sbd kar a barsu su kadai sbd Abbansu bai barinsu fita su kadai amma sai da ya cuce mu ,kalllon Afifa tayi tace"tashi ki shiga daki zamu yi mgna "ba musu Afifa ta mike domin daman ta gaji da durkushen da tayi .Ma'u ce ta kalli haj zainab tace zainab baki ce komai ba ya kamata kice wani abu yanzu haka rayuwa zata yi ta walagigi damu da sunan *ZAMAN YA'YA* yanzu wane amfani ne zaman yayi mana bayan gashi sai matsala ke fitowa Lumshe ido tayi cike da damuwa tace to ni me zance maku Abunda nake gaya maku shekara da shekaru kuna gani na a matsayin wadda bata san me take ba shine dai yanzu zan sake maimatwa.Shin menene zaman ya'ya wani kalar zaman yara ne ya kamata mace tayi a mahangar musulunci?shin akwai zaman ya'ya a musulunci ko a'a duk Shin ya kmta ku zauna?shin da wace zuciya kika zauna zaman ya'ya ?shin kun manta nasha fada maku cewa laifin iyaye yana shafr yaransu a zamantakewar Aure .Amma kullum sai kuyi ta ganin kmr ina yi maku bakin cikin zama gdn mazajenku kullum gani kuke zan tarwatsa maku jin dadin yaranku sbd ni mijina bai kai naku wadata ba shin yaushe zaman Amana yayi karanci😢 da ace a baya na biye ta maganganunku a kaina da tuni mun rusa zumunci da kawancen da tun da muka tashi ake yinsa.
Haj balkice taja numfashi Alamar wanda yaci kuka ya gaji tace haba zainab kiyi hakuri yanzu ba lkcn maido da Abunda ya wuce bane lkcn neman mafita ne .Ya kamata mu kawo karshen damuwan mu.
Shiru sukai su duka dakin yayi tsit baka jin karar komai sai karar AC.Haj salma ce ta katse masu shirun nasu domin tunda suka fara mgna bata saka baki ba sbd itaama matsalar gdnta sun isheta game da Halayyar mijinta da Halin da Yaranta suke ciki gidan aure tace ni ina ganin ya kmta ace mun yi tunanin rayuwar mu ta baya dan muga ta inda muka kuskuro.
Dukkan su suka kalleta ckn damuwa domin kowacen su tana da lbr mai taba zuciya basa sun su tona bakin ckn da suka binne na shekara da shekaru Amma ya zasuyi ya xama dole su tono sa domin maganin matsalolinsu.
****30YEARS BACK*****
Balki,zainab,salma,Ma'u haifaffin garin katsina ne abokan juna ne sbd makwabtani dukkansu sbd gidansu balki yana kallon na juna zumuncin su ya yi karfi ne sbd zumuncin iyayensu Ada can makwabta sukan zamo tamkar yan uwan juna wanda har idan mutum yazo gidan da wuya ya gane dan gida da dan makwabta sbd yadda makwabci yake da iko Akan dan makwabcinsa wanda haka yanzu Abun ne mai wuya da zaka samu irin wannan zamantakewar a yanzu sbd yadda son ya'ya ya rufe mana ido kowa bai iya kauda kai kan yaranshi.
Kamar yadda muka sani yaran makwabta sunayin makaranta kusan daya da sauran yan unguwa haka ce ta faru g su balki Mkrtarsu daya boko da mkrantar Allo da mkrtar islamiyar dare.
Iyayensu balki masu rufin Asiri ,shiyasa suma su balki suka tashi ckn rayuwar rufin Asiri,yan mata ne da a lkcn bazasu wuce shekara 18 ba Sun kamala mkrtar secondary schl wanda a lkcn Ana shirin masu Aure ne da mazajensu da suka fiddo.
Bala shine zai auri balki ya gama krtunsa na degree a fanni kasuwanci shiyasa ma da ya gama sai kawai ya fara kasuwancin a ckn kasuwan central market katsina yana zuwa yana saro kaya ne a kano a wancan lokacin.Ma'u kuma itace zata auri Mudi,ma'aikacin gobnati ne yana aiki lkcn a NNPC a matsayin karamin ma'aikaci yana kwasar Albashin sa dai dai misali.
Sai salma ita ce zata auri sule ,sule shima dan kasuwa ne amma shi kasuwancinsa ba a garin katsina yake yinsa ba a Abuja yake da shago kayan masarufi .Sai Zainab zata auri Talle shima wurin aikin su daya da mudi mijin ma'u wato NNPC.
**A al'adarmu ta aure idan za'ayi akanyi bincike tou haka dai ya faru ga su mudi iyayesu zainab sunyi bincike sun kuma gane mutanen kirki ne a zahiri haka ma iyayensu. Amma a badini kowa ne yana da mugun halinsa shidai mudi shaye shaye yake yi talle kuma maneman mata ne haka mijin balki ma bala ba a barshi a baya ba domin suna hadewa *sabon layi* shiyasa ma suka zama Abokai,sabon Layi tsohuwar unguwa ce a garin katsina mai tsohon tarihi unguwa ce da tayi kaurin suna wrn tara karuwai da yan daudu da yan karta da mashaya a wancan lkcn zai yi wuya kaga mutumin kirki yana zaman hira a sabon layi sbd unguwa ce da idan marece yayi zaka iske an shimfida tabarma duk wata karuwa tana gefe sai abokan holewarsu suna zaune ana karta a takaice kamar wata gargajiya club ce zaka iske yan daudu suna tuwo a wrn na saidawa da sauran Abun bukata tou su mudi acan aka jame da su talle da bala.Kasancewar su bala suna da abun hannun su a wancan lkcn saboda Bala ma yana da motarshi (hajiya ba duwawu🤣)shiyasa kowa yake jin shakkun zuwa ya fadi Abunda su bala suke aikatawa.Shi daman sule ba gari yake ba bare a gane halinsa.
An sha biki Amare sun tare lpia An fara zaman lpia daga farko kmr duka kenan,sule yanan shima bai koma wrn aiki ba domin kuwa a gdn iyayensa aka bashi sashe ya aje salma su kuwa sauran kowa mijinta ya kama mata gd Ana zaman lpia.
********************
Ko yaaa suka fara fuskantar matsalolinsu bayan auren 🤔🤔ko ya akai laifin iyayen ha shafi yaran sannan gashi dai Auran soyayya akai ta ina likon ya balle ?
Ku biyo yar mutan garin kt dan ji ya aka fara ❤️❤️❤️❤️
YOU ARE READING
ZAMAN YA'YA
Non-FictionLabari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari n...