AISHA
Walidation S Mapi
Page 25
Lateefa ce ta cire tsoro ta shige ofishin c.e.o Hamlam,tana shiga ta hango shi a zaune shi din ma ita yake kallo yadda take tafiya kamar bata son taka kasa sai dai shine asalin tafiyarta ba wai yanga ne ba,dan murmushi yayi ganin a tsorace take, tana zuwa ta zauna a inda tasan ake zama idan anje office din c.e.o, tana zaunawa ta gaida shi cikin harshen turanci tare da fadin "nima ina daga cikin masu neman aiki ne".
Hamma kuwa a karo daya yarinyar ta matukar shiga ranshi sai kuma ya tsinci kanshi da yi mata murmushin da bai san ya iyata ba, sannan yace "barkanki, nasan kinga wasunki sun fice a nan office din dayawa daga cikinsu ma kuka suke".
Lateefa tace "ehh ranka shi dade hakane,dalilin haka ne ma ya'r uwata tace mu tafi saboda tana da tabbacin baza mu samu ba don mu kadai muka rage ni kuma ce mata nayi tayi hakuri mu gwada sa'ar mu idan munada nasara ai zamu shiga".
Hamma ya dubeta cikin nutsuwa yace "ai kuwa da bata taimake ni ba, irin wannan kyau haka.ta rabani dashi, kinma saj dalilin da yasa na kora sauran ya'mmatan kuwa?".
Girgiza kai Lateefa tayi ba tare da tayi magana ba,kanta a sunne yake kamar tsohon mashayi.
"Saboda basu da tarbiya wasun su kuma sunyi kwalliya su a dole sai sun burge ni m, wasu daga ciki kuma basu da tsari, ke kuma gani nayi kinada dukkanin wadannan abubuwa da na lissafa wanda su ya'mmatan basu dashi, gashi kuma kinyi kwalliya sai dai ba don ni kikayi shi ba kuna sauke kai kasa" Hamma ne yake fa kwararo bayani ya kasa dauke idonshi a kan Lateefar ita kuwa kunya ce ta cikata.
Sai a lokacin ta budi baki tace "Yallabai kenan ai kwalliya ba don mutum nake yi ba kawai ina yin abu na ne don kaina".
murmushi Hamma yayi yace "dagaske?" A takaice.
Dago kanta tayi ta kalle shi sai a lokacin ya wayance ya dauke idon shi daga gareta ita kuma tace "dagaske mana yallabai".
"To kije kin samu aiki, kece p.a na".
Da wuri ta zaro ido ta dube shi tare da fadin "don Allah yallabai?".
"Mun taba haduwa dake ne bare nayi miki karya?".
Girgiza kai Lateefa tayi tace "aa nagode sosai da sosai, Allah ya kara daukaka ya baka mata ta gari" a zuciyarta kuwa cewa tayi "Allah yasa nice" tana fita ta cewa Aisha ta shiga ita ta samu.
Da tsoro da faduwar gaba Aisha ta shiga ofishin Hamma tana tunanin kada ya gane ta da hannh dayan dukda cewa fuskarta lullube yake da nikabi, tana shiga office din ta karasa kan kujera ta zauna saura kadan ta fadi a kasa saboda rikicewa tana zaunawa ta canza murya ta gaida shi.
Shiru taji yayi ta dago kai ta dube shi taga kamar yana nazarin wani abu ba tare da ya amsa gaisuwar ba yace "kije kema kin samu aiki, ke zaki rika kawo min coffee a duk lokacin da na bukata" yana gama fadin haka ya fice a office din cikin faduwar gabanda bai san menene silarta ba.
Yana fita Aisha ta diba dagudu tayi waje ta hango Lateefa a karkashin bishiyarda suka tsaya dazu tace "my baby girl na samu aiki, nice zan rika kawo mishi coffee a koda yaushe".
Kankame ta Lateefa tayi tare da fadin "mun godewa Allah daya bamu wannan damar Aisha, ni wallahi yau ina cikin farincikin da bai taba ziyarta ta ba, ji jake kamar na zuba ruwa a kasa nasha, kuma kinsan na dauka sai munzo da qualification dinmu kafin a bamu aiki ashe ba'a ma bukatar shi".
Aisha ma rungume ta tayi tace "wallahi nima haka Latee sai dai wani abu ne yake damuna wanda ba zan iya sanar dake ba sai dai na barwa zuciya".
Lateefa bata damu ta san ko menene ba taja hannunta suka tafi tana ta tunanin c.e.o Hamlam yadda yake gudanar da ayyukan shi kamar wani sarki, babu girman kai a ciki yana kula da jama'a yadda ya kamata.
YOU ARE READING
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.