AISHA
Walidation S Mapi
23
Dakyar Lateefa ta amshi kudin ta shiga gida da murmushi a fuskar tayi sallama ta shige daki cikin takun kasaita da isa da batsewa ita a dole tayi shigan matan minsters.
Dubanta Aisha tayi tana kokarin yin dariya ta make tace "First lady har an dawo?".
Lateefar ce ta karasa kan cinyar Aisha dake zaune ta kwanta tace "wallahi kuwa bakiga yadda na gaji ba sisina", "Ince Koda kafa kika dawo?"Aishar ta tambaya,
"A'a a motar Prince charming dina na dawo".
"don Allah karki fadamin".
"wallahi kuwa Humaira bakiga yadda yadda sake shiga raina ba yau kamar nayi hugging dinshi na maida shi ciki,wani fresh dashi".
"Allah kara dankon soyayya tawan" Aisha ta fada tareda Mika Mata hannu don su tafa.
Miko hannunta tayi suka tafan tace "ameen,kuma fa wai dazu yazo unguwar nan shima".
Ba tareda Aisha ta kawo komai a ranta ba tace "to kodai ya jiki shiru ne ya biyo ki?".
"A'a bana tunanin haka don jiya banyi mishi kwatancen gidanmu ba".
"kika san ko yana bibiyarki tun asali?".
"kuma hakane fa Humaira,abinka da soyayyar da Allah ya hadata daga sama".
"kai bakida dama Lateefa daga haduwa jiya yau har kin zille,to Allah ya barku tare in shidin Alkhairi ne a gareki,kinga kasuwa nake so ki kaini ba wai ki tsaya bani labarin Prince charming ba nagaji da labarin gayen nan yaseen".
"Haba ta wajena shine fa yanzu annurin zuciyata in ban baki labarinshi ba nawa kikeso na baki" ta fadi hakan tareda rufe fuskarta da tafin hannunta wai ita a dole kunya take.
"to shikenan na yadda ki rika bani labarinshi Amma muje ki rakani kasuwar tukunna".
"To jirani nayi sallah mu tafi dama a shirye nake,Amma fa dole ki sake gyaramin kwalliya ta saboda bazan biki kasuwa da fuska dabar-dabar ba,yadda nayi kyau dazu haka nakeson nayi yanzu.
"nidai kije ki dauro alwalar nan kiyi sallar na gaji da surutunki Lateefa".
"ai baki gaji dani ba sai randa na kasa bacci,don wallahi tashinki zanyi ki tayani hira,kuma kinsan me?".
"A'a saikin fada" Aisha ce tayi maganar tare da mika kunne don jin me Lateefar zata ce.
"wallahi Humaira bakiga yadda maza ke tururuwar karbar number ta ba yau,har fada wasu sukayi".
"don Allah?".
"Wallahi kuwa,niko idan na lura ka hadu sai in baka in baka hadu ba hanawa zanyi wallahi na Isa".
"good tashi kije lokacin sallah ya kusa fita" "to" Lateefa ta amsa dashi tareda fita daga dakin don yin alwala, tana kammalawa ta shigo daki ta gabatar da sallarta ta dauko kayan kwalliya Aisha ta gyara mata kwalliyarta suka shirya Aisha ta dauki kudinda Hamma ya aje mata suka tafi kasuwa suka kuma bar gidan a bude saboda Babu me shiga daki kawai suka rufe, Ammi kuwa taje unguwa tun safe shiyasa ma Lateefar bata tambaye ta ba.
Saida suka bar unguwar suka Isa bakin titi kafin suka samu abin hawa suka tafi kasuwar,ba wasu abubuwan kirki suka siya ba,manyan lantern ne guda biyu masu hasken gaske wanda ake cajinsu da rana kuma zaka iya sanya cajinka a jikinshi don dauke yake da igiyoyin caji me biyar, sai kuma kayan abinci masu dama da buhun shinkafa guda biyu,sai kayan miya da suka biya suka siya,Aisha ce ta bukaci Lateefa ta kaita shagon saida kaya, ba tareda tambayarta kome zata siya ba ta jata suka nufi want babban collections, shagon saida kayayyaki irinsu dogayen riguna da abaya da Kuma takalma da jakunkuna, suna shiga shagon Aisha ta hango wasu abaya kala biyu iri daya,saurin karasawa wajensu tayi ta dauko su gabadaya tazo wajen me shagon ta tambayi kudinsu idan zaiyi ta siya saita siya musu guda biyu itada Lateefa, dubu goma sha biyar-biyar ne Amma da yake me shagon tunda suka shigo ya kasa dauke idonshi a kan Lateefa yace musu dubu biyar-biyar ne,da sauri Aisha ta ciro kudin ta biya ba tareda ta tsaya neman ragi ba saboda tasan kudinsu yafi haka itama ta lura da yadda yake bin Lateefar da kallo, karban kayan yayi ya zaro daya daya cikin ledojin collection din ya sanya kayan a ciki ya fara kokarin mikawa Lateefa da ko kallonshi batayi ta zubawa collection din ido sai kalle-kalle take kamar wata ya'r kauye,ita batama san wainar da ake toyawa ba,Aisha kuwa murmushi tayi ta barshi saboda ta gane me yake nufi yasa bai bata kayan ba yake bawa Lateefa, ganin Lateefa bata kallonshi yasa yace "madam ga kayanku".
YOU ARE READING
AISHA
Historical Fictionlabarine a kan wata yarinya mara hannu daya wacce take kaunar dan uwanta Amma shi baya sonta ko kadan.