18

92 13 1
                                    

AISHA

Walidation S Mapi

18

Assalamu alaikum masoyana Kuma masoya wannan littafin nawa mesuna Aisha, ina mai baku hakurin jina da kukayi shiru kwana biyu hakan ya faru ne sanadiyyar sakaci na, ina nufin komai lafiya kawai typing dinne na gaji dashi ayi min uziri,Kuma insha Allah zanyi kokari naga na kammala rubuta wannan littafin nawa nagode sosai.

Tunkude ta yayi gefe guda yace "kina ganin nayi farincikin dawowar ki ne? Kinyi kuskure! Dalilin Farincikin da kika ga nayi shine kin tsamo ni daga ruwan dana fada ne banza jahila" ya zare belt dinsa ya fara jibgarta dashi.

"Don Allah kayi hakuri ka saurare ni Yaya Hamma" shine kawai Abinda Aisha take iya furtawa.

"Anki a saurare ki din jahila wacce batasan darajar Aure ba".

"Kai din kasan darajarta ne? mugu kawai azzalumi, Allah bazai taba kyale ka ba sai ya bimin hakkina" Aisha ta mayar.

"Har kina da bakin magana?wallahi Aisha zan kashe ki".

"Daka kasheni dana huta wallahi Yaya Hamma ai da wannan Abinda kakemin gwara mutuwar" "to barin kashekin inga yadda zakiyi" ya daina dukarta da belt ya shiga dukanta da hannu saida ya tabbatar da cewa ta daina numfashi ya karasa wajen gate din ya rufe gidan ya shiga ciki ya kwanta abinsa.

★★★
Anty Amarya ce zaune a daki ta zabga tagumi tana ta tunanin halinda Aisha take ciki ga rashin masoyi ga rashin iyaye a kusa da ita,daga ita sai wanda yafi tsanarta a duniya,sallamar Maleeka ne ya dawo mata da hankalinta,samun waje Maleeka tayi a gefen anty Amarya ta zauna tace "Anty anji labarin Aishar ne?" Anty Amarya ce ta dago kai ta dubi Maleeka "A'a Maleeka ba labari,tunda Hamma yayi mana karya bai sake daga wayarmu ba,wallahi ina cikin matsananciyar damuwa ji nake kamar ma Aishar bata tare dashi" Maleeka ce tayi saurin rike mata baki "Haba Anty na bai kamata kina furta irin wadannan kalaman ba,rashin Aisha bazai zautar dake ba,don Allah ki cire wannan zargin da kikeyi ko zuciyarki zata samu sadida" "shikenan Maleeka zanyi kokarin hakan ya Haidar da Khadeeja kinsan kwana biyu ban leka ku ba" tabe baki Maleeka tayi tace "Haidar na lafiya sai dai bansan wancan ya'r lukutar ba" "kina nufin baku hada kanku keda ya'r uwarki ba?haba Maleeka kufa ya'n uwa ne ba bare ba ku shiga hankalinku" "Anty wallahi duk yadda nayi wajen mu saba da Khadeeja taki, sai nunamin takeyi ita ya'r gata ce bayan a gida daya muka fito shiyasa kikaga sam kanmu ba'a hade ba".

Numfasawa Anty Amarya tayi tace "ku dai yi kokari ku hade kanku saboda mu ya'n uwane gabadaya,kuma idan bakwa yiwa Haidar Abinda yake so to wallahi gab yake daya kare Aure kuma kunsan ya halarta a familynmu idan kayi Auren farko a cikinmu kayi na biyu a waje,shawarata Kenan".

Maleeka tace"Thank you Anty na shiyasa nake Kara sonki a koda yaushe kina bawa mutum shawara mai matukar amfani,wanda idan yayi Amfani dashi zata taimaka mishi a Koda yaushe".

"Ai haka akeso mutum ya kasance a Koda yaushe kada ya bawa mutum gurbatacciyar shawara domin takan iya lalata dukannin rayuwa ita Kuma" Anty Amarya ta mayar.

"Kinga Anty ni zan koma sashenmu yaya Haidar bai fita aiki ba yau".

"Ok to aje Asha faman kula da miji shine Abu mai kyau domin da kinyi sake ya'r lukuta zata kwace shi rasss".

AISHAWhere stories live. Discover now